Breaking News

Gidan Aunty book 1 page 13-14

 



💖💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖💖


PAID BO


OK

 

Dedicated this page to masoyiya and the talent troupe writers, masoyiya I heart ❤️ you Lodi Lodi.


Book 1 💖


Free page 13🦋

 

Sosai ta rintse idanuwanta , tsawan yan sakanni jin bata fadi kasa ba kamar yadda tayi tunani, hakan ya bata damar  fara bude idanuwanta a hankali cikin fargaba, akan fuskarsa dake hade sosai idanuwanta suka sauka , ta manta a yadda take sabida shagala da tayi da kallan kyawun fuskarsa, tsawar daya daka mata  a lokaci daya da sakin gefen rigarta ne ya firgitata,  ga kafarta dake mata zugi kadan kadan adalilin sakin ta da yayi ta fadi, a hankali ta saki wata yar karamar kara tana rike kafartata “are you mad” taji kausashshiyar muryarsa cikin dodan kunnanta, girgiza masa kai tashiga yi , sosai ta tsorata da yanayinsa ko kallansa ta kasa,ba karamin baci ransa yayi ba ganin yadda ta basa amsa “are you mute” takarajin saukar muryarsa, nan ma kai tashiga kokarin girgiza masa,wata gigitacciyar tsawar data sata mikewa ya daka mata , bata san lokacin da ta fara “kayi hakuri dan Allah “, ta karasa a hankali tana sun kuyar da kanta kasa , dan siririn tsakin da ko ita bata jisa ba yasaki tare da komawa inda ya tashi ,”clean this mess, and bring my coffee”, ya fada a takaice har ynxu fuskarsa ba a kanta yake ba, da sauri ta jinjina masa kai sai kuma tayi saurin bude baki “toh” tana gama fada ta koma kitchen, cikin kankanin lokaci ta gama hada coffee din da sai faman kamshi yake , cikin wani dan cup me shegen kyau , a hankali tayi sallama cikin rawar murya, kamar ba zai amsa ba kuma sai ya bude bakinsa a hankali”Wa’alaykumussalm “, ko ita da ke shigowa falan bana tunanin taji , cikin rawar hannu ta karasa inda yake , duk kamshin turaran sa ya cika mata kunne , so take kawai taga ta kebance, kusan mintuna daya bece komai va kuma be amsa coffee dinva, saida ta gaji dan kanta kafun tace “gashi”kamar me kokarin sakin kuka , nan din ba bai amsa ba saida ya mula dan kansa sannan ya saka fararan hannunsa ya dauka a hankali, wani sanyayyar ajiyar zuciya tahee ta sauke ganin ya karba , sai ta koma kitchen ta dakko abunda zata gyara inda ta bata , a hankali take yin komai duk da yadda zuciya da jikinta ke rawa,cikin kankanin lokaci ta gama gyara  komai ta mayar kitchen . Tana shiga bata tarar da asabe ba aciki, tunani ta fara ta tafi daki ko tajira ya tafi, dan harga Allah shakkar fita take, ta dau kusan mintuna ashirin a kitchen ganin lokaci yaja atunaninta ya tafi zuwa yanxu, Daidai ta kai tsakiya falon sabida yadda tasawa ranta ya tafi sai jin muryarsa kawai tayi a fiske “coffee” daga nan be kara cewa komai ba.”Innalillahi “ shine abunda tahee ta fada cikin zuciyarta kafun a hankali ta nufi kitchen kamar wata muna fuka , wani coffee din Ta hado masa, yanxu cikin rawar murya ta bashi, kamar dazu sai da ya gaji dan kansa sannan ya karba, ta juya da niyar komawa ta kara jin saukar muryarsa “wait”,ji tai kamar ta fasa ihu a wajan, gashi tana tsoran ta tsugunna kartaje tai wani laifin , tsawan mintuna goma tana tsaye bece da ita komai ba ,cikin dan guntun tunanin da ta fada ta kara jin saukar muryarsa “coffee”, kukane kawai tahee bata saka ba a haka ta koma ta kara hada wani coffee din ta na kawo masa bata jira cewarsa ba ta arta a guje sai cikin dakinta. A hankali ya dago da kyawawan idanuwansa “ is she mad “ ya tanbayi kansa sai kuma ya tabe baki tare da jan siririn tsaki a haka yaci gaba da sipping coffee dinshi a hankali,kusan 11 na dare yana falon kafun ya nufi nashi part din.


A Daidai gaban dressing mirror din dakin ta tsaya sai faman haki take, ita kadai ta san karfin halin da tayi kafun ta rugo a guje , sosai zuciyarta take harbawa ga wani irin kasala da take ji, “amma kyakkyawa ne”ta fada a ranta sai kuma ta ja dan tsaki, tare da hade rai “coffee”,”coffee”,coffee”,ko wanne shi oho, bata gama tunaninta ba fuskarta ta hango mata yadda fuskarsa yake a hade, yawun bakinta ta hadiye”nide nashiga uku” sai kuma ta tsaya kamar me tunani “wata kila bakone shima , naga bayajin Hausa gashi dan balarabe dashi”da wannan tunanin ta kwantar da hankalinta, watsa ruwa tayi tare da kwantawa, lokaci zuwa lokaci tunanin mutumin na fado mata a rai musamman yadda dan karamin bakinsa ke cewa “coffee”.


*******

WASHE GARI

 Tahee na zaune kan lallausan medium carfet din dakin tana karanta azkar din ta aka kwankwasa kofa , bada izinin shiga tayi, a hankali asabe ta turo kofar bakinta Dauke da sallama sai faman kawar da Kai take gefe , TAHEE na kula da yanayin ta amma batace mata komai tunda itama Allah ya tseratar da ita .gaishe da asabe tayi, duk sai asabe ta tsargu ta kasa cewa komai har tazo fita sai ta Waiwayo kanta a kasa,”uhm dama hajiya ce tace idan kin kammala cin abincin ki same ta a falo”, toh kawai tahee tace mata kafun asabe ta bar dakin. Tana kammala cin abincin da aka kawo mata kamar yadda ammi ta umarcetan falo ta nufa, anan ta tarar da ammi na kallo a tv, ammi na ganin ta tamike “Yawwa daman ke nake jira , nasan kowa yana falan dada”, da karfi zuciyar tahee ta buga ,  tuno fuskarsa da tayi “nashiga uku , yanxu ya zanyi idan naganshi acan”, ammi ce ta katse Mata tunanin da ta fara ,”muje ko”murmushin yake tahee ta saki har ynxu zuciyarta bata dena bugawa ba ,a haka suka nufi part din dada kasancewar hijabi ne a jikinta. 


Zazzaune suke a falon dada , sai faman hiransu suke gwanin burgewa , shigowar su ammi ne yasa ko wannansu maida hankali kan har yar shigowa, amrah na ganin tahee take a wajan wani tsanarta ya darsu a ranta, ji take da za ta kashe mutum babu wannan da zata kashe face wannan maiyar. Cikin sanyin jiki ta gaishe da kowa na falon , ganin irin kallan da kowannansu ke binta dashi, sabanin ummey da abeey da fuskarsu ne dauke da murmushi, sai kuma dada dake faman washe hakwaranta. “Zonan kizauna kusa dani”cewar dada , a hankali tahee ta koma kusa da ita , nuna abeey dada tayi “kinga wannan , toh shine babban dana , kuma shine baban yaran gidan, daga yanxu Kema zaki dinga kiransa da abeey kamar sauran”, sai musaddiq da uncle Saleem da ta nuna, “ wannan kuma Itace babbar maman ku, ana kiranta da ummey, ga kuma matan kawunki musaddiq , ana kiran wannan ta farko mamy sai kuma momy gatanan, sai kuma ta karshen su da ake kira da aunty , ita matar kawunci salim ce, ga yan matan gidan kuma ,duk da nasan zuwanki zaki iya saninsu tunda kullum suna wajan maman yara, bayansu akwai babbar yayarsu dake aure a saudiya sunanta samareena (samreen😂) ana ce mata ukuti( ukhti)zaki ganta wataran,akwai maza guda biyu suna karatu a turai, sai sadauki” tana ambatar kalmar sadauki gaban tahee ya fadi , jitai dada na cewa “ zaki ganshi shima wata ran amma kiyi taka tsantsan , ah too in fada miki gaskiya, ga autar gidan kuma can” ta nuna zoya dake kwance kan cinyar ammi tana bacci,kadan tahee ta dago ta kalleta “amma kyakkyawace sosai “ ta fada a zuciyarta”Nima akwai yar autata da ban fada miki ba sunanta “zarmeen sai danta kwallin kwal wato mijina sha’aban “.kallan abeey da ummeey tayi “nasan ku ai duk kunsan da zuwan ta ko” eh dada duk suka bata amsa , har yanxu da Sauran guntun murmushi akan kumatun ummey,” toh sunan ta tahura” yalwataccen murmushi abeey ya saki “taheera dai ko dada”, gyada masa kai dada tayi “ au kai da kasan da sunan ma amma sai ka wahalar dani”, wani murmushi abeey ya kara saki batare da ya ce komai ba , kallan ta hajiya ameena tayi cikin sakin fuska” gata kuwa kyakkyawa da ita kamar ka sace”, sosai ran amrah ya baci da Jin kalaman auntyn tata, ranta ya baci sosai da irin yadda kowa ke karbarta, “Shegiya in ma asiri kikai musu nice zan karyashi “ ta karasa tare da binta da kallan tsana bata re da kowa ya lura da ita ba . 


*********

**************

Zaune take kan daya daga cikin daddiyar kujerar falon mahaifiyarta, tunda suka dawo daga falon dada take zaune a wajan hannun ta dauke da juice yayin da Dayan hannun nata ke dauke da wayarta sai faman latsawa take , sam hankalinta na kan abunda take a wayarta, jin taku a falon yasa ta saurin fita daga abunda take tare da sassaita nutsuwarta, hajiya hauwace ta shigo falan, tun zuwansu falon dada sai yanxu ne take dawo wa , cikin izza take taku har ta karaso kan daya daga cikin kujerun dake fuskanta sumayya. Murmushi sumayya ta saki, mamy daman ke ce , “nice mana akwai Wanda kike jiran zuwan sane “, tabe baki sumayya tayi ,”toh mamy daga tanbaya, tun dazu nake jiranki fa , amma daga zuwanki kina so ki bata mun fai “, washe baki hajiya hauwa tayi “Haba summy ta ne yayi zafi kinsa Nima wasa nake miki”, jinjina kai sumayya tayi” mamy baki kula da yar iskar yarinyar da aka kawo gidan nan ba , ki duba ki gani fa yanda kowa ke kaffa kaffa da ita ko mu da muke jininsu ba ai mana wannan abun ma , musamman dada  da ke faman nanike mata, wallahi in bamuyi wasa ba sai dai mu zama yan kallo a gidan nan , se abunda yar iskar yarinyarcan ta fada sannan za’ai , kina kallanta kinsan ba haka taxo ba , akwia wata kullalliya a kasa , ni tsorona kartaje ta asircemun king, sabida kinga yawanci king acan yake wuni kuma mu ba mu isa shigaba in yana nan, gaskiya mamy ya kamata ki dauki matakin gaggawa, bazan taba bari cikar burina ya tafi a banza ba , inaso nayi suna, inasan duniya ta san da za mana , inasan mallakar king ko ta halin yayane mamy”kin Hana na nuna alamun ina san sa a fili har waccan banzar take tunanin auransa, dole mamy na mallakesa sannan dukiyar gidan nan mu ya kamata muji dadin ta ba wasu ba”, ta karashe maganar tare da kurawa mahaifiyar tata idanu, sauke nunfashi hajiya hauwau tayi kafun ta soma magana “tabbas Kinyi gaskiya Nima na dade ina halkanta da hakan , a sannu zanyi maganin kowa dan bazan taba bari dukiyar da na kwallafawa Raina zubucewa ba , aure kuwa kamar anyi shine “. Sallamar ihsan ce ta katse musu zancensu , bin ko wannensu tayi da kallo tare da girgiza kai, tasan halinsu Sarai , fatan ta Allah ya shirya mata su, ganin yadda take bunsu da kallo ne yasa mamy mikewa tare da hararar ta sama sama ,bata jira cewar ihsan din ba tai wuce warts daki, itama sumayyan tashi tayi tare da nufar nata dakin,ganin duk sun watse ne yasata kiran number wayar da tayi saving da my yaya, bugu biyu ya dauka..


🫧🫧🫧🫧🫧🫧

Tunda ta dawo daga part din dada take safa da marwa , ita kadai tasan radadin bakin cikin da takeji, ta tsani yarinyar tsana mafi muni, ko ita lokacin da tazo ba a nuna mata kauna haka ba kamar yadda aka nuna wa waccan , “tabbas sai na lahantaki, lahanin da ko kyawun da akace kina dashi ze gushe, da kanki zaki bar gidan nan”, duk wannan zan tuttukan ita kadai amrah take yinxu kamar wata zautacciya, tunani ta fara me zatayi mata da zai kunsasa mata , ta dade tana tsaye a falon kafun ta saki wani shu’umin murmushi, kitchen Dinsu ta nufa, ba a dau dogon lokaci ba ta fito sai faman sakin murmushi take , direct part din ammi ta nufa dan tasan har yanxu su ammi Suna part din dada, ilaikuwa tana shiga bata tarar da kowa ba sai kamshin turare da sanyin  Ac dake tashi, jin motsi a kitchen yasa ta kara sakin wani shi’umin murmushin, ta dau kusan mintuna biyu tsaye a wajan, jin alamun taku kamar za a fito daga kitchen din yasata zuba mangyadan da debo a kan  hanyar da ta san dole koma wanene ta nan zai wuce . Taheee ce ta fito daga kitchen din hannunta dauke da bottle water tana sha dan ishirwane ya kaita kitchen din, bata san da mutum a falon ba , sai ji tayi an tura ta da karfin gaske, kafarta ta sulleba a cikin man da amrah ta zube, sosai ta saki gigitacciyar kara tare da tafiya Gadan gadan zata fada , ta rotan da taji anyi , a lokaci daya da gigitacciyar marukan da aka suke akan fuskar wanda bata sani ba ya kara girgitata, lokaci d’aya nunfashin ta ya dauke alamun ta suma .



Share ✍️


Littafin gidan aunty na kudine , akan 300 kacal , da zaran na gama free pages dina Wanda suka biya ne kawai zasu dinga samun update , mai don gidan aunty zai iya biyan kudin ta wannan account din 7041879581 opay, Ayshatou galadima sai a turo sheda ta wannan number 07041879581.


💖💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖💖

‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA


💖💖GIDAN AUNTY💖💖

           (a heart touching love story)


Story &written 

        By 

Mss Lee💖


💖💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖💖


PAID BOOK


Nakusa kammala free pages dina,littafina na kudine akan 300 kacal, 

VIP 500, 

special 1000 

mai bukatar cigaba da karantawa zai biya 300 ta wannan account din 7041879581 OPAY, AYSHATOU GALADIMA, sai a turo shaidar biya ta wnn number 07041879581.


Wanda suke da bukatar a tallata musu kasuwancin su kuma zasu iya yimun magana ta wannan number 07041879581. 


BOOK 1 📕


بسم الله الرحمن الرحيم 💖💖……


Free page 14 🦋



Wani gigitaccen  marin ya kuma saukewa akan amrah da tayi mutuwar tsaye , sosai marin ya shigeta nan take ta fashe da kuka,a matukar firgice ta daga idanuwanta, Wanda taganine yasa zuciyarta bugawa da zauri , fitsarine ke kokarin kwace mata da bata shiryaba, batai tunanin samun sa anan ba ko waninsa , kallan dake firgita Mara gaskiya ya bita dashi kafun ya mayar da idanuwansa kan tahee da kallo daya yayi mata ya dauke kansa da jan tsaki , kan daya daga cikin 3sitter din kujerun falon ya kwantar da ita, wani siririn tsakin ya kuma saki ganin dan karamin abinnan ya sumarda ita, da baya wajan kenan mutuwa zatai, ya kara Jan wani Siririn tsaki “spoiled rat” ya fada a kasan zuciyarsa. “Water “ ya fada cikin da kakkiyar muryarsa, cikin zabura amrah da jikinta ke faman rawa ta nufi kitchen da sauri ta dakko, zuciyarta sai faman tsinewa tahee yake ”nashiga ukuna Shegiya yar yarinya daga zuwan ta tasa ya mareni, nashiga ukuna, Allah yasa bega man da na zuba ba”, sai kuma ta zabura cikin sauri ta fito daga kitchen tare da kai masa ruwan sai faman sauke kai take zuciyarta na tsananta bugu, bai kalletaba sai ruwan da ya bude ya yattafawa tahee, a firgice ta tashi zata kara sakin wani karan,” if you dare”taji saukar  muryarsa , kara rintse idanuwanta tayi zuciyar ta na tsananta gudu, siririn tsaki ya saki tare da matsawa can gefe,amrah na tsaye sai faman gumi take hadawa, cikin kausasshiyar muryarsa yace “apologize “daga nan be kara cewa komai ba kamar bashine yayi maganar va, wani irin kuka ne yazo wa amrah amma ta rikeshi, sosai zuciyarta ta kara tsanar tahee,”are you mad” bata bari ya karasa ba ta ce “kiyi hakuri” ta karasa cikin rawar murya sosai takejin ba’kin ciki a cikin zuciyarta ,”kneel and apologize with sympathy “ba yanda ta iya haka ta tsugunna ta  shiga bawa tahee hakuri , sai lokacin tahee ta bude idanuwanta, sosai kwayar idanuwanta suka canza kala musamman bakin idan nata da ya fara dan washe wa kadan, gaban amrah ne ya fadi da Sauri ta sun kuyar da kan ta, “bakomai ya wuce “ tahee ta fada, ganin king na falon tace “nagode “ duk da kwata kwata basu yake kalla ba. Sallamar ammi ce ta katse tunanin amrah , ganin ammin yasata mikewa , Binsu da kallo ammi tayi tare da nufar tahee “lapiyan ki kuwa” sai kuma ta maida kallanta kan amrah”amrah “ ta kira sunan ta , in ina amrah ta soma , ammi bata kulata ba ta kara maida kallanta kan king” son”, lumshe mata idanuwansa yayi tare da bude wa akanta ba yabo ba fallasa, “me yafaru “ ta kara tanbayarsu, dan tabile bakinsa yayi kamar bazai ce komai sai kuma yayi magana a fisge “ I just come in, but I will come back later “yana gama fadar hakan bai jira cewarta ba ya juya , duk da kallo suka bi bayansa “ ko shine babban yayan su “zuciyar tahee tabuga sosai , musamman da taji ammi na kiransa da “son”,  katse mata tunani ammi tayi “ba magana nake muku ba” amrah ce tayi saurin bude baki”daman ammi santsine ya kwasheta, sai yaya king ya temaka mata” ta karasa maganar cikin Dacin rai.kallanta ammi tayi cikin damuwa”hope bakiji ciwo ba “ gyada mata kai tahee tayi, sai a sannan amrah tayi wa ammi sallama ta bar part din, tagefan ido tahee ta bita da kallo tana cije baki, sannu ammi tayi mata kafun ta nufi dakin ta, itama tahee mikewa tayi tare da nufar dakinta.


➰➰➰➰➰➰➰➰➰

🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧


BUNKURE 


Dije ce zaunce cikin wata bukka dake dauke da wasu irin tarkace , gefenta kuma bintalo ce sai faman bin wajan take da kallo duk da ba yau suka fara zuwa wajen ba, wani irin dariya aka brake dashi kafun wani hayaki ya cika wajan , kafun wani bakin mummunan mutumi ya bayyana a wajan, duk jikinsa tabo ne a jiki, ga wani irin wari dake tashi a jikinsa, kara bude bakinsa dake faman wari yayi yana faman sakin dariya , ko wannansu kasa sukai da Kai , duk da warin da yake , “Allah ya kara…. “ wata gigitacciyar tsawa ya daka mata, cikin wata murya Mara dadin sauraro ya soma magana “ hatta dai , kull din ki kisan yadda zaki dunga magana agaban shugaban ku “,sun kuyar da Kai Dije tayi” tuba muke boka , me biyawa kowa bukatunsa “, wata irin dariya ya barke da ita , kafun ya hade rai “ meke tafe da ku, ko da yake Munson me ke tafe daku, me kuke so ayi musu”, cikin jin dadi Dije tace so nake a batar dasu , itama wacca aka tafi da ita gidan daula a batar da ita ko a haukatata, sai yata bintalo takoma can da zama “, wata dariyar ya kuma yi kafun ya soma magana “bagamar a haukatar da yarinyarcan ba zaiyuba sai in har tana kusa daku, uwarta da dan uwanta kuma zaki iya kawar dasu cikin sauki idan kin bi sharadaina, a sannan ne kuma za a tura yar taki inda kikeso harta daukaka”, washe baki Dije da bintalo sukayi”Godiya muke boka” katseta yayi yana babbaka wannan mummunar dariyar tasa kafun wani dan karamun kulli ya fado a gabansu,” wannan zaki barbada musu a kofar dakinsu, da sun taka shikenan, amma kada ki kuskura wani ya taka basu ba , inba haka ba aikin ze ruguje, sharadi na biyu kuma dole ki bani yar taki na sadu da ita ,dan maniyinta kadai da aljani zai tabane zai zama cikar aikinkubayan hakan ba iya can din va, hatta maganarta sai andungaji akasin hakan kuwa rayuwarkuce zata kaskanta“, yana kammala maganar tasa ya babbake da dariya , tsuru Dije tayi tare da kallan bintalo dake faman zare ido”batare da wani dogon tunani va Dije tace “na amince”kara babbakewa yayi da dariya,cikin muryarshi da bashi da dadin sauraro yace” zaki iya tafiya, inna gama aikina sai ku tafi”, kallan Dije buntalo tayi kafun ta dauki maganin ya fita waje, yai saura daga bintalo sai wanan bokan da babu komai a jikinsa sai dan ganyen da ya rufe masa al’aurarsa. Cikin tsawa yace “mike” da sauri kuwa buntalo ta mike tana zare ido,”tube kayan ki , kizomun da baya da baya”, cikin sauri tsananin yadda ta tsorata da sauri ta cire kayanta , haihuwar uwarta, ta soma tahowa da baya da baya jikinta sai faman karkawa yake. Duwawunta ya zuba wa idanu sai faman hadiyar yawu yake yana sidar baki, cikin azama ya janyo hannunta ta fado kansa, wata kakkarfar ajiyar zuciya yasaki tare da sakin gurnani yana kara matseta a cikinsa, duk da warin da yake, ko motsi buntalo ta kasa sabida tsoran da taji, cikin azama ya juyar da ita ya Dane kanta, ba tare da wani abuba ya dage dan karamin ganyen jikinsa, take a Wajan bakakirin alaurarsa ta fito sai yawo take, bintalo kuwa harta fara hawaye, be tsaya wata jinkiriba ya shigeta da karfin gaske , tare da matseta a jikinsa yana sakin gurnani kamar wani mayun Wacin zaki…….


➰➰➰➰➰➰➰➰➰

🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧 

Yana barin part din ammin nasa hadadden gym dinsa ya nufa cikin kayan motsa jiki, sosai ya motsa jikinsa, ya dau dogon lokaci yana motsa jiki da abubuwa mabanbanta , kafun ya koma dakin sa ya watsa ruwa cikin shigarsa da tayi matukar yi masa kyau ya fito , sanye da blue din t_shirt da white jeans , sosai kakkarfar damshen hannunsa ya fito, kayan ba karamin yi masa kyau yayi ma , gashinn kansa sai faman kyalli yake, duk inda ya wuce sai kamshin imperial ya cika wajan, bai dau dogon lokaci ba yashiga cikin farar Lamborghini din da sai faman kyalli take da dauka ido take, cikin lokaci kankani, jerin motocin nan suka fita daga cikin gidan, sojojin wajan sai faman sawara motocin suke.



Karfe 8:30 na dare amrah ce sanye da dan karamin towel da ko kwiwa be kara sa mata va, sai uban gashin attachment din dake yawo a bayanta. Waka ta saka tana tikar rawar ta , saida ta gaji dan kanta sannan ta kashe tana sauke ajiyar zuciya. Toilet ta nufa da nufin watsa ruwa ko dan kwali babu ajikinta, ta karasa kenan zata kunna fanfo, abinda ta gani ne ya firgitata tare da sakin gigitacciyr kara…..


Comment and share ✍️


💖💖💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖💖💖

Mss Lee 💖


Masu comment da masu yimun magana akan gidan aunty , ina matukar Godiya da jin dadi ✍️…

‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA

💖💖GIDAN AUNTY💖💖

   ( a heart touching love story)

 

Story &written

       By 

   Mss Lee 💖


💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖


No comments