Furar Danko 88
88
.........Aunty Khadijah bata ma san sanda ta afko bayin ba. Da ƙyar suka iya riƙe Lulu su biyun, alamar ya fita aunty Khadijah tai masa, badan yaso ba ya fitan ita kuma ta shiga cikin ruwan ta riƙe Lulun da jikinta ke karkarwa sosai. Ta gama fahimtar minene matsalar Lulun, ko muryar Smart ɗin bata son ji sam dan firgitata take sake yi, dan haka ta fara mata magana cikin lallashi da kulawa, sannu a hanakali yanayin nata ya shiga canjawa, ta koma laƙwas sai kuma ta saki kuka da riƙe aunty Khadijah. Cigaba da lallashinta Aunty Khadijah tai da canja mata ruwa har sai da ta tabbatar ruwan zafin yay mata ratsawar da zai iya bata nutsuwar da take buƙata sannan ta fito ta ɗaukar mata kaya. Smart na zaune ya dafe kansa bayan ya gama ƙarfin halin yaye bedsheet ɗin saman gadon ya canja da wani. Shiya ɗakko kayan ya bama aunty Khadijah ta koma bayin, babu jimawa sosai sai gata ta fito riƙe da Lulu da ke takawa da ƙyar tana hawaye. Ya nufosu da niyyar taimaka musu aunty Khadijah ta girgiza masa kai, dole yaja ya tsaya badan yaso hakan ba. Sai matsanancin tausayinta da ke ratsa shi ganin yanda take tafiyar a wahalce duk da dama rabin jikinta a jikin aunty Khadijah yake. Saman gadon ta kwantar da ita sannan ta ɗaura mata ruwan data riga ta haɗama alluran barci a ciki masu ƙarfi. Cikin sa'a ruwan baifi mintuna bakwai da fara shiga jikinta ba barci mai nauyi ya ɗauke ta, ajiyar zuciyar da take saukewa a jajjare kawai kake iya ji.
Aunty Khadijah ta sauke numfashi da ajiyar zuciya tana kallonsa, yanda ta kafesa da idanun ya sashi kasa jurewa yay ƙasa da nasa. Zama tai a bakin gadon da masa nunin ya zauna shima. Zaman yay kamar yanda ta buƙata.
“Aliyu ka kwantar da hankalinka abinda ya faru bashi bane dalilin shigarta a wannan halin.”
Da sauri ya É—ago ya kalleta, cikin nuna mamaki ya ce, “Amma aunty kafin yau ban taÉ“a ganinta a irin wannan yanayin ba”.
“Bazaka gantaba dama, saboda ba'ai mata abinda zai kaita ga shiga irin yanayin bane. Dan akwai É“oyayyen al'amari a rayuwarta. Yanayin da ta tsinta kanta a ciki yayi kama da na mutanen da aka taÉ“a ma fyaÉ—e....”
“FyaÉ—e!..”
Ya maimaita kalmar da wani irin yanayi mai kama da almara. Ko ruÉ—ani.
“Tabbas fyaÉ—e Aliyu, shiyyasa a wannan gaÉ“ar abinda ya faru a baya ya shiga tariyo mata kansa, dalilin da yasa ta firgita kenan har tana neman rasa tunaninta”.
Kai ya shiga girgizawa da sauri. Duk da yau ne karansa na farko da fara mu'amulantar mace bazai yarda da hakan ba. Shi mai ilimi ne, sannan mai zurfafa bincike akan abubuwan da yake buÆ™atar sani tun bai kai haka ba. Ya nema sani matuÆ™a akan mace da suffofinta. Taya ma zai yarda waninsa ya aikata abinda shi shaida ne akan zama na farko a yau É—in nan bayan wasu awanni kaÉ—an. Sake girgiza kan nasa yay da janye idanunsa da ya zuba akan Mawaddat ya maida su ga Aunty Khadijah. “Aunty mudai yi wani tunanin ba wannan ba, Mawaddat she is virgin hundred percent”.
Cikin mamaki ta ce, “Aliyu kasan mi kake faÉ—a kuwa?”.
“Tabbas wannan shine gaskiya. Na baki kowace irin dama kuma ta tabbatarwa ta hanyar aikin ki”.
Sosai hakan ya nema saka Aunty Khadijah a ruÉ—ani, amma kuma tabbas ta san Aliyu akan gaskiya da furtata, sannan ita kanta a yanayin data ga Mawaddat ya tabbatar mata yau ta fara sanin É—a namiji a rayuwarta, dama tana son sake tabbatarwa ne. MiÆ™ewa tai tsaye ta fara kaikawo kusan na minti guda, sannan ta juyo tana kallon Smart da ya sake zubama Mawaddat dake barci da sauke ajiyar zuciya har yanzu idanu. “Aliyu indai hakane kuwa akwai É“oyayyen al'amari Æ™unshe da rayuwar Mawaddat. Tunda har ka tabbatar min na yarda da kai, amma tabbas an taÉ“a harar rayuwarta da wannan siffar kuma lamarin bai kasance Æ™arami a gareta ba, dan ta ajiyesa a zuciyarta da har takai yake iya firgitata irin haka. Ba kowa ne ake kai masa harin fyaÉ—e ya ke tsintar kansa a irin matsanancin firgicin nan ba har sai ya tabbata an aikata masan. Shiyyasa kaji nace maka an aikata matan da farko”.
Kansa yake jinjinawa cike da nazarin kalamanta. Tare da haÉ—asu waje guda da wasu É—abi'un Lulu da mabanbanta kalamanta a wasu lokuta. Idan ya É—auki kalamanta na safiyar yau da ta tabbatar masa zata iya halakashi kamar yanda ta kashe wancan, hakan na nufin abinda Aunty Khadijah ta faÉ—a tabbas dole ne ya zama gaskiya, sai dai ba'a cimmata ba. Idan aka É—auki yanda take kallon maza, da yanda ta tsani duk wani da ya aikata fyaÉ—e da tsaiwar da take akan case irin hakan cikin zafi da zafafawa. WaÉ—an nan duk hujjojine abin kallo da dubawa. Maganar Ammah a randa ya kaita gidansu da take ce masa ya kusanta kansa da ita ya fahimci damuwarta, dan akwai É“oyayyen al'amarin data fahimta game da ita a cikin hirarsu. Anya kuwa ma shaye-shayen yarinyar nan baida alaÆ™a da wannan al'amarin? “Oh my God!” ya faÉ—a a zahiri yana furzar da iska mai zafi.
Aunty Khadijah ta ce, “Ka kwantar da hankalinka Aliyu. Wannan damar gareka take na bincika ainahin gaskiya a yamzu. Dan inhar ta iya faÉ—ar duk abinda ke a ranta tamkar mun yaÆ™i kaso sittin ne cikin É—ari na halin da take a ciki, in ba hakaba zakuyita fuskantar matsala ne kai da ita matsayin ma'aurata dan kaima zata dinga kallonka ne da wannan siffar a duk sanda ka raÉ“eta. Dan al'amarin ya matuÆ™ar taÉ“a brain É—inta da rayuwarta.”
“Insha ALLAH Aunty zanyi iya bakin Æ™oÆ™arina akan hakan. Sannan ni kaina ina son sanin kowanne tsinanne ne wannan domin É—anÉ—ana masa fiye da azabar daya dasama ruhinta na tsawon lokaci. Sai dai ina roÆ™on alfarmar kar wanda yasan wannan zancen dan ALLAH”.
“Karka damu Aliyu aikina ne hakan. Akwai amana tsakanin likita da majiyaci, balle ma abinda ya shafeka muma ya shafemu. Kallon É—aya daga cikin ahalinmu nake maka tamkar Ahmad. Haka itama Mawaddat tana da alaÆ™a damu mai Æ™arfi. Dan haka in sha ALLAH a duk sanda kake buÆ™atar wani taimako ka nemeni”.
“Insha ALLAH aunty Nagode sosai, ALLAH ya saka da alkairi”.
“Amin. Sai kuma kayi haÆ™uri dan yanzu koda ta farka gaskiya akwai daru, dole sai ka kauda kai dan itama ba daga gareta bane tun farko an dasa mata tsoron hakanne a zuciya. Dan ma kayi matuÆ™ar yin farar dabarar kiran Ahmad É—in kuje asibiti, da ace kace sai har zuwa safiya brain É—inta zai iya birkita fiye da hakan. ALLAH dai ya rufa mana asiri yay mana maganin azzaluman mutane”.
Ya amsa mata da amin zuciyarsa na masa Æ™una. Da ga haka ta ajiye masa magunguna suka fito falon inda Ahmad ke zaune cikin damuwar daÉ—ewar tasu. Dan a Æ™alla sun samu cikakkiyar awa guda a ciki. Suna fitowa ya miÆ™e zumbur idanunsa akan Smart. Aunty Khadijah batace masa komai ba ta nufi hanyar fita tana kallon agogon dake É—aure a tsintsiyar hanunta. Smart zaiyi magana Ahmad É—in ya taresa da faÉ—in, “Please Mawashi ka gafarce ni!”.
“Akan me? Ahmad kaida ka taimakeni ka kawo min aunty Khadijah akan lokaci, ni ya kamata na nema afuwar taso ku da nai a daren nan”.
Kai Ahmad ya girgiza masa da cewa “Aliyu laifina ne, na aikata kuskure”.
Sosai Æ™irjin Smart yay masifar bugawa, dan abinda Ahmad ke nufi daban shi abinda zuciyarsa ta kawo masa daban. Sai kuma yay saurin ture hakan a ransa ya zubama Ahmad É—in idanu. “Mi kake son faÉ—a Ahmad, ka bani abuÉ—e kasan bana son kwana-kwana”.
Hannu Ahmad ya kai saman kansa ya shafa, sai kuma ya furzar da huci mai Æ™arfi. “Na zuba abu a cikin FURAR nan É—aya. Saboda ma an tabbatar min maganin nada Æ™arfi yasa na saka É—aya kawai, sai dai zuciyata taita angizani akan na Æ™ara ta yadda zaka kasa control É—in kanka har sai ka tabbatar da abinda muke fata.”
Shiru kawai Smart yay yana kallon Æ™asa hannayensa duka a cikin aljihun dogon wandonsa. Kamar bazaice komai ba sai kuma ya É—ago ya dubi Ahmad É—in yay Æ™aramin murmushi da sai ka Æ™ura masa ido zaka tabbatar yayi. “Baka jin magana Ahmad sam wlhy, ban san mi kake nufi zakai kenan ba ai da ban yarda munsha furar da ka kawo É—in ba. Amma ka rubuta ka ajiye zan rama nima”.
Ba haka Ahmad yay zaton ji ba dan haka ya zuba masa idanu kawai yana kallonsa. ÆŠauke kai Smart yay gefe da sake faÉ—in, “Ban san kallo malam kaje ka kai aunty Khadijah gida ta huta”.
Yanda Smart É—in yayi duk sai Ahmad ya sake jin jikinsa yay sanyi. Sai dai dole suka fito dan dare yaja kusan Æ™arfe biyu. Godiya Smart ya sakema aunty Khadijah tare da harar Ahmad da ke kallonsa har yanzu dan shi gani yake tamkar Smart É—in ya shanye komai ne kawai a ransa dan ganin aunty Khadijah. Bayan wucewarsu ya rufe ko'ina da kashe komai. ÆŠakin ya koma inda Lulu da aka sakama Æ™arin ruwa take. Ya jima tsaye yana kallonta wasu abubuwa masu girma game da ita na sake hauhawar farashi a zuciya da É“argonsa. Kafin ya lumshe idanunsa tare da ramÆ™wafawa kanta ya sumbaci goshinta da idanun nan da suka sha kuka yau da bakin tsiwar da ya tabbatar kona dare É—aya ne dai ya mutu murus yau. “ALLAH yay miki albarka _Noorun Nisaaa_” ya É—an ja sunan da hura mata iska akan idanunta yana murmushi mai sanyi Æ™asan zuciyarsa cike da É—unbin tausayinta...
Da ga haka ya miÆ™e ya nufi bedroom yana sauke tagwayen ajiyar zuciya. Jikinsa ya tsaftace. Koda ya fito maimakon kwanciya sallaya ya shimfiÉ—a ya fiskanci alÆ™ibla domin miÆ™a godiyarsa ga UBANGIJIN talikai mai rahama mai jin Æ™ai. Sai gabannin asuba da ya fuskanci ruwan daya saka mata na biyu da Aunty Khadijah ta bari ya Æ™are ya je ya cire shi ma. Zama yay kawai ya saka hannunta cikin nasa ya zuba mata ido, yanda take barcin da sauke numfashi a hankali lokaci zuwa lokaci takan saki ajiyar zuciya. Abubuwa da yawa yake nazarta a kanta. Tun daga randa ya fara ganinta a airport da yaje É—akkota har zuwa masifar da ya dinga ci a wajenta, aurensu da zaman sati uku da kwanaki huÉ—u yau cikon na biyar. Ya bata sunan HAWAINIYA da kan canja akowane lokaci da kuma kowane irin yanayi. Kai tsaye baka yanke mata hukunci akan kanta dan sanin ainahinta sai ALLAH. Wato duk bawan da kake kallo yana rayuwa akan kuskure ashe kai tsaye yanke masa hukunci da abinda idonka ya gani a kansa tamkar son zuciya ne. Duk wanda zai baka amsa a kanta zai ce maka she is bad girl ne kai tsaye, domin da wannan siffofin take bayyana kanta wa duniya. Dalilin shine haka aka raineta, haka ta tashi, da hakan kawai tai imani a matsayin gaskiya. “Lokaci yayi da zan san wacece ke Mawaddat? Wace irin turnuÆ™un Æ™ura kika tsallake a baya data gina miki rayuwa kamar haka? Wanene yaso lalata miki rayuwa? Miyasa mahaifinki ya nuna miki soyayya amma ya gagara tsayawa akan tarbiyyarki? Miyasa ahalinki sukai sakacin fuskantar rayuwarki na cikin wani Æ™ulli tun a gaÉ“ar da ya dace ace sun fuskanta É—in? Ina son sanin waÉ—an nan amsoshin da ga bakinki MATATA. na miki alÆ™awarin sake gina nagartacciyar rayuwar da zata fahimtar da ke tsakanin fari da baÆ™i koda sun gauraye a mazubi É—aya da izinin ALLAH. In sha ALLAHU zan share miki dukkanin hawayenki na zuci dana bayyane da tafukan hannayena na maye gurbinsu da tarin farin ciki Mawaddatan'warahmah”. Motsawar da tai ya bama hannunsu damar sake matsewa cikin na juna tamkar mai jaddada masa ta amshi dukkan kalamansa itama. Hakan ya sakashi lumshe idanu da sakin ajiyar zuciya...........✍️
No comments