Breaking News

Furar Danko 87

 


87


.........“Dada wane ɗa ne zai yi fushi da iyayensa. Balle ma ke nasan baki da laifi akan wannan al'amarin sam.”


     “Naji daɗi da ka fahimci haka Sulaiman, dan babu ta yanda zan goya bayan bare sama da jikana. A yanzu haka koda akai min katanga da bibiyar halin da kuke ciki ban zauna ba, kuma nayi alƙawarin sai Mawaddat ta dawo hanun Tajuddeen matsayin mata dan bazan taɓa amsar waninsa ba”.


   Wani irin farin ciki ne ya ratsa Alh. Sulaiman, dama shi yasan Dadarsa na tare da su. Dada dake murmushin itama ta ƙara ƙasa da murya da faɗin, “Labari ma mai da ɗi......” Tsaf ta kwashe yanda sukai da Lulu ta sanar masa. Baima san sanda ya lailayo wata ashariya ya dire ba a gaban mahaifiyar tasa. Ya ce, “No wander naga yaron nan Yousuf nata rawan kai, ashe shegen shine ya ƙulla komai”.


     “Wlhy kuwa, nima abin ya girgizani Sulaiman. Amma ka kwantar min da hankalinka jibi da kaina zanje na ɗakko Mawaddat ko yaron nan na yawo da ubansa a baya sai ya saketa”.


   “ALLAH ya barmin ke Dada ta”.


Ya faɗa cikin wani irin matsanancin farin ciki. Gaba ɗaya damuwarsa ta shafe ma. Bai iya dogon Zama ba a gidan bayan sun ɗan tattauna akan abinda ya samu Baba da ta bashi labari ya wuce gida kasancewar dare ya fara yi, yana tabbatar mata gobe idan ALLAH ya kaimu Tajuddeen zai zo ya gaidata, da dai ya ɗauki fushi bazai sake zuwa wajensu ba, amma yanzu zai lallasoshi, dan zai sanar masa ƙoƙarin da take masa. Sosai Dada taji daɗin hakan, dan ita kam ALLAH ya jarabceta da shegen ƙulafucin ƴaƴanta da ma jikokin duka. Sai dai kuma matan ƴaƴan nata da babu wanda ta ɗagema hula a rashin mutunci, juyasu take san ranta kamar waina a tanda kamar yanda ta kame ƴaƴan nata ram a hannu sai yanda tace musu, Alh. Sulaiman ɗin nema dai kan botsare mata a wasu lokutan dan shima dai halayyar tata ce ya ɗebo tsaf. Shiyyasa takanji shakkarsa duk da kasancewar itace ta haifesa, san nan tana sonshi sosai wannan a bayyane yake a wajen kowa ma, dan sam idan rashin mutuncinsa ya tashi ba raga mata yake ba tun ma yana ƙaraminsa, balle yanzu da yake jin ya gawurta da tumbatsa a gidan ta fanin dukiya da yin suna a cikin ƴaƴan nasu. Amma a kullum Dada bata ganin laifinsa sai ma bashi goyon baya da takeyi....


     __________★


    Matuƙar tashin hankali Smart ya shiga a lokacin da ya fahimci halin da Lulu ke ciki. Ta sanƙame masa babu alamar rai tattare da gangar jikinta, da ƙyar tunanin zuba mata ruwa yazo masa a rai, sai dai koda ya shafa mata ruwan ma shiru kake ji. Gaba ɗaya ruwan ya zazzage mata zuciyarsa na wani irin dokawa tamkar zata faso ƙirjinsa ta fito waje. Wata irin zaburowa tai jikinta na jijjiga. A tsahon rayuwarsa baya jin ya taɓa fuskantar makamancin farin ciki da tashin hankali masu gogayya da juna irin haka. Duk yanda yake tunanin iya shawo kan matsalar hakan ya gagara, dan yanayin nata ya wuce dukkan tunani. Yasan idan yace zai ɗauketa zuwa asibiti a wannan halin bazai ma iya driving ba, to yama manta motar su Amrah sun tafi da ita gida, dan haka ya shiga neman wayarsa. Da ƙyar ya iya samota a ƙasa harta fashe. Bai damu ba ya shiga neman Ahmad dan shine kawai yazo masa a rai. 


     Shigowar kiran ta saka Ahmad kwashewa da dariya, amma daya ɗaga sai ya dake dan shi duk tunaninsa Smart ya gano ne. Sai dai kuma jin muryarsa ta saka gabansa faɗuwa. Da sauri ya ce, “Mawashi Are you okay?”.


   “I am not Ahmad. Ina cikin tashin hankali ka taimakeni kazo mukai Mawaddat asibiti, Ahmad akwai matsala wlhy na saka yarinyar mutane a masifa....”


    Sosai zuciyar Ahmad ta jijjiga, amma sai yay saurin tarar numfashin Smart da faɗin, “Kaga Aliyu dan ALLAH ka kwantar da hankalinka, ka faɗamin mike faruwa ne. Ka sakani a tashin hankali nima....”


   Cikin ƙaraji Smart ya katsesa da “Mi kake son sani ne Ahmad!! Ina faɗa maka kazo muje asibiti kana gaya min na kwantar da hankalina na sanar maka mike faruwa?. Ahmad ka taimakeni karna rasata, bazan iya yafema kaina ba idan hakan ta kasance”. Ya ƙare maganar cikin sanyin murya hawaye masu zafi na gangaro masa a karo na farko... 


       Kaɗan ya rage Ahmad yin aman zuciyarsa. Muryarsa na rawa da daburcewa ya ce, “Ka.. ka yi haƙuri gani nan zuwa.” baima jira amsar Smart ɗin ba ya miƙe tare da figar jallabiya ya saka. Karo suka kusan ci da Coach da ke ƙoƙarin shigowa ɗakin nasa, da mamaki ya ce, “Ahmad kana lafiya kuwa? Ina zaka haka?”.


    “Yaya babu lafiya, na aikata babban kuskure wlhy.”


   “Kai miye haka wai, nutsu mana”.


 Coach ya sake faɗa yana riƙo Ahmad da ke ƙoƙarin turesa ya fita. 


     “Yaya dan ALLAH kayi haƙuri idan na dawo zan maka bayani. Aliyu ne ya kirani...”


  “Kai bana son shashancin ka nutsu kamun bayani mana”.


    Rasa mi Ahmad zaice yayi, sai kawai cikin matuƙar gundura ya ce, “Asibiti yaya. Asibiti zan kaisu, na tabbata koma minene yanada alaƙa da abinda na aikata wlhy. Dan girman ALLAH ka barni naje”.


      Hankalin Coach ya fara tashi shima, dan Ahmad yana magana ne kamar zai yi kuka. 


   “Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un. Ahmad Please ka faɗa min mike faruwa? Miya samu Aliyun ne? Mika aikata masa kuma?”.


      “Yaya nayi kuskure, abu na saka musu a fura, bana raba ɗayan biyu koma miya tada hankalin Mawashi nada alaƙa da abinda na aikata ɗin. Yaya kamarfa kuka yakeyi da tabbatar min zai rasata. Yaya ka barni naje dan ALLAH”.


    Kai Coach ya dafe domin ya samu amsar abinda ya kawoshi sashen ƙanin nasa dama. Dan dama matarsa ce ta bashi maganin da Ahmad ɗin ya yarda ɗazun batare da ya sani ba kuma an ɓalla maganin, kasancewarta likita yasa hankalinta tashi fahimtar maganin datai kona minene. Taso danne zuciyarta ta binciki Ahmad ɗin ita kaɗai amma saita kasa haƙuri ta tunkari mijin nata da batun shine dalilin fitiwarsa zuwa inda Ahmad yake. Yanzu kuwa jin zantukan Ahmad ɗin ya tabbatar masa su Aliyu ya bama maganin ke nan. Ba lokaci bane na dogon tunani, dan haka ya ciro wayarsa da ga aljihu yana faɗin, “Kaga bari Khadijah tazo kuje tare, yanzu dare yayi duk asibitin da zakuje zaku iya fuskantar matsalar ganin doctor.”


    Tuni Lulu ta sake fita a hayyacinta wa Smart, zuwa yanzu kam koda ya zuba mata ruwan ma batako motsa ba. Sai kawai ya dafe kansa dake wata irin masifar sara masa. Ya auna kiran Ammah sau shuri masaƙi zuciyarsa na gargaɗinsa. Hakama Abba. A wannan halin ya tsinkayi horn ɗin da yake ƙyautata zaton na Ahmad ne. Zumbur ya miƙe ya fito, dan yasan dole sai ya buɗe masa gate ya shigo. Doguwar riga ya samo ya saka mata, dama shi tuni ya suturta nasa jikin. Yana buɗe gate ɗin bai jira ƙarasa shigowar Ahmad ɗin ba ya juya cikin gidan da sassarfa. Fitowa aunty Khadijah tai tabi bayansa, yana ƙoƙarin shigewa bedroom ta kirayi sunansa. Da sauri ya juyo dan shi idonsa ma yay rufewar da bai kula da ita ba, sannan ya manta ma ita likita ce har sai da tai masa bayani. A tare suka shiga ɗakin, ta ajiye ɗan akwatin dake hannunta ta haura gadon ta ɗagota Lulu zuwa jikinta....


   Smart da gaba ɗaya dauriyarsa ta gama ƙarewa cikin sarƙewar murya ya ce, “Aunty mun rasata ko?”.


     “A'a Aliyu da ranta. Dan zuciyarta na harbawa suma tai kawai. Amma miya firgitata haka? Dan irin wannan sumar mai nauyi mummunar firgici ko tsorata mai tsanani akan abinda mutum baya so ke kawota”.


    Kasa bata amsa yay dan tana cikin mutanen da a rayuwa yake matuƙar ganin girma da jin kunya. Itama fahimtar hakan ya sata cewa, “Shike nan ɗan bani waje mugani”. Babu musu ya fita, inda ya samu Ahmad a falo na faman kai kawo. Da sauri ya taresa da tambayar “Ya ake ciki?”. Zaune Smart ya kai cikin kujera dan ji yake jiri na ɗibarsa kamar zai zube a ƙasa shima. Ya dafe kansa da duka hannayensa kamar bazai cema Ahmad ɗin komai ba. Sai zuwa can ya furzar da zazzafan numfashi ya ɗan kallesa ya girgiza kansa, dai-dai nan Aunty Khadijah ta leƙo ta sake kiransa. Ta shi yay cikin ƙarfin hali ya nufi ɗakin. Batare da aunty Khadijah ta kallesa ba tace, “Kaimin ita Bathroom ka sakata a ruwan dana haɗa, ka riketa da ƙyau dan zata iya zabura”.


   Duk yanda tace masan hakan yayi, sai ko gashi Lulu tai wata gigitacciyar zabura lokacin da yake sakata a ruwan. Da ƙyar ya iya rirriƙeta ajiyar zuciya mai nauyi na suɓuce masa yayinda wanin sashe na zuciyarsa ke matuƙar jin tausayinta da jin haushin kansa mai tsananin gaske. Sai da ta shafe kusan minti biyu tana fisge-fisgen kafin ta saki wani irin kuka mai tsuma zuciya tana mai ambaton sunansa da kausasashiyar muryar ta data gama ɗashewa cikin roƙo da magiyar ya barta, karya aikata. Kalamaine data dinga roƙonsa da su a lokacin da ya gaza amsa mata dan yakai fagen da bazai iya fahimtarta ba a lokacin. Goshinsa ya haɗe da nata yana ambaton, “Kiyi haƙuri Mawaddat kiyi haƙu......”


    Bai kai ƙarshen kalma ta ƙarshen biyar ɗin ba ta ƙwalla wani masifaffen ƙara da zabura........✍️

No comments