Breaking News

Furar Danko 85

 85



.........Lulu duk da ranta a dagule yake tayi dauriyar dannewa saboda yaran, kasancewar Maryam akwai hankali tunda daddare ta tsara musu su tafi yau suba ma'auratan waje, sai kuma akai sa'a har su Amrah suka fahimceta. Koda gari ya waye sukaga basu fito ba basu damu ba suka gyara gidan tsaf sukai break fast. Nasu sukaci suka shirya musu nasu a table. Sun kammala kenan Lulu ta fito. Gaisheta sukai su duka cikin haÉ—a baki, ta amsa musu tana murmushin Æ™arfin hali, dan girmamawa na É—aya da ga cikin abinda Lulu keso gana Æ™asa da ita. Wannan kuma shine mataki na farko da dangin Smart suka kama mata zuciya da shi, yau gashi har Æ™annenta sun kwatanta abinda bata taÉ“a gani ba. Kamar yanda suka tsara Maryam ce ta sanar mata zasuje gidan Æ™unshi su taho da mai Æ™unshi da tace tana so. Lulu bata kawo komai a ranta ba ta ce, “Da sassafen nan kuma Maryam. Ku bari sai anjima ni Æ™unshin ma kamar na fasa kuma”.


    “Kai aunty dan ALLAH karki fasa. Ai zamuje ne dan ta sani inma tanada wani aiki kinga ta kammala da wuri bawai yanzu zata zo ba”.


   “To shike nan, amma har ku duka zakije?”.


  A tare suka amsa mata da eh. Key É—in motar ta dake a falon ta miÆ™ama Amrah dan sun iya driving duk da dai ba basu mota ake ba sai ta kama. Cikin gargaÉ—i tare, “Banda ganganci Please”. Dariya kawai su Afrah sukai dan sun san dai aunty Lu.. É—in su indai tuÆ™in ganganci ne ita É—in master ce. Sallama sukai mata suka fice, dama sun fidda kayansu tun É—azun..


   Kwanciya tai a falon batare da neman abincin da zata ci ba duk da kusan goma ne yanzun. Tana a wajen kwance ba barci take ba har sha biyu, tunanin abubuwa kawai take daban-daban, babu alamar su Maryam dan haka ta É—aga waya tai kiran su Amrah. Cikin dariya suke sanar mata ai su suna ma gida, sai da suka fara ajiye su Asma'u ma sannan. Shiru kawai tai da mamakin wai ita yaran nan zasu yaudara, sai kawai tai Æ™wafa ta yanke kiran. ÆŠan jimm tai saboda abinda take jiyowa kamar Æ™aÆ™arin amai, kamar zata share sai kuma ta miÆ™e da sauri jin abin na Æ™aruwa. Sam batai tunanin Smart na gidan ba, É—akin nasa ta shiga dan anan take jiyowa, nan É—inne kuwa a cikin toilet, mamaki ya kamata duk da matsanancin haushinsa da take ji na abinda ya faru sai ta nufi bayin. Sosai gabanta ya faÉ—i, har bata ma san sanda ta afka bayin ba inda yake.


    “Lafiya kake kuwa?”.


  Bai iya bata amsa ba dan ya gama galabaita da aman, dole ta ajiye komai da ke ranta kuma ta shiga taimaka masa ya wanke bakinsa da fuska, da taimakonta ya fito ya sake hawa gadon ya kwanta. 


      “Please lulluÉ“e ni”.


    Ya faÉ—a da Æ™yar. LulluÉ“e san tai hankalinta a tashe, dai-dai nan kiran Ahmad ya shigo wayarsa, har ya lumshe idanunsa ya buÉ—e, ita ya kalla yayinda ita kuma take kallon wayar. “Waye?”. Ya faÉ—a a hankali. Wayar ta miÆ™o masa da faÉ—in, “Besty kasa”. Sake maida idanun nasa yay ya lumshe da faÉ—in, “Ahmad ne É—aga”. Kafin ta É—aga É—in wayar ta yanke, tana Æ™oÆ™arin kira Ahmad É—in ya sake kira. ÆŠagawa tai ta saka a Hansfree da faÉ—in “Hello”. Daga can Ahmad ya amsa mata duk da yayi mamakin jin wayar a hannunta. Gaisheshi tai da sanar masa bai da lafiya. 


     Hankali tashe Ahmad ya ce, “Ya ALLAH gani a Æ™ofar gate ai”. 


  “Okay to bara ina zuwa”.


Tai maganar tana yanke kiran. Wayar ta ajiye ta miÆ™e, Smart da ke saurarensu ya buÉ—e idanunsa a kanta, a hankali ya furta “Please kar ki fita a haka kisa hijjab”. Harararsa tai batare da tace komai ba ta fice. Samun kanta tai da shiga É—akinta ta É—auka hijjab É—in ta saka sannan taje ta buÉ—ema Ahmad É—in. Ita tai masa rakkiya har É—akin Smart É—in ta fito ta barsu. 


     Bayan Ahmad yay masa sannu ya ce, “Tashi zakai mu tafi asibiti”.


Kai Smart ya girgiza masa yana É—an buÉ—e idanunsa, “Basai naje asibiti ba zai bari da kansa in sha ALLAH. Tunda ma na samu nayi aman shike nan”.


   Ahmad ya riga da yasan miye matsalar Smart É—in. Dan haka yay shiru kawai. Dai-dai nan Lulu ta shigo É—akin da sallama. Amsa mata Ahmad yayi. Ta ajiye tray data haÉ—o abincin tana faÉ—in “Ya sanar maka abinda ke damun nasa kai ko?”. Murmushi Ahmad yay da bata amsa. “Kin san mutumin naki ai, yanzu ma fama nake da shi muje asibiti yaÆ™i”.


     Kallonta takai kan Smart, ganin shima ita yake kallo Æ™asa-Æ™asa saita janye nata da É—an taÉ“e baki. Shi Ahmad ma sai suka bashi dariya. Dan haka ya miÆ™e. “Inaga bashi abincin ni bari naje na samo masa magani, dan tunda yace bazaije asibitin ba to bazai je ba”. Bai jira cewarta ba ya fice. ÆŠan hararar Smart Lulu tayi, a taÆ™aice ta ce, “Ka tashi”. Sake buÉ—e idanun nasa yay ya zuba mata su na kusan minti É—aya, ita kuma ta kauda nata dan tun É—azun yanda idanun nasa launinsu ya sake canjawa suka fito a sak na macizan da take kiransu taji bata son ya kalleta. Hannu ya miÆ™a mata alamar ta kamashi. Kamar zata share sai kuma dai ta kama dan ya É—an bata tausayi kuma. Harya faÉ—a kamar wanda ya kwana biyu yana ciwon. Shayin data haÉ—o masa ta miÆ™a masa, babu musu ya amsa tare da motsa lips É—insa kaÉ—an ya ce, “Thanks”. Koda ta miÆ™a masa soyayyan doyan sai ya girgiza mata kai alamar bazai ci ba. Kamar zatai magana sai kuma ta fasa ta maida doyar ta ajiye. Tana zaune ta É—an juya masa baya tana latsa wayarta har ya kammala, kofin ya miÆ™a mata ya koma ya kwanta, ta tattare kayan ta fita da su, a lokacin kuma Ahmad ya dawo, ruwan da ya buÆ™ata da Smart É—in zai sha magani ta É—akko masa, da ga haka ta koma falo tai zamanta...


   Ahmad bai bar gidan ba sai da Smart ya samu barci, bayan wucewarsa Lulu ta leÆ™asa, ganin yay barci ta É—an sauke ajiyar zuciya da hararsa kamar yasan tanayi. ÆŠakinta ta nufa ta É—an kwanta itama dan shirun gidan kuma duk sai yay mata babu daÉ—i. Kusan a tare suka tashi bayan la'asar, tai wanka tai salla dan yanzu kam Alhamdullah, idan ma tai kamar zatai sakaci lokaci ya wuce sai taji duk babu daÉ—i har sai ta tashi tayi sallar take samun nutsuwa. Cikin skert dogo baÆ™i da Æ™aramar top baÆ™a itama datai mata É—as a jiki ta fito, kanta babu É—ankwali sai gashin da ya sha gyara yanata walÆ™iya. Wayar da take dannawa tana charting da aunty Naja'atu yasa bata lura da shi ba har sai da takai zaune. Shiko tun fitowarta ya zuba mata idanu, murmushin da take yi ya matuÆ™ar Æ™awata Æ™yawunta da motsa rauninsa. Hakama kwalliyar tata ta É—auki hankalinsa duk da ita hakan normal ne a gareta badan wani birge miji ko wani abu ta saka ba tunda dai sune kayanta na koyaushe fiye da atamfa. Ƙaramin gyaran murya da yay ya sata farga da shi, dariyar da takeyi a hankali ta haÉ—iye ta É—ago idanunta da sukai wani tar-tar da su da haske mai É—aukar hankali kasancewar duk yau da ba'asha komai ba. 


   “Dama haka ake jiyyar mara lafiya Madam?”.


   Hararsa ta É—anyi da taÉ“e baki. “Ka dai san mai jiyyarka ba dai Mawaddat ba”.


     “Uhm hakane ashe Ahmad ne kuma fa”. 


    Ya faÉ—a yana danne dariyarsa. 


  Sake taÉ“e bakin tai taÆ™i cewa komai. Da ga haka shiru ya ratsa falon, yana tunanin faÉ—a mata zancen tafiyarsa da ya taso ne, dan abinda ma ya kawo Ahmad kenan, amma sai yaga bari dai ya bari ta sake nutsuwa ko zuwa gobe in sha ALLAHU. Kusan mintuna goma ya sake takalota da faÉ—in, “Ba abinci gidan ne? Ina kuma yaran nan banji motsinsu ba?”.


      Yanzu kam kai tsaye ta bashi amsa da “Sun wuce”.


   “Abincin fa?”.


“Na daina girki a gidan nan”.


“Miyasa?”.


   “Ba sai da dalili ba, dama can ra'ayi nayi, yanzu kuma na daina sai ka bari sai ka auro matar da zata maka”.


      “Kishiya kike sha'awa kenan?”.


   Kamar bazata tanka masa ba sai kuma tai murmushi. “Sai dai idan yau zaka aurota ko gobe kafin cikar jibi da zan Æ™ara gaba maybe wasu su kalleta a matsayin hakan”.


    Murmushi kawai ya saki, maimakon cewa wani abu akan batun nata sai cewa yay “Bani furar da Ahmad ya kawo Please dan yunwa nake ji”. Kamar bazata je É—in ba sai kuma ta miÆ™e. Babu jimawa ta dawo da furan da kofi ta ajiye masa ta koma inda ta tashi. Television ta kunna shi kuma ya zuba furar ya fara sha. 


  “K mi kika ci?”.


 “Ba buÆ™ata”.


Ta faÉ—a a takaice. 


   “Okay amma da kinsha furan da ga gidan Ammah ya amso ta”.


   ÆŠagowa tai ta kallesa. Sai ya jinjina mata kai alamar tabbatarwa. 


      “Gama ka bani kofin bana jin sake tashi”. Ta faÉ—a tana maida kanta ga wayarta. Bai sake magana ba har ya gama É—in ya zuba mata, sai dai bata da yawa dan haka ya miÆ™e da kansa yaje kitchen ya sake É—akko wata ya Æ™arasa cika kofin ya miÆ™a mata. Hankalinta nakan waya take shan furar harta shanye, sake Æ™arawa tai. Sai da ta shanye ta biyun yay Æ™aramar dariya da faÉ—in, “Babu wata furar Ammah da kika sha yarinya a titi ya sayota”. Da sauri ta kallesa tana yamutsa fuska, ya sake sakin dariya da nuna mata 8-10. Filo ta É—auka ta jefa masa da yin Æ™wafa tana harararsa, sai kuma ta fara Æ™aÆ™arin amai shiko ya cigaba da dariyarsa. Kofin takai kitchen ta wanke dan bata Æ™aunar Æ™azanta, duk da kuwa aikin na cimata rai dan ma yana Æ™oÆ™arin taya ta ne, tun tana Æ™orafin mai aiki har ma ta bari tunda dai taga kwanakin sun Æ™are mata a gidan. Falon ta dawo ta cigaba da É—an kallon abubuwa a TikTok. Shiko yana kwance shiru ya zuba mata ido ta Æ™asa kawai yana kallonta. Kiran sallar magrib ne ya tadasu su duka. Smart ya wuce massalaci ita kuma ta tafi É—aki. Bai jimaba ya dawo gidan saboda abinda ke damunsa ba wai ya gama sakinsa bane gaba É—aya, jarumtar da ya saba ce kawai ta dannewa. Bai samu Lulu a É—akin ba dan itama tana nata É—akin a cikin makamancin irin nasa yanayin koma ace wanda yafi nasan. Dan wani abu ne ke faman ratsa mata jiki mai ban mamaki. Ga tsigar jikinta sai faman tashi take kamar mai jin sanyi. Al'amarin kamar wasa sai ya fara neman fin Æ™arfin Lulu, dan da Æ™yar ta iya tashi tai sallar isha'i........✍️


   ðŸ˜µ‍💫Lulun mu muya hwaru kuma🥲?

No comments