Breaking News

Furar Danko 83

 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲






  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗




           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻



𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 8️⃣3️⃣




........Bayan an idar da salla har ya nufo hanyar gidan sai kuma ya dakata. Napep ya tare ya shiga tare da gaya masa inda zai kaisa. Cikin ka ƙanƙanin lokaci suka iso. Ya biya sa kudinsa sannan ya shiga gidan bayan sun gaisa da maigadi. Ahmad na zaune a falonsa ya barbaza takardu ga laptop a gabansa Smart ya shigo. Ɗagowa yay yana kallonsa cikin nuna mamaki. Smart ya watsa masa harara da faɗin, “Lafiya kake kallona?”.


   “Inafa lafiya, kai da nake tunanin kana can kana aikin ALLAH yanzu kodan kewar juna da akai amma sai na ganka anan”.


      Ƙaramin tsaki Smart yay yana kaiwa zaune da faɗin, “Banza ɗan iska kaifa baka tauna magana kafin ta fito maka a baki”.


   Dariya Ahmad yayi da cewa, “Gara na dinga muku ɓaro-ɓaro kuyi ku aurar dani kuma ku huta. Amma fa sai naga kamar kana cikin damuwa. ALLAH dai yasa ba wani abu ka tarar a gidan ba?”.


     Smart baida yawan magana. Sannan akwai zurfin ciki. Duk abinda kaga ya bayyana shi ga waninsa to lallai ya matuƙar girgiza shi ne. Sosai ya nisa da furzar da iska mai zafi. “Ahmad akwai matsala ne”.


    “Ya salam matsala kuma Mawashin. To tami? Akan kuma mi?”.


  Shiru kamar bazai ce komai ba, sai kuma ya ɗago yana kallon Ahamd ɗin da shima ya zuba masa idanu. “Badan ina son fara tona sirrin gidana bane, al'amarin ya girgiza nine ina buƙatar shawara dan kar na aikata abinda ba haka yake ba. Bayan kun saukeni na shiga gida sai na samu.......”


   Tsaf ya zayyane masa abinda yaji tsakanin Lulu da Dada na tattaunawa. Shima kansa Ahmad yasha mamaki. Amma sai ya dafa Smart yana jinjina kansa. “Niko kaga ko bana jin shi Yaya Yousuf da wata manufa yay hakan. Domin idan ka auna zancen tsohuwar zaginsa take akai-kaice shima. Sai naga yayine domin ma Mawaddat wayo kawai”.


      “To miye na wayon anan Ahmad, aure ne fa kuma ta isa aure tunda ba gunkinta zasuyi su kafe a gidan ba. Kawai dai akwai abinda suke shiryawa a kaina na yaudara”.


   “No no relax kar kabari ka yarda da hakan. Sam sam bazaiyi hakan ba. Amma ina zuwa dai”. Waya Ahmad ya ɗakko yay kiran Uncle Yousuf. Da ƙyar ya samu ya shiga kasancewar har yanzu bai dawo ƙasar ba. Sun gaisa cikin mutunta juna batare daya nuna yana tare da Smart ba. Uncle Yousuf daga can cikin tsokana yace, “Yaya dai Auta ko batun auren ne ya tashi akeso na fara haɗo lefe?”.


       Dariya Ahmad yayi da faɗin, “Kai haba Yaya a'a. Wannan ai sai kun yarda da zaɓina sannan zamuje wannan matakin. Duk da nasan ma kunaji da gudu zaku amince. Wani abu ne fa da na jiyo ya girgizani. Sai nace bari dai na kiraka ko kasan da zancen”.


    “Oh to Masha ALLAH, ALLAH ya tabbatar da khairan sa. Minene kake son ji haka?”.


   “Uhm wlhy Yaya nafaje gidan Smart ne ɗazun sai na samu Mawaddat na waya cewar ai ta kusa komawa free nan da 4days aurenta zai ƙare da Aliyu. Abin ya girgizani matuƙa”.


     “Ya Arrahaman”. Uncle Yousuf ya faɗa daga can cikin dafe kai. “Yaya kama sani kenan?”. Numfashi Uncle Yousuf yaja da saukewa. Sannan cikin nutsuwa ya sanarma Ahmad yanda akai zancen ya fito, ya ɗora da faɗin, “Ni ko ma Aliyun bamma maganar ba dan ba haka bane a raina. Wannan auren ina fatan sai mutuwa ce zata rabashi. Na saki jiki ne da tunanin tana zuwa gidansa zaibi duk hanyar daya dace wajen mantar da ita wannan shirmen. To ashe wata sabuwa ita hakan na ranta. Dole ne na kira Aliyu na sanar masa komai sannan kuma ya ɗauki duk ma matakin daya dace akan hakan. Amma zanyi ƙoƙarin dawowa nima duk da ban gama abinda nake ba. Dan ALLAH kaima ina son ka zaunar da Aliyu ka nuna masa abinda ya dace akan wannan batun. Idan ma yana ma Mawaddat saku-saku ne ya ajiye gefe ya koma wuta-wuta tasan shi bamu bane ba. Idan komai ya daidaita ya mata sauƙin”.


   “Shike nan Yaya insha ALLAHU yanda mukai da shi zakaji”. Daga haka ya yanke kiran. Smart yaji komai dan a hansfree yasa baya buƙatar ƙarin bayani, sai ma ajiyar zuciya da ya sauke dan ya fahimci Uncle Yousuf ɗin da manufarsa akan hakan. Ya kuma daina ganin laifinsa dan ko shine abinda zai yi kenan domin toshe kowace matsala da zata iya ta taso a lokacin.... Ahmad ne ya katse masa tunani da faɗin, “Mawashi a yanzu fa wannan yaƙin naka ne bana wani ba. Kai ya kamata ka nuna mazantaka komai ma za'ayi ayi karka biye mata. Sannan na fahimci kamar ido ka kawo ka zubamata shiyyasa ma take ganin komai normal ne. Dole fa kai ƙoƙarin dashen shukarka dan hana kowace irin barazana tasiri. Dan hatta da ita kanta hakan da zakai zai karya lagonta dan bazata taɓa yarda a tunɓuke wannan shukarba”.


   Tsaf Smart ya fahimcesa dan haka yay ɗan gajeren murmushi yana girgiza kai. “Ahmad bazaka fahimta ba. Mawaddat fa ta wuce duk yanda kake tunani. Sannan ni harga ALLAH bana son zuwa gareta batare da amincewarta ba. Shiyyasa na sake mata tare da nuna mata har yanzun a ƙasan nata nake dan hakan ne kawai zai iya karya lagonta harta saki jiki dani. Kuma Alhmdllh naga hakan yana tasiri sosai akanta . Taya kake tunanin yanzu na tunkareta da wannan sigar ai babu zaman lafiya”.


   “Humm kaifa na manta ashe sunanka namiji ɗaya tilo a tsakkiyar ƴaƴa mata shiyyasa. Mawashi na yarda da yanda ka tsara ɗin kuma hakan ma hanyar maslaha ce mai ƙyau da anan gaba ita kanta sai tayi alfahari da kai. Amma kai ya kamata ka memo hanyar da zakabi ta amince maka da kan nata ku zama ɗayan. Mudai fatan mu ai ayi shukar dan shi kaɗaine nake ganin zai hanata kowane irin motsi musamman daya kasance a yanzu tanada defenders a gefe kuma masu ƙarfi.”


    “Na yarda da kai, amma kuma tayaya zanyi hakan batare dana ɓata abinda na fara ginawa a zamanmu ba?”.


   Dariya sosai Ahmad ya shigayi har sai da Smart ya fara ƙuluwa sannan ya sassauta. Ya ce, “Shiyyasa nace kaifa gata yay maka yawa na kasancewarka ɗa namiji ɗaya tilo a tsakkiyar mata shiyyasa abubuwa da yawa kai hoto ne. Karka damu wannan aikina ne. Kai dai yanzu tashi ka koma gida ka maida komai ba komai ba. Amma yaran nan data cika gida da su ka tattarasu gobe su koma gida”.


      Cikin ɗan taɓe baki Smart yace, “Dama zasu koma goben ne ai saboda school. Amma ka faɗamin mi zakayi?”


   “Babu ruwanka da abinda zanyi, ai kasan dai bazan cutar da kai ba.”


  “Na sani, amma dai ya kamata ace na sani ko”.


     “Karka damu zaka sani, nima sai nayi mazari”


  Daga haka suka fito anan massalacin ƙofar gidan su Ahamd sukai salla. Ya amshi key ɗin motar Ahmad ya wuce gida. Yanzu kam ya samesu su duka a falo suna kallo. Sannu da zuwa suka shiga masa a zatonsu isowar kenan. Ya zauna yana amsa musu da tambayar lafiyarsu. Lulu na zaune a ƙasa tana shan fruits da aka yayyanka a bowl. Ta sauya kaya alamar wanka tayi, dan wando ne da riga marasa nauyi a jikinta. Kan babu ɗan kwali ya dai sha gyaran da sukayo yau sai ƙyalli yake yi. Idanunsa ya ɗan lumshe da sake lafewa cikin kujerar zantukan Ahmad na dawo masa a rai dalla-dalla. Shi yasan akwai ƙura, dan ko za'a kaisa jail sakinta bazai taɓayi ba koda a mafarki ne. Maryam ce data kawo masa abinda yace a masa cikin hikima ta janye su Amrah suka koma ɗaki tunda acan ma akwai tv. Lulu ta bisu da kallo tana faɗin, “Ku kuma ina zaku muna hira?”. Da dariya Maryam tace, “Aunty muna zuwa sirri zamuyi mu dawo yanzun”.


    “To ALLAH dai yasa bani za'a ƙullawa ba”. 


  Dariya suka shige sunayi, yayinda Smart ya sakko ya zauna a ƙasan kusa da ita. Hannunta ya riƙo ya kai apple ɗin data ciro jikin cokalin bakinsa. Juyowa tai ta hararesa. Yay murmushi da ɗan kashe mata ido ɗaya. “Idan ma ke zasu ƙullawa ba gani a kusa da ke ba sai na kunceki tsaf na maida igiyar kansu Madam”.


    “A'a Granny ƙarewar Madam”. Ta faɗa tana sake balla masa harara. Dariya yayi yanzu kam fararen haƙoransa na bayyana da ƙyau. Sai da taji wani zuuu cikin kanta amma tai azamar ɗauke idanun cikin basarwa. Shiko ya cigaba da faɗin, “Ai ki godema ALLAH da baki zo a kakar tawa ba. Gaskiya da Kinga takanki dan sai na addabeki”.


    “Sai dai ko mu addabi juna. Dan kaima kasan Lulu ƙamshi ba kanwar lasa bace.”


   “Niko nasan haka”.


 Ya faɗa cikin ɗage gira. Kankanar data tsiro ta tura masa a baki tana harararsa. Ya shiga shan abarsa yana murmushi. Itako ta maida hankalinta a kallon da sukeyi dan tana matuƙar son film ɗin duk da horro ne. Shima gyara zamansa yayi ya matsa jikinta sosai ya jingina bayansa da kujera kamar yanda tayi. “Wai sai sha kike baƙya bani ALLAH sarki autan Ammah akwai haƙuri”. Ya faɗa a mararairaice. Juyowa tai ta kallesa, sai kuma ta kalla fruits ɗin. “Oh kace kwaɗayi ya zaunar dakai nan ɗin ba kallo ba ashe?”.


    “To kusan haka”.


  Ya bata amsa yana shafar sumar kansa da bata da yawa can sosai, sannan tafi saisaye kuma. “Kwaɗayi dai mabuɗin wahala ne” ta faɗa tana tsiro abarba ta miƙa masa. Maimakon ya amsa cokalin sai ya riƙe hanunta ya kai abarbar bakinsa a haka da nata hannun. Batace komai ba ta janye hanunta daga nasan. Sai ta koma idan ta sha saita tsira ta miƙa masan, shi kuma ya riƙe hannun nata ya kai bakinsa. Harda ɗan kwanto kansa a kafaɗarta kaɗan. Shagala datai a kallon yasa bata maida hankali ba duk da tabbas tana jin kan nasa a kafaɗarta sai dai ba sakar mata nauyi yay ba sosai.


     “Wai ko ki tambaya inda naje, da zan tafi baki tambaya ba. Ina can munyi waya baki tambaya ba. Na dawo ma haka. Anya zaman tare yace haka Mawaddatan'warahmah”.


   Yanda ya kirayi sunan nata sai da taji zuciyarta ta motsa. Duk da kuwa Uncle Yousuf kan kirata da sunan lokaci zuwa lokaci. Kansa da ke a kafaɗarta ta ture da faɗin, “Mi haɗina da tafiyarka da dole zan dage sai naji. Ko salan a kirani mai gulma kuma”.


      “Haka ne kuma fa”.


   Ya bata amsa cikin rashin damuwa. Sai kuma ya jawo tray ɗin da Maryam ta ajiye ya buɗe ƙaramin flaks da ta saka kunun madara a ciki ya zuba a cup, kaɗan yasa suga. Ya fara sha ya lura tana kallonsa. Kofin ya miƙa mata batare da yayi magana ba. Sai ta ɗan yamutsa fuska tana girgiza kanta. 


      “Da akwai daɗi fa, ɗan-ɗana kaɗan kiji”.


   Kamar bazata amsa ba sai kuma dai ta amsa ɗin, kaɗan ta ɗibo a spoon ɗin takai baki. Sai ta ƙara ɗibowa tana kallonsa. “Akwai fa daɗi, ni dana ga tanata haɗa-haɗa sai na ɗauka jagwalgwali ne kawai”. 


    Murmushi yay mata da amshe spoon ɗin yana faɗin, “Karkuma ki shanye min to daga tayi”.


   “Oh ashe ba daɗi ni ka shanye mun fruits ɗina.”


       “Tofa gori ne abun? To shikenan musha”. Ya faɗa yana miƙa mata. Amsa tai ta sha ta miƙa masa itama, haka suka dingayi yanzun ma dai da spoon ɗaya suna kallo. Ya ƙare ya sake ƙara musu wani. Sai gashi sun shanye kunun flaks ɗin duka. Farfesun dake cikin kwanon kuma bai ciyu ba. Suna a falon har sai da Film ɗin ya ƙare. Shi ya kwashe kayan ya kai kitchen tare da kashe komai ya rufe ƙofar. Ita kuma ta tattara kayanta ta wuce ɗakinta ko sai da safe babu. Da kallo kawai ya bita yana girgiza kai, shima sai ya nufi nasa ɗakin. Sai da ya kammala komai na al'adarsa kafin kwanciya sannan ya canja kayansa zuwa na barci yasa turare yay brush ya fice. Lulu na zaune a tsakkiyar gadonta tana aiki a system ya shigo. Kallonsa take da mamaki daga sama har ƙasa. Kafin cikin ƙarfin hali ta ce, “Lafiya kuwa?”.


     “Ƙalau”.


   Ya faɗa a taƙaice yana hayewa gadon.......✍️


    😜Wace gulma ta kawoshi ka to🚴

No comments