Breaking News

AQIDARMU Book 2 Page 9

 🅿️9️⃣







Gyaran murya Dr yayi ya furta Alhaji bisimilla da kyar baba ya iya zama baima yi magana ba dr ya fara magana



An turo mana da umarni daga headquater na abuja cewa wannan yarinyar ta ka matar aure ce don haka mijinta ya saka hannu cewa in bamu sake ta a yau ba zamu fuskanci hukunci daga babban kotun duniya wanda a gaskiya mu arfinmu iya Nageria ne ba zamu iya wata shari'a da kotun duniya ba 




Yawu baba ya ha'diya ya kasa magana Dr yaci gaba 




Alhaji inaso kayi hakuri abokin aikina yamin bayanin dalilin da yasa is kawo ta amma shawarata shine ka tafi da ita ku zauna ku fahimci juna shi banbancin AQIDA har duniya ta na'de baza'a dainaba domin et har qarshen duniya za'a yi izala, 'darika, tijjaniya, shi'a da sauransu zagi da cin mutunci da gaba bashi bane mafita a tsakaninmu domin ita rahama da shiriya hannun ubangiji take wani iyayensa da kakanninsa 'yen IZALA shi ya zama 'dan shi'a wani a farkon rayiwarsa 'dan IZALA a qarshe ya qare a shi'a Allah shine mai juya al'amuransa idan har bamu mutu ba bamu cire rai da ikon Allah don hak... Baba ya miqe yace nagode 



Ok Dr yace bari na ta fito ya kira waya suna gun a ka fito da Mimi hibinta har qasa kanta na asa baba ya fita ta bishi.. 




Kallon Lauyan Najwa tayi tace ka tabbata duk hujjojin da mu ke da su sun isa.? Lauyan yace eh IA kuma monday zan gana gana da wancn lauyan 







Suna isa gidan su ka goggo su ka rungumeta ganin yadda ta zama kamar ku'din guziri dada tace muje kiyi et wanka kici abinci 





Baba ya kalli Salman yace na kai hannunta iyaka lamarin nan ya gundureni yanzu ko kai zaka qarasa kamar yadda kai ka 'daura musu auren haka yanzu ko kai zaka tabbatar ya kammala sakinta kafin ta haifi wannan qadararren cikin domin zai zama mune sakarkaru idan har ta qara haihuwa da wannan halakakken 



Ajiyar zuciya Salman yayi yace IA baba..





A asibitin kuwa Hayat ba alamar fita comma jiya i yau 




Bayan tayi sallah azahar tana zaune kan dadduma addu'a take yi masa sosai dukda yanzu hawaye ma sun daina fito mata 





Salman yana fita goggo asma ya kira ya bata labarin komai shiru tayi duk surutunta ta jiyo muryarsa 



Goggo inaso yadda kika shawo kan mimi ta yadda da auren nan kizo mu ingénieur shawo kanta cikin kwanciyar hankali ta rabu da 'dan shi'ar nan 



Ajiyar zuciya goggo tayi tace Salman rabuwa da 'ya'ya bakwai da kuma wani cikin.? Yawun takaici ya ha'diya kaddai itama goggo asma tana bayan mimi ya jiyo muryarta 



Salman akwai abinda in Allah ya tsarashi wlh ko duniya zasu ha'du basu iya rusashi, auren mimi da wannan balaraben tsarin Allah ne domin ina tabbatar maka ni kaina ranar da ka fara fa'damin maganar auren sai da nayi mafarkin Mimi tsakanin tsuntsaye tanata musu wasa tana murmushi ban fahimci manufar mafarkin ba sai da ka kirani kacemin mimi tayi haihuwa ta biyu sannan yara uku wlh Salman ya kamata ka janye ka kiyaye shiga hurumin ubangiji tun Farko shine mijinta uban 'ya'yanta da Allah ya halitta ta domin sa Allah ya rubuta auren na su ne a yadda mu ka tsara ni da kai bawai mune mu ka tsara ba tun can rubutacce ne don haka Ni babu ruwana zunubin da nayi a baya na roqi Allah amma yanzu bazan qara shigar da kaina cikin hurumin Ubangiji ba kaima ka kiyaye AQIDA ba hauka bane Allah shi ke da iko kan komai babu wanda yasan arshensa da zamu shantake a duniya muna cewa wane 'dan wuta ne ko da kuwa munga mutum cikin karkataciyar hanya addu'a ce tamu domin Allah zai iya shiryashi kafin mutuwarsa kai tayi kuma da ke kan hanya ka ta'be yayin mutuwarka kamar yadda yazo a hadisi guda Allah ya ganar da mu yasa mu gane banbancin AQIDA da alhaki domin dayawa ana zalunci a danganta hakan da AQIDAR mutun bayan babu inda Allah y yace wani ya zalunci wani don wanin na hanyar da ba daidai ba ta kashe wayar 




Shiru Salman yayi yana kallon wayar dukda bawai ya karaya bane ya shiga tunanin mafita...





Kallon Siyama goggo binta tayi tace shiasa banso kina mu'amala da su goggo idan har su ka gano wannan sirrin da mu ke 'boyewa yau shekaru hu'du wlh bansan yadda zanyi da kaina ba don haka ki kira yaya hanne kice musu abinda yasa bakiso suzo gidanki yana cike da dangi baban Amal da sukazo wani biki 



Ajiyar zuciya tayi tace to mama ta jefa layin goggo bugu 'daya goggo ta 'daga Siyama ta gaida goggon, goggo tace haba siyama kema fushin kike yi da 'yer uwarki a ce duk abin nan da ke faruwa da Mimi sam kin kasa zuwa ki gaisheta haba Siyama 



Ajiyar zuciya Siyama tayi tace goggo wlh school ne ya tasani gaba ga Amal na kiwya ko ina da ni da mai aikina mu ke tafiya shiasa kuma jiya Dada tace zakuzo da Mimi kuyi kwana biyu ko.? 



Goggo tace eh mun  yanke hukuncin ne ganin su fauza duk suna makaranta ko hutu suka zo basu da'dewa gidan daga mu sai iyayenku sai ita shine mu kace tunda babban gida gareki bari muzo da ita ta 'dan huta ta samu nutsuwa 



Ajiyar zuciya Siyama tayi ta kalli Mimi mamanta kafin ta fara magana





Wlh goggo yanzu haka gidan nan a cike yake da bakin baban Amal 'yen maiduguri biki biyu garesu shine duk rabin baqin gidana suke ko falo cike yake 




Shiru goggo tayi Siyama taci gaba don Allah goggo kuyi hakuri yaso IA ni zanzo cikin satin nan muyi wk end toh shikenan goggo tace su kayi sallama





Bayan ta kashe wayar ta kalli goggo jummai tace yaya na rasa dalilin dayasa na lura sam daga binta har Siyama basu so a na zuwa gidan siyama ga mijinta kuma mai rufin asiri sosai 



Mami da ke shigowa tace ba ku ba har mu haka siyama ke yiwa yaran nan in suka zo hutu suka kirata zasuje sai tace tanada baqi ko tayi tafiya




Goggo hanne tace wannan gida nata da mutum 100 ma zasu iya zama wasu irin naqi ne zasu hanaka tar'bar dabginka 




Mami tace sai kiga ta tura musu ku'di tace suyi zamansu bayanan kinsan yara su kuma da ta tura musu ku'di sai su bar maganar 



Shiru su goggo su kayi mami tace kin san mijinta ance waje shima yayi karatu qila baya domin son mutane shiasa 





Mummy ta tafi duba su huda a gida Najwa taje gun kaita ita yanzu busy hidimar kotu babu kowa 




A hankali ta ke fitowa gidan har ta kai gate dedans ke a na sallah asar duk suna masallaci ta tari Aca'ba ta hau tana hawa Salman na qarasowa ya ganta da sauri shima ya hau ya bi bayan ta...








Mummy da su Huda da masu renonsu ta taho asibiti sabida khausar na gidanta tare da su twins 'dinta 




Najwa da yanzu suka gama da lauya ta nufi asibiti ta duba Hayat kafin ta wuce gida mugun bacci ta keji yau mummy zata bari haka ta ke ta ayyanawa a ranta har ta shigo asibitin



A daidai zata shiga word 'din ya kira sunanta da arfi a mugun firgice ta juya take idanunta su ka fara sucres kawo ruwa a ka tsaya a na kallonsu da son gane mai ke faruwa ya fara magana





Wlh Mimi in kika kuskur... Da sauri ta qarasa gabansa ta riqe qafarsa tana sakin kukan da ta kwana biyu bata iya yinsa



Kallon2 mutane suka shiga yi a na kuma kallonsu




Mummy da najwa ma a harabar suka ha'du suke qarasowa tare suna magana Najwa na cewa gaskiya Yasmin yau zanyi bacci gida yaso gobe kema sai in rama miki kije mummy tayi murmushi tace karki damu kedai kije suka hango qofar word 'din a cike wani irin kallon juna Mummy da Najwa su  kayi a tsorace kardai ya qarasa da hanzari su ka shiga jarabarsu ratsa mutane suna wucewa har su ka hango ashe Salman da Mimi a ke kallo suma su ka tsaya 




Ya furta mimi wato kin zama jahila kin zama mara tsoron Allah duk sabida soyayyar wannan halakak... Ta furta don girman Allah yaya ka taimakeni duk hukuncin da zaku 'dauka kaina ku bari na gama jinyarsa wlh babu abinda zan iyayi idan yana cikin halin da yake ciki yaya kai 'dan uwana ne jinina kafi kowa sona da sanin darajata kamin alfarma ka barni nayi jinyarsa ko ba domin ina sonsa ba sai domin hannunsa ne a kaina na kula da shi a matsayinsa na mijina kuma na tabbata bazakaso in mutu Allah ya kamani da rashin bashi hakkinsa ba alhalin shi yana bani dukkan hakkokina ta qara sakin kuka tana riqe afarsa 




Najwa macece kamar namiji a domin hatta 'yen uwanta yawanci ita ke shige musu matsalarsu ko qwalla da wuya ka ganta tayi amma a yau ganin yadda mimi ke durqushe qafar yayanta tana magiyar ya barta tayi jinyar mijinta da dama nauyinta ne tayi jinyarsa ta tsinci kanta da hawaye tare da fa'dawa tunanin wai kawai sabida AQIDARMU yaran nan su ka kasa samun kwanciyar hankali a rayuwarsu dukda itama tana sane Tuni Hayat baya shi'a 




Wani irin tausayi ne taji na Hayat da ke tu kwance rai hannun Allah da yaransa da ke rabe à duniya wasu na Nigeria wasu na America a yayinda babu wanda yaga yasan a yanzu kuma me Allah ya sake hallitawa cikin mimi juyawa tayi ta kalli Mummy ta furta Yasmin IA daga yau na bar AQIDARMU kuma IA zan tabbatar 'yen uwana da yaranmu kaf sun barshi domin Hayat har ya auri farida kinfi kowa sanin bai ta'ba fa'da da kowa ba sai 'yen matayensa amma an wayi gari ya zama kamar zaki yau idan ya mutu ko munada hakkin domin sabida AQIDARMU rayuwarsa ta shiga wannan masifun 




Ajiyar zuciya mummy tayi domin a yau itama tausayin mimi da Hayat ya qara ture mata duk wani tunani a duniya tabbas bazasu iya rayuwa babu junansu ba amma banbancin aqidar Iyayensu ya hanasu morar Furen da Allah da kansa ya kulla tsakaninsu 



Domin kuwa tabbas ubangiji da kansa ne ya kulla aurensu da soyayyarsu a yayinda yanzu AQIDA ya hana su moriyar ni'imar Allah a kansu 





Kuka ta keyi sosai ta 'dora kanta ta qafarsa shi cikar da a kayi a na kallonsu ne ya fara damunsa ganin wasu ma na'dar abin suke suje su watsa a media cikin kakkausar murya ya furta zaki yi jinyarsa bisa shara'di 'daya 




da sauri ta 'dago ba tare da jin shara'din ba ta furta  yaya ko menene na yadda "ajiyar zuciya yayi yace *alqalin baba zai sanar miki shara'din bayan ya warke in zamu koma kotu kin amince.? 



Girgizata kai tayi ta furta wlh na amince sam batada idea a kan shara'din saidai shi ya ma na'di maganar ya janye ta daga afarsa  ya wuce duk a ka bishi da kallo....

💖AQIDARMU💖







PART2





No comments