Breaking News

AQIDARMU Book 2 Page 4

 🅿️4️⃣





Goggo ta furta "haka ne Mimi" kuka ta saki tana sunkwi da kanta baba kuwa yaci gaba *idan kika qara bari na ji maganar wannan yaron a gidan nan wlh zakisha mamaki na sakarya wacce batasan ciwon kanta ba tsaf anbani tarihinsa da yadda ubansa ma yazo ya hutsube uwarsa 'yer babban malami da duniya ke karramawa wato ya gado ubansa su sun iya butsube yaran mutane wlh ko mutuwa za kiyi baza ki koma hannunsa ba.. kuka ta saka da arfi tana 'dora kanta kan cinyar goggo hanne ya saka kai ya fita goggo na shafa bayanta taji tudu ta cinyarta da Mimi ta kwanta da hanzari ta 'dago Mimi tana yaye mata hijabin jikinta ta 'daga rigar jikinta sosai ga ciki ya fara tasowa salati ta saka suma duk kallon Mimi su keyi da kanta ke da qasa tayi shiru kamar ruwa ya cinyeta 




Kallonta goggo tayi kafin ta kalli mami tace ga cikin da mu ka fa'da muku kuka musa mana a hankali goggo tace Mimi kije ki huta kasa motsi tayi Dada ta riqo ta suka bar falon duk suka bi ta da kallo 



Mami ta furta inajin tsoron rabo ya kashe wani idan har masu nacewa suka ci gaba da yiwa Allah shishshigi goggo tace suyi dai mu gani shi da binta da Safwan da Salmanun 



Allah ya kyawta mami tace ta miqe ta nufi 'dakinta.









***************





Satinsa biyar a Ireland aiki ya ke tukuru a yayinda zuciyasa ma ke aikin begenta da kewarta yakan ji kamar zuciyar na dab da fashewa ya yi rama amma a hakan bai ta'ba gwada nemanta ba saidai ya kan kalli video ko pic 'din da yakan yi mata batama sani ba yaransa duk suna Cambridge ana kai su crash duk sunyi kyaw sunyi qiba su biyar ko yaushe Najim ke musu video ya tura masa sabida a Iran ma duk sunyi busy aikin sabbabin reshensu 





Dukda mugun 'baci da ran baba yayi tare da mamakin yadda Hayat ya rika bibiyarsa har yasan zai zubda cikin mimi ya rusa gashinan ciki yanzu ya turo kai haikan kowa yana gani 




Mugun tashi hankalin Taimur yayi tayaya cikin bai fita ba wani irin tsanar Hayat ne ya qara dirar et masa tare da burin zasu zuba domin kuwa dole ne ya mallaki Mimi tunda shi ba 'dan shi'a bane kamarsa 





Kallonsa mama tayi ta furta "plz Taimur ka hakura da maganar yarinyarnan domin har yanzu ba sakinta yayi ba banaso a je a 'dora maka wani sharri wlh danginsa manyan mutane ne sosai kuma kansu na ha'de zasu iya jefa rayuwarm... Daddy ya furta sun da'de basu yi ba mahaifinta baya sonsa sannan ke maimakon ki tausaya wa 'danki kina nuna banbanci wato kinfi gane ta ci gaba da auren halakakke yaron 'yer uwarki a matsayina na abokin babanta yamin bayanin komai kuma wlh a wannan karon har da ni à yakarsa bansan wa ya so kasheshi a baya ba amma tabbas yanzu nima zan taya ubanta kawo qarshen auren kuma na nemawa Taimur 



Ajiyar zuciya tayi tata kasa furta komai Taimur ya furta tnx daddy ya miqe ya fita daddy ya kalleta yace ko da wasa kada naji maganar nan bakin kowa har a 'daura auren tukuna ki sanar a su



Kallonta dada tayi tace kiyi hakuri ki fara zuwa awon nan ko sabida abinda ke cikinki da ke kanki kada kije kisamu wani matsala baki saniba hawaye ta share ta shiga ta shirya doguwar riga da hijabi dada tace muje suka fito su goggo na musu Allah ya kiyaye 





Biye da motar ya ke har su ka iso asibitin ita dada su ka fito suna shiga Giwa shima yana shiga mimi kanta na qasa taji anshinsa cikin rashin yadda da abinda taji ta 'dago a hankali ta ganshi bai ko kalli inda ta ke ba ya gaida dada da itama duk mamaki ya cika ta shikam bayajin gajiyar tafiya idan kudin sun masa yawa na sintiri tsakanin Nigeria da Iran



Ansawa tayi ya furta "muje dr yana jiranmu" bata motsa ba dada tace kuje kamar kwai ya fashe mata a ciki ta nishi har Office 'din dr na ganinsu ya furta "Welcome madam" ya basu guri inda ya furta bari mu fara scanning nan ya kalli hayat ya ce yalla'bai ka gyarata kallonta yayi dr ya fito office 'din ya barsu 




Cikin nutsuwa ya miqe yana miqar da ita ya cire mata hijabinta ta lumshe idanunta wani irin masifar missing 'dinsa tayi ya ajiye hijabin ya 'dan kalleta ya riqo hannunta har kan gadon scanning ya kwantar da ita ya koma ya zauna

 Binsa tayi da kallo tana hawaye baya kallonta saidai hankalinsa na kanta su kaji dr ya shigo nan ya fara mata scanning yana nunawa Hayat twins na yara mata biyu lafiyayyu wani irin farin ciki ne mara misaltuwa ya shiga a hankali ya furta "tanx" dr yace ka gyarata ina zuwa ya sake fita 




Ya da'de a tsaye kafin ya je ya goge mata ciki da wani irin salo tana lumshe idanuwa qura mata yayi kafin ya 'dagota ya sakko da ita kamar zata fa'di ta ya tarota zuwa irjinsa su ka saki ajiyar zuciya a tare ya fara qoqarin 'dagota daga jikinsa ta riqe yatsunsa tana hawaye bai ce qala ba ta fara magana 



Plz 4giv me ina dab da mutuwa in kaci gaba damin irin wannan hukuncin.. ajiyar zuciya yayi baice komai ta zagaye cikinsa da hannayenta tana kwantar da kanta cikinsa sabida ya mata tsawo ajiyar zuciya yayi ya furta " baby kinyi za'binki kuma IA zan rungumi za'binki da sauri ta 'dago tana hawaye ta fara magana



Wlh mine ko Yah Salman yace in yaqi saurarona pls ka taimakeni ka bari muci gaba a yadda mu ke ko yaushe kazo zan sameka duk inda kake zanyi maka duk abinda kake so tana kuka 



Matsawa yayi ya zauna yana kama kansa yayi shiru durkusawa tayi ta dafa gwiwarsa tana kallonsa bai ko motsi ta kira sunansa *Hayat* a hankali ya 'gado idanunsa duk sun ka'da ya furta "Baby na tunkari duk jarabawar da ta tunkarenj domin kasancewarmu tare amma ke kin amince kawo arshenmu ko"? Girgiza kai take ta riqo hannunsa ta furta wlh bazan ta'ba kawo arshenmu ba miqewa yayi ya jawo system 'din gefensa ya kunna ya tura mata gabanta 





Baba ne ya kalli Safwan ya furta "mai yasa baka shawarscenj ba kafin kayi haka.? Shiru Safwan yayi baba yaci gaba na fi ka tsanar yaran nan kamar yadda na tsani 'dan shi'ar ubansu sabida ko komitin  masallacine suka san Farida na auren 'dan shi'a zasu kwace duk wani kambu na girmamawa da suka bani don haka yanzu zan kirawo binta kuje maza ku samo wanda zasu fara rainon yaran kafin na samu mafitar yadda zasu koma hannun ubansu ba tare da wani ya gano komai ba Safwan yace to baba sannan jummai da hanne sun fara tausayin mimi hakan kuma shima matsala ne a garemu to ka tabbatar kaje an kai yaran gidan har in samu mafita su kayi sallama videon ya tsaya 'dagowa tayi tana kallonsa idanunta cike da qwalla ta taso a hankali ta qara zama kusa da shi ta riqo hannunsa ta fara magana "pls mine ka fahimceni ko me baba da safwan zasuyi dol... Ya katseta yana furta *zan barki kibi umarninsu da zarar kin haihu* cikin gigita ta kalleshi tana hawaye miqewa yayi ya furta 



Yara na na bukatar kulawa idan har ni bana bukata tunda kuma ba zamu iya samu ba daga gare ki zan tayasu ceremu daga rayuwarki da zarar kin haihu hakan zai tabbatar musu kin za'besu a kan ni da yarana.. 



saurin matsawa tayi gabansa ya zame jikinsa  fita ya barta gurin



Durkushewa tayi tana sakin kuka....

💖AQIDARMU💖





PART2


No comments