Breaking News

AQIDARMU Book 2 Page 3

 🅿️3️⃣





Mummy da dama zaune ta kwana sallah tana nemawa Hayat rahama gurin ubangiji sai yanzu ta tuna da Mimi ta miqe ta nufi 'dakin da Mimi take cike da muguwar mamaki gabanta na fa'duwa ta tsaya jikin qofar sakamakon motsinsu da take ji busbewa tayi na mamaki jin muryarsa yana furta *Tun bayan da kuka taho ke da mummy*



Na samu hatsari nayi jinya na fito na koma Babban gidanmu wata akwai abubuwa dayawa da na fara zargi daga dangina har danginki don haka na yanke hukuncin ci gaba da qaryar ciwo domin gano abubuwan da ke faruwa inda na ha'da cameras duk gidan bayan wanda mu ke da shi a gidan inda na kan saka a tsayar da na gidan nawa suna aiki da haka ne wata rana ina 'dakina da safe kawunaina suna office 'din kakana 




System ya miqa hannu ya 'dauka a gefen su ya 'dagota ya zaunar da ita ya kunna system 'din ya kalleta ita kuma tana kallon system 'din video ya fara nunawa ya 'dan qara sautin yadda zata ji da kyaw




Abu'Ahlam ne da Abu'noor Abu'Ahlam ya kalli abu'noor yace *Akhu* ni wlh banida damuwa idan ma Hayat ya bar AQIDARMU damuwarsu 'daya ya zame daga zuri'armu wannan babban abin kunya ne a garemu a ce tun farkon kakanninmu na biyar sun kasance da juna tare kamfanoninsu da komai tare cikin kaunar junansu da zumunci dama dole a na ita kuma samu wasu generation da ba lallai bane su bi Aqidar da suka tsinci iyayensu da kakanninsu a kai idan ka duba ko mayan malamanmu zaka samu iyayen su sun kasance wasu 'yen *Sunna* wasu kuma 'yen *tijjaniya* amma kowa ya tafi a kan Aqidarsa dukda hakan basu bari kansu ya rabu a na zumunci sannan a na tare





Ajiyar Zuciya Abu'noor yayi yace jiya maganar da mu kayi kenan da Abu'Nawwal karka manta  Hayat shi ke da 60/% na kamfanoninmu shida

 Da ke fa'din qasar nan wanda sune jigonmu na future idan har mu ka saki ya bar qasarnan muna cikin tashin hankali na har abada domin ko banki ba zasu ta'ba bamu bashin da zamu qara domin farfa'dowa ba, yaci gaba domin in maganar *AQIDARMU* wlh na da'de da gane Hayat baya cikinta kallonsa Abu'Ahlam yayi ya girgizawa Abu'ahlam kai yaci gaba kaima nasan kagane haka

 Shiru kawai kayi domin tun lokacin da Hayat ya cika shekara 13 ka ta'ba  ganinsa cikin wani irin taro na mu na *AQIDARMU*? Shiru abu Ahlam yayi Abu'noor yaci gaba a lokacin nayi bincike sosai na gano ita kanta Yasmin bata gane abinda Hayat ke yi ba saidai daga bincikena na gano shi kansa mutha ya a qarshen rayuwarsa ya canza AQIDARSA ba tare da mun gane ba sabida bai canza mana daga yadda ya ke bawa zumuncinmu matsayi mai daraja ba, abinda na ke so ka gane shine Hayay kansa ba *AQIDARMU* ya keyi ba zumuncinmu ya ke bawa muhimmanci wanda ya ke kore masa ganin AQIDARMU hakan yasa nima abin bai dameni ba saidai idan har wannan surikin nasa zai rinjaye  shi a kan ya shiga  kyamarmu gara mu san duk yadda za muyi domin mantar da shi wannan matar ta sa da itama nayi bincinke na gano Yasmin ta ha'da auren ne domin Hayat ta kar'bi koda rabin  dukiyarsa koma Eng ko Ireland da rayuwa ita da haka tayi plan 'dinta na cireshi daga AQIDARMU batasan ma baya ciki ba ita kanta wanda sai daga baya na kara gane dalilinsa na 'boye mata ya tabbata in ta sani zata bayyanawa wasu wanda hakan zaisa mu sani kuma zumuncinmu zai samu rauni


Ajiyar zuciya Abu'Ahlam yayi yace yace allurar zamu saka noor yaci gaba da yi masa ya manta wannan yarinyar da ya maidata kamar numfashinsa, dagowa Mimi tayi ta kalleshi tana 'dan qwalla ta sake mayar da kai kan system 'din




Idan har Allah ya saka ya manta komai daga rayuwarsa da ita sai mu tasashi gaba mu bashi biro da paper yadda zamu na fa'da masa yana sakinta har ya gama rubuta mata sakinta sai mu turawa ubanta mu riqe 'danmu kafin mu aura of masa matar da mu ka tabbatar ko Tehran ba zash Roma fita ba sai da saninmu kuma no insemination ne mu saka a yi mata na yara uku kaga tafi waccan dole ko sabida yaran zai hakura rayuwa da ita kasanshi da son yara murmushi abu'Ahlam yayi yace "Akhu" wannan shawara tayi sai gobe na yi magana da Najwa muji nata ganin ok yace su ka miqe ya kashe system 'din yana kallonta sai hawaye ta keyi 




Ajiyar zuciya mai nauyi mummy ta sauke 



Riqo hannunta yayi yana kallonta sosai kanta na qasa ta kasa kallonsa ya furta *my queen* still bata 'dago ba a hankali ya saka hannayensa ya tallafo fuskarta duk hawaye ya furta *wlh baby tun ina 13yrs na bar AQIDARMU wato Aqidar kakanni da iyayena* ke kanki nayi sallah na a 'daki a ranar kafin na fito falo na qara yin na su domin inaso in gane mizanin soyayyarki a kaina shin zaki jure sona a hakan ki rika min addu'a shiriya ko zaki gujeni " manzon Allah saw yace idan kaga 'dan uwanka ko wani masoyinka cikin hali na sa'bon Allah ba gudunsa ya kamata kayi ba a farko 'dagowa tayi tana kallonsa yaci gaba ina matukar kaunar kawunaina kuma tabbas bazan ta'ba gudunsu ko kyamarsu ba illa zan kasance ina musu addu'ar shiriya da gane gaskiya domin na sani idan ko 'dayansu ne ya gane gaskiya to tabbas duk zasu je gane wannan dalilin yasa bazan ta'ba barin Iran ba har sai naga nayi nasarar dawo da  dangina hanya madaidaiciya ya riqo hannunta yana kallonta ya ci gaba "baby ina mutuwar sonki ina miki son da bana yiwa kaina ko rabinsa inaso ki tausayamin ki taimakamin muyi wannan jihadin tare kinji.? Hawaye ta keyi sosai ta kasa magana tallafo fuskarta yayi da kyaw yana jiran ansarta a hankali ta furta *baba bazai ta'ba barina na koma Iran* shiru yayi still yana kallon yadda ta ke ta hawaye ajiyar zuciya yayi shima yayi ya shiru tunani fal zuciyarsa a hankali ya gyara jikinsa zai tashi ta riqo hannunsa ya tsaya yana kallonta ta kasa magana shima bai tsaya ce ba 



Kusan 10mnts ya furta "baby zanyi Sallah lokaci na tafiya" a hankali ta zame hannunta tana sharar qwalla ya shige bathroom 'din yayi wanka ya fito 'daure da tawul ya jawo drower ya jefa jallabiya ya fita tana zaune inda take tana kuka 



Yana fitowa mummy na tsaye ya mata murmushi ya wuce ta jima kan ta kutsa kanta cikin 'dakin mimi ta na'de jikinta da zanin gadon sunkwi da kanta tayi ganin mummy tsayuwa mummy tayi ka'dan tana kallon gadon da mamakin yadda har sudai sam basu gajiya da cin junansu ajiyar zuciya tayi ta basar ta qarasa bakin gadon ta zauna shiru kafin ta fara magana 




Farida yaushe kike ganin zaki bar kowa ki bi mijinki.? Shiru mimi ba ansa taci gaba tun ranar da na sanar masa 'daurin aurenku ya furtamin wata kalma da bazan ta'ba mantawa ba *Mummy inaji kamar Allah ya shiryamin wannan auren ba yadda mu mu ka shirya ba* na tanbayeshi maiyasa kace haka.? Yace mummy tun shekaran jiya na ke mafarkin da *Mama* tana sanyamin albarka da yimin fatan alkairi cikin auren hawaye mimi ta keyi mummy taci gaba Hayat ya sadaukar da hatta dukiyarsa domin ki kuma na tabbata har kisan nan da a kaso kasheshi sabida wannan ke ne ya tsallake to shin baki ganin lokaci yayi da kema zaki manta kowa ki bi mijinki.? Kuka mimi ta saka tana sunkwi da kai mummy tace "a gaskiya farida a wannan karon ni kaina idan har baza ku koma Iran tare ba to banga anfanin kuci gaba da rayuwar aure a titi ba sabida Hayat ya wuce haka yanada arzikin 'daukar nauyin ma'aurata 'dari so ya kamata ki yanke hukunci domin ni na shirya ya yi miki gara ko ta millions nawa da uwa ke yiwa 'yerta ki est koma tare da mijinki ki haihu gidanki gabansa da danginsa kiduba yadda mimi nayi tsammanin sune matsalarmu ashe ba su bane tsananin zafi da 'daukaka banbancin aqida irin na babanki kun mayar da yaranku marayu haka kike so kuci gaba.? Kuka ta keyi sosai Mummy ta miqe ta furta kiyi shawara nan zuwa gobe ta fita ta barta tana kuka Sosai




A masallacin bayan ya gama sallah ya fito yana zaune dakalin mummy ya yi shiru ya da'de kafin ya dawo gida direct part 'din mummy ya nufa jin hayaniyar twins a na musu wanka ga motsin baki Sosai yana  ji ya shige 'dakin mummy da sauri tana kan dadduma sai da ta idar da sallah ya gaishe ta shiru tayi tana kallonsa duk tausayi ya ke bata ya 'dauki zuciyarsa ya mallakawa Mimi amma ita tananan har yanzu tana tunanin bazata iya barin danginta sabida aurensa ba a hankali mummy ta taso ta zauna kusa da shi tana riqo hannunsa ta furta "my boy yanzu mainene next plan 'dinka.? Murmushi yayi yace zan wuce yanzu zuwa 'dan marina mu koma Iran sabida inada ayyuka sosai da zanyi sannan tafiya ta sameni a office maganar new industrial companies da office 'dinmu suka bu'de a Swaziland da Turkey so inada aiki sosai a gabana.



Shiru tayi sosai shima kafin ta furta to "Farida"? shiru yayi yace mummy ki barta tayi abinda taga yafi dacewa da ita ko dana zo dama just appointment 'dinta zamuje na san time table 'din antinatal 'dinta ina zuwa kaita " kallonsa mummy tayi da tausayi a ce mijinka yana tasowa har wata qasa don kawai yazo kaika asibiti Shafa kansa tayi tace haka ne my boy ya kamata zuwa yanzu itama tayi wani qoqari a kan rayuwarku domin ko komawa nayi na fa'dawa babanta baka aqidar iyayenka bazai ta'ba yadda ba ajiyar zuciya yayi ya miqe ya furta mummy sai munyi waya ok tace ya mata peck a goshi ya wuce 




Kuka tayi sosai kafin taje tayi wanka tayi sallah tana zaune tana tsammanin dawowarsa suyi magana yayi hakuri suci gaba da rayuwarsu a haka ko yaushe a 'boye2 ita zata jure ko har abada ne domin tasani ko baba yaji  baya shi'a bazai ta'ba barinta rayuwa da shi ba domin ai danginsa shi'an su keyi 





General ya furta Yasmin ta tafi da ita kaduna wai can za tayi takaba "shiru baba yayi saidai kuma yayi ajiyar zuciya hakan yayi masa no babu komai rabuwar dole ta zo bayan takaba dai ai shikenan ya yar da qwallon mangwaro ya huta da quda ya jiyo muryar general IA nima zan shigo kaduna cikin sati mu tattauna wasu maganganu toh baba yace su kayi sallama baba ya kira su mami da su goggo yana fa'da musu yadda su kayi da general inda goggo tace to ai sai mu shirya anjuma muje musu ta'aziya..




Suna fita baba ya jefa layin maman Safwan yace kizo anjuma zasu fita gaba 'daya ya tsinke kiran








Kallon agogo tayi 9:45 cike da fargaba ta miqe tana sharar qwalla ina kuma ya shiga zama tayi tace ta fara fara tunanin kiransa ta 'dauko h/bag 'dinta da ke gefe ta 'dauki wayarta wayar ma duk ta fashe ta mayar ta ajiye tana tunanin ta hango wayarsa shima a hankali ta miqa hannu ta 'dauka qwalla ne ya qara taruwa mata ganin hotonta ne kan screen 'din wayar ta share qwalla ta fara tunanin bari ta kira Fauza ta bata no 'din Salman domin ta haddace no 'din Fauza qoqarin bu'de key 'din tayi ta kasa sai taji zuciyarta na fa'da mata saka sunanta ta saka nauyi ba a hankali ta saka *my queen* ya bu'de ta shigar da no 'din fauza 




Tana shirin shiga lecteur kiran ya shigo ta kalli no da informations na tru/c *My quee* tayi mamaki kafin ta 'daga mimi tace Fauza ni ce pls karki kashe ki saurareni



Fauza tayi ajiyar zuciya tace maiyasa zan kashe mimi? Kece fa kika yakice ni daga rayuwarki "ya hakuri"? Mimi tayi ajiyar zuciya ta furta plz ki turomin no 'din yah Salman yanzu pls "ok" fauza tace mimi ta kashe wayar 




Suna zaune babban falon gidan nasa su kaji motsin bu'de d/bell duk suka tsurawa kofar idanu a hankali ya shiga wani irin zabura Mustapha yayi yaja baya su kuwa iyayen ikon Allah duk basuyi mamaki ba ya qarasa shiga yana zama kusa da Abu'Nawwal ya ga yadda duk suka bushe kallonsa murmushi yayi ya furta *is me Hayat Muthallib* suka saki ajiyar zuciya najwa ta furta we kno alls cewa ba kai cikin gawarwakin da mu ka gani suma dangin Zainab is just bcs basu sanka bane shiasa suka yadda ajiyar zuciya yayi yace "gara muyi shiri ni zan wuce ko ku kunanan tukuna miqewa abu'Ahlam yayi yace ah ah kowa ya shirya duk suka shige. Shima 'dakinsa ya shiga ya zauna shiru bayason  abinda ya ke shirin yi mata amma bashida mafita sai hakan  a hankali ya miqe ya shiga wata danqareriyar *range rover* ya saya mata ne a kan domin duk sadda su kazo Kaduna tana anfani da shi yana tuqi har ya isa kinkinau yana kofar gidan su goggo ma na fitowa ya Fito cikin nutsuwa zaro idanu duk su kayi suna tsayiwa baiyi mamaki ba ya gaishe su da kyar mami ce ta iya ansawa goggo jummai da goggo hanne na goye da yara sai dada na riqe da 'daya 



Cikin girmamawa ne ya kalli dada ya furta nazo kar'barsu ne kallon juna su kayi zai qara magana su ka ji baba na fitowa shima baban babu wani alamar mamaki ya furta "zasu haka bisa shara'din itama mimi zata dawo a yau 'din nan ajiyar zuciya yayi yace "Insha Allah" 



A hankali su ka fara miqa masa yaransa 'daya bayan 'daya yana saka su cikin kujerar jarirai da dama ya akwai a motar ya gama sakasu duk suna ta baccinsu ya musu sallama su goggo duk tausayi ya hanasu iya magana  har ya bar gurin suka juya gidan jiki duk a mace yana shigowa gidan suna fitowa suma duk suka qarasa gaban motar ya fara fito da yaran Abu'Ahlam ya furta "Shukhran ya Allah" haka suka shige da yaran 'daya hannun abu'noor sai 'daya hannun najwa




Bayan shigowar no 'din take ta jefa kiran 



Salman da fitowasa kenan lecture yamma tayi a malay ya ansa tayi sallama "Sosai yayi kewarta yana son kiranta saidai sosai shima ya ke fushi da ita kan soyayyar 'dan shi'a katse masa tunani tayi ta fara magana



Yaya nasan kasan komai amma inaso ka sani wlh ba 'dan shi'a ban... Ya daka mata tsawa "kenan abinda kika kirani ki fa'damin kenan? Wlh tallahi ko mutuwa za kiyi bazamu ta'ba barinki rayuwa da shi sai dai in ki za'ba ko mu ko shi ya tsinke wayar ta kalli wayar ta qara jefa call 'din yayita ringing yaqi 'dagawa sannan a qarshe ma ya kashe kuka ta saki da arfi tana kama kanta 




Kallon daddy general mama tayi ta furta "na rasa tayaya tun farko baban ya barta ta aure shi bayan sunsan Aqidarsa da ta iyayensa shiru.. daddy yace baimin bayani ba a lokacin kamar yadda na fa'da miki cemin yayi kawai ya saketa ne ya kuma sadu da itA ta samu cikin shiasa ya ke so a cire ni kaina ya 'boyemin dayawan abubuwa sannan ni kaina na fara bincike a kan yadda a ka so kasheshi a cikin garin nan..




**************




Daf magrib ne mummy ta shigo ganinta a kwance ta qarasa tana furta "haba farida baki ci abinci ba.? Shiru ta saki hawaye, mummy tace ki tashi ki kintsa babanki ya turo a 'dauke ki kallon mummy tayi da mamaki

 Mummy ta riqota ta tashi jin jikinta da zafi mummy tace Kinshasa magungunanki.? Girgiza kai tayi mummy tace ok duk na ha'da cikin kayanki har an kai miki mota shiru tayi tana hawaye mummy ta rikota har mota salisu ya bu'de mata ta shiga mummy ta kalleta tace ki kula da kanki kinji.? Hawaye ta share mummy ta kullo mata qofar ya tayar su ka bar gidan 




Kuka ta saki a motar Sosai har suka iso kofar gida su goggo na jiranta ta fito duk suka rungumeta tanata kuka suka shiga gida baba bayanan an jima kafin ta kalli Dada tace "pls Dada a kawo min su kallonta duk su kayi 



Goggo jummai tace ina ubansu ya zo ya tafi ya da su ance sun koma can qasarsu share fuskarta tayi tana kallon su duka suka ji muryar baba




Ya yankewa kansa hukunci mai kyaw sanin auren na ku ba mai yuwuwa bane har abada kuwa ko bana raye Salman ma bazai bari hakan ta faru ba don haka shi ya hakura da ke shiasa yazo ya kwashe yaransa ya saura naki ki mantashi



Hawaye ne suka shiga silalowa tana kallon su goggo cikin mugun tashin hankali ta furta "goggo ya hakura da ni..?

💖AQIDARMU💖




PART2


No comments