Breaking News

AQIDARMU Book 2 Page 19

 🅿️1️⃣9️⃣








Kwanansu biyu da  wuniba haka  in yanason abu ya kira nurse mimi tayi ta kuka a 'boye Cikin dare duk fargabarta sakinta zai karasa mata har yanzu bai sakko daga abinda ya faru a kotu ba 




A rana ta uku ta tashi da safe babu shi tayi neman babu shi ta tanbayi Dr yace ai ya sallameshi kuka ta saki ta rasa ina zata nufa ita yanzu 



Taso kiran mummy ta fasa ta yanke hukuncin komawa kinkinau dukda zuwa yanzu batasan halin da suke ciki ba gashi jibi ne ake saka ran komawa kotu 



Ha'da kayanta tayi da 'yen tarkace ta nufi kinkinau 



Saidai ga mamakinta DA baba ta fara karo a kofar gida tsayiwa tayi kasa shiga ta fara sabon hawaye tabbas shima korarta zaiyi 



Bata Ankara ba taga su mami da goggo na rikota suka shiga gidan da kyar ta bisu tana waiwayen baba kada yazo ya korata







Haka suka shiga kowa nanan ga mamakinta harda goggo binta da Salman 



Wani irin hawaye ta saki tana sunkwi kai  tana jin tsoron sanar da su Hayat ya rabu da ita tajiyo muryar mami da goggo sun fara magana




Mimi Allah yayi miki albarka ke da mijinki bayan duk abubuwan da suka faru jiya da kansa ya kira kotu ya sanar da ya yafewa su malam abinda duk suka masa yace dalilin ma kenan a tun farko bai bayyanawa kowa abin ba danginsa ne su kayi binciken suka shigar kotu ya biya tarar da kotu ta tanbayi babanku 5M ya kuma saka a ka sakesu baki 'daya harda safwan da 'dan uwansa soja yanzu haka ya sayawa babanku babban filin da namadi sambo ya saka kasuwa nan titin kinkinau ya saka a yiwa babanku babban masallacinsa na Sunna domin qara ya'da aqidarsa bisa ga tsarin musulunci 



Goggo ta Share hawaye tace mimi Allah ya baki miji nagari mai dukkan halaye nagari ki riqeshi da kyaw domin Salman kawo mana video munyi kallo can tvn babanku taronsu kusan asa Awa hu'du muna kallo 



hawaye mimi keyi tana qara jin sonsa da masifar kaunarsa ya mamaye mata ko ina na jininta da tsoka 




Haka suke ta mata labari har dare ta wuce 'dakin dada 




sunyi 'yer hira ka'dan da dada dukda bata nuna mata komai na tsakaninta da Hayat ba dada ta bata magani tace kisha wannan zaki qara samun hutu





Ta ansa tasha tas dada ta bata gumba. Taci 


Dada ta bata robar babba tace kullum kici kisha wancan har su kare



Toh kawai tace ta nemi guri zuciyarta zafi ta keyi mata 



Kwanciya tayi lamo tana tunanin sa da fargabar matsayin aurensu hawaye ta Share ta kalli gefenta wayar dada na gurin ta 'dauka ta shigar da no 'dinsa na Nigeria domin ita tsabar tashin hankali tama rasa ina ta zubda wayoyi daga nata har nasa da ya bar mata sabon number da ya saya kafin matsalolin ta shigar 



ana gaban system 'dinsa yana aiki kiran ya shigo 



Kallon wayar yayi tsaf ya gane number dada ce ya qi 'dagawa har ya tsinke 



Ta daure ta kara jefawa yana kallo yana murmushi mugun bukatarta ya keji amma dole ya qarasa gyarata 



Sai da wayar ta kusa tsinmewa ya 'daga baiyi magana itama haka ganin haka ya tsinke 



Kallon wayar tayi ta saki kuka...

💖AQIDARMU💖











PART2



No comments