Breaking News

AQIDARMU Book 2 Page 18

 


🅿️1️⃣8️⃣






Likitoci ne har biyu su ka shigo 



Tsayuwa su kayi cike da mamakin yadda sukaga mimi kan hayat daga farfa'dowarsa 



Itama kunya ta zamo har kamar zata fa'di qasa ta gyara jikinta tana qifta idanu kamar wace tayi sata 



Qarasawa su kayi kansa suna dubashi tuni ya qarasa bu'de idanunsa saidai ba magana su ka kalli injinsa is 100%100



Suka juya suna tsokanar mimi wai hala magic love ta masa ya farka tashi guda haka 



Sunkwi da kai tayi suka qarasa aikinsu suka cire masa injunan suka ce ta bashi ko da tea ne tace toh suka wuce  




Shiru ta kasa motsawa shi dama shi ba motsawan zaiyi ba domin dole sai ya qara kwari zai fara motsi da kyaw




Ganin mintuna na tafiya ta ha'da masa tea ta qarasa da kyar tana kallonsa kafin ta zauna kusa da kansa tana qoqarin 'dagoshi ta saka masa filo ya matsa da kansa alamar baya so 




Ruwa idanunta su ka fara tarawa ta furta "pls kasha" 



Ajiyar zuciya yayi baiyi magana ba ya juya fuskarsa yana rufe idanunsa zaiyi bacci ya barta galala da tea a hannu tana hawaye 




Takai 17mnts a gurin kafin a jiki a mace ta miqe ta koma kujera tana hawaye ko da kuskure bai juyo fuskarsa ba har cikin dare  da ya tabbatar tayi bacci ya gyara ya juyo yana kallonta tana baccin 



Lumshe idanunsa yayi ganin yadda ta rame sai cikinta ya hango ya 'dan taso ya qurawa mararta idanu kafin ya lumshe idanunsa ya juya ya koma bacci shima





da asuba da ta tashi yana jinta a kansa tana kallonsa saidai bata ta'bashi ba mintuna tayi kafin ta wuce toilet 




'dan bu'de idanunsa yayi ya bi toilet 'din da kallo wato ma har ta karaya ta dawo da girman kanta jiya kawai amma ta fara nuna kamewa 



Numfashi yaja yana furta "sorry baby zanyi maganinki wannan karon sai na tabbatar baki iya 'boye darajata a zuciyarki ta kowa a duniya"  




Yaji motsinta da sauri ya maida idanunsa ya rufe 



Shiri tayi Cikin gown dark purple tayi kyaw har ta gaji ta zauna shiru kenan Dr ya shigo ta gaisheshi ya tanbayi mai jiki tace da sauki 



Yace yaci wani abu.? 



Kallonsa tayi yana yadda yake ta ce ah ah 



Dr yace haba tayaya ya kwana baici komai ba bayan nace miki ko tea a bashi yana bukatar abinci sosai domin kuzarinsa ki tabbatar yaci wani abu yanzu yasha drugs 'dinsa 



Toh kawai ta ce ya bata drugs ya wuce 




Ta da'de zaunen kan ta tashi taje ta ha'da masa tea mai kauri ta nufi gadon shiru tayi ta kasa tashinsa girman kan tsaf ya dawo 



Yana jin 'duminta da yayi missing yanajin anshinta yanajin kewar gaba 'daya jikinta amma ya share ganin lokacin na tafiya ta fara shafa hannunsa a hankali yi yayi kamar mai bacci a hankali ya juyo babu walwala baiyi magana ba itama tayi shiru tana kallonsa ganin haka ya kalli hannunta da tea ya kau da kansa 




Maimakon tayi magana ta fara qwalla tayi shiru taji yana qoqarin tashi tana gun ta ganshi tsaye duk da jiri da ke 'dan 'dibarsa ya taka har toilet yayi wanka yayi brush da brush 'dinta ya 'dauro alwala ya fito 'daure da tawul inta a kugunsa 



'dagowa tayi tana kallonsa cikinsa danshinsa jikinsa fatarsa wani irin yawu ta ha'diya kamar mayya idanunta tsaf jaraba kana kallo yi yayi kamar baisan tana gurin ba ya qarasa 'yer  akwatinsa da ya gani ya tabbatar mummy ce ta kawo asibiti ya bu'de ya fidda boxer da jallabiya 



Miqewa tayi zata ajiye tea ya zame tawul 'din yana ajiyewa 



Wani irin numfashi taja ta saki cup 'din hannunta 



Sunkuyawa yayi ya saka boxer yayi murmushi ya 'dago ya saka jallabiya ya shimfi'da dadduma ya tayar a sallah 




Sai yanzu ta dawo hayyacinta ta kalli cup a qasa ta qarasa ta zauna kujera tana sunkwi da kanta zuciyarta kamar ta fashe 




Bayan ya idar ya kalli gurin da cup 'din ya ke da tea da ya zube ya miqe ya zauna zai ha'da tea 



Ta miqe taje ha'da masa ya furta it's ok tnx yana ha'dawa 



Tsayuwa tayi idanunta su ka cika tana kallonsa har ya ha'da ya zauna yasha ya gama yasha drugs ya koma ya kwanta yana juya mata bayansa 



Hawaye ta keyi sosai amma ta kasa zuwa ta bashi hakuri..

💖AQIDARMU💖





PART2






No comments