Breaking News

AQIDARMU Book 2 Page 16

 1️⃣6️⃣







Hawaye ta saki tana furta 



Ah ah



Yayi murnushi yace in kotu zata fahimta 



Tun ranar da ya fara saduwa da ke da son ranki ya sadu da ke.?




Kuka ta saki sosai tana girgiza kai 




Murnushi yayi ya juya ya kalli alqalin yace nan zan tsayar da tanbayoyina na yanzu sai kuma zuwa anjuma





Lauyan su baba ya tashi ya qarasa tanata kuka ya kalleta kafin ya furta 




Farida no zaki bawa kotu labarin yadda kuka ha'du da Hayat muthallib.?



'dagowa tayi fuskarta jiqe sharkaf da hawaye tana kallonsa ta ha'diyi yawu 



Sake maimaita tanbayarsa yayi 



A hankali ta da'de kafin ta furta "ha'damu a kayi "



Yace kamar yaya ha'dawa iyayenku.?




Kallon baba tayi kafin ta furta "yayana da goggona"



Yace shin lokacin iyayenki basu raye.?




Shiru tayi ya maimaita 



Tace mahaifina ya rasu amma mamata tana raye 



Yace to babu wani dangin mahaifinki da ya ke da alhakin aurar da ke a lokacin.? 




Shiru tayi ya qara maimaita tanbayarsa ta furta 



Akwai..



Yace to mai yasa goggonki da yayanki su ka miki aure da mutumin da basu sani ba alhalin wanda ke da alhakin aurar da ke na raye su kayi babu saninsa.?




Sunkwi da kai tayi tai shiru 




Lauyan ya juya yana kallon alqalin ya fara magana






Mai girma mai shari'a kamar bai yadda nayi bayani a baya Hayat muthallib da qanwar mahaifiyarsa sun yaudari Farida da Yayanta da goggonta ne da kud'...



Ta miqe da tana sakin kuka ta furta 




Wlh ban ta'ba kwa'dayin ku'dinsa ba tun a farko na amince da auren ne domin taimako 



Lauyan ya juya yana kallonta ya furta wani irin taimako.?




Lauyan Najwa ya miqe ya furta objections my lord 




Alqali ya kalli lauyan baba yace ka gyara takunka 




Yace afuwa my lord ya qara maimaitawa Mimi tanbayar 





Shiru tayi ya juya yana kallon alqalin ya cigaba 



Mai girma mai shari'a 



Hayat ya auri Farida ne domin wasu manufofi nasa da bai kamata a yi aure domin su ba 



Mai girma mai shari'a baban Farida babban malamin sunna ne Hayat kuma gaba 'daya da shi da danginsa 'yen shi 'a ne 




Da haka baban farida ke rokon kotu mai alfarma ta duba kukansa ta kar'bawa Farida takardar sakinta gurin Hayat muthallib ya zauna




Miqewa lauyan baba yayi ya kalli alqalin ya fara magana 




Mai girma mai shari'a Hayat muthallib ya auri farida ne a hannun yayanta wanda balagagge ne yakai magidanci wanda bacin qila bayada arfin ajiye iyalai da yanzu yanada iyalai domin shekarunsa 35 a yanzu haka 




Sannan shi da kansa ya bada auren Qanwarsa a matsayin ubansa wanda kowa yasan hakan daidaine ko a musulunci 




Sannan ba su qulla auren kan yarjeneniya ta ku'di ba sai kan taimakon Hayat wanda hayat ne da mamansa suka ga dacewar yiwa Salman Tukwici na basu auren qanwarsa inda suka cika masa burinsa na sonyi karatu Malaysia suka biya masa karatunsa yanzu haka yanacan yana yi 




Jakarsa ya bu'de ya fito da takardu ya miqawa alkali yace wannan shine takardar yarjejeniyar auren hayat da Farida wanda babu komai ciki illa alkawarin da zarar rayuwarsa tayi daidai in tanaso zai sawwake mata saidai hakan ya sanja domin ita da kanta Farida ta kamu da son mijinta ta kuma amince da cigaba da kasancewa matarsa 




Ga kuma shaida ya kunna wayarsa yana juyawa alqalin video Hayat ne da Mimi a airport ta rakashi suna rungume da juna tana kissing 'dinsa inda lauyan yaci gaba 



Wannan videon lokacin da Hayat ya gane an kai matarsa Calabar  ne sabida ya saka masu kula masa da duk wani motsin matarsa inda wannan videon ma 



Taimur Sa'id Hashim ne yasa a yiwa Hayat da matarsa domin wani shiri da ya keyi a lokacin a kan Hayat 




Wani irin yawu Taimur ya ha'diya yana kallon babansa 




Shi kuwa baban tsabar tashin hankali ko qiftawa baya yi wajen kallon lauyan 




Lauyan yaci gaba




Mai girma mai shari'a Hayat miji ne na kwarai ga matarsa domin babu abinda bai jure ba domin kasancewa da matarsa daga cikin abinda ya jure kuwa 




Bayan matarsa ta haifi yaranta na farko tagwaye a ka sacesu a garin shanono a ka sacesu alhalin daga ita har ubansu basu ko ta'ba ganin yaran ba




Inda hayat yana jinya lokacin amma da labarin ya sameshi hankalinsa ya tashi ya taso da kansa a karon farko a rayuwarsa ya shigo Nageria ya 'dauki masu bincike na sirri ya biyasu zunzurutun ku'di har 3M kuma .ca hamstrung biyan ka duba mai girma ya miqawa alqali yaci gaba 



Ya biyasu domin su gano masa yaransa inda suka fara aiki babu kama hannun yaro 




Yawu goggo binta da Baba su ka ha'diya lauyan yaci gaba 




Inda suka gano masa yaransa can unguwar shanu layin masu itace gidan wani mutiny mai gadin gidan wani MD na UBA bank 



Koda suka bincika ba wani bane ya sace yaran face (Safwan Mu'az) tsohon mijin farida kuma 'dan uwanta 




Cikin tashin hankalinsu Mimi ta juya tana kallonta Safwan ya 'dauke kansa tana hawaye 



Lauyan yaci gaba sannan mahaifiyarsa ma tasan da haka da kuma saka hannunta ga shaida ya miqawa alqalin hoton goggo binta a qofar gidan suna magana da mai gadin wato wanda yaran suka zauna hannunsa 



Inda a qarshe Safwan da mamansa suka sanarwa da Malam Sa'ad amma suka ha'da kansu suka ci gaba da ganin Farida cikin tashin hankalin 'batan jariranta 




Ko da ma'aikatan da Hayat ya 'dauka suka sake sato masa yaransa faga qasqantaccen gurin da su Safwan suka kai masa yara gurin da ko mai shara da wanke2 gidan Hayat yafi arfin zama agurin bai musu komai ba 



Hasali ma jan kunnen ma'aikatan yayi kan bayaso su kai aikin office 'dinsu domin bayaso a hukunta Safwan sabida kasacewar Safwan 'dan uwan Farida 




Hawaye ta saki sosai tana jin sonsa na nunkuwa a zuciyarta 




Wani irin gumi baba ya fara yana qifta idanu 




Gogoo da su mami kuwa tsanar Safwan su kaji ya 'darsu musu a zuciya da shi da mamansa inda ita kuwa dada ta qudurce tabbas wannan karon zata bar baba da aqidarsa ta bar gidansa da aurensa 




Lauyan yaci gaba bayan haka 




Farida ta samu matsalar qoqolwa samakon soyayyar mijinta da 'batan yaranta inda Dr yace a kaita sakatri ta samu lafiya saidai a b'oye mahaifiyar Safwan ta bi tasa a rika yiwa farida allurar qara tinzirata daga hauka domin su samu suce babu wanda zai iya aurenta a haka sai Safwan 




Ita batasan hayat ya saka ana bibiyar matasa ko ina ba labarin ya iskeshi da kansa ya ke shigowa Nigeria ko ita kanta matarsa bata sani ba dukda tana ganinsa amma ta 'dauka mafarki ta keyi 



Domin jeta biya kaf masu kula da ita a asibitin inda in yazo ma Cikin 'dakinta mahaukata  ya ke kwana tare da ita sai in gari ya waye ya koma masaukinsa 



Wani Irin hawaye mimi keyi da baya tsayiwa 




Salati su goggo ke yi suna jinjinawa Irin Soyayyar da Hayat ke yiwa Mimi tabbas na ta wasa ne a kan nasa




Lauyan yaci gaba da haka har ta samu ciki wanda da kansa ya sayi abin gwajin ya mata gwajin kafin ya koma Iran 




daga lokacin yaci gaba da zuwa ganinta duk inda take kuma in yaji saduwa da ita ya sadu da ita a yayinda ita duk take tsammanin mafarki ne dukda ha'din kan da take bashi yayin saduwarsu




Ko da ta haihu Hayat da kansa ya je ya kar'bi yaransa ya kaisu Cambridge inda ya ha'dasu da sauran 'yen uwansu da ke can wato yaransa na fari gudun faruwar wani abu mara da'di domin sam bayason cin mutuncin kowa Cikin zuri'at matarsa 



Sosai ta ke hawaye.. 



Su goggo kansu hawaye su keyi na tausayin Hayat 




 Inda Hayat yaci gaba da bin matarsa duk inda take inda har Allah ya sake bata wani cikin wanda wannan ma shi da kansa ya 'diba jininta bata saniba ya kai a ka gano masa Cikin cike da farin ciki ya qara 'daukar wasu ma'aikatan sirri domin kulawa da ita inda daga cikinsu harda wanda abokin babanta ya turo gadinta domin kada Hayat ya rika kusantarta ba tare da sunsan Hayat ya gama sayan securities 'dinba a ka turo musu 






Wani irin iska General ya furzar yana tuna ranar da ya kira office 'din kaduna yace a tura securities gidan baba a ka ce masa ai an gama sayar da su yace a sama masa ko goma 



Wani irin numfashi ya fitar wato na dama Hayat a ka saidawa su 




Inda su kewa Hayat aiki suna kallon komai da ke faruwa sannan hayat na zuwa har kwana da farida cikin 'dakinta ba tare da wani ya sani ba cikin jama'ar gidan 




Salati goggo jummai tayi tace hanne mu kayita cewa tana mafarki 



Goggo hanne tace kedai Yaya bari ai dole Mimi ta haukace kan sonsa wannan soyayya da ya nuna mata ai ni ko Cikin fim ban ta'ba gani ba





Layyan yaci gaba a na haka babanta ya kai qararsa inda gomnatin qasarsa ta sanarwa iyayensa ganin daraja da 'daukakar da suke dashi a kasarsu yasa gomnatin ma tace in sunga baban Farida cin mutuncinsu ya keson yi su basu basu damar hukuntashi 



Saidai Hayat ya hana gomnatinsa inda ya shaida musu matarsa tafi komai daraja a rayuwarsa kuma zai iya jure qasqanci daga kowa domin ta ballantana daga iyayenta 




Qwalla goggo jummai ta share tace Allah sarki 'dan albarka 




Lauyan yaci gaba inda dalilin wannan qarar Malam Sa'ad ya gano Farida na da shigar ciki ya sanarwa abokinsa ya kaita zuwa Calabar su zubar da Cikin 



 

Salati su goggo suka saka dada ta furta "Ya Allah"




A Calabar Hayat yana asibitin malam Sa'ad da abokinsa General Sa'id da yaronsa Taimur da matarsa Zulaiha suka jagoranci Zubar da cikin 




Hawaye mummy ta share tana ayyana daga nan zata je gidan Zulai domin taji suna ma abujar 




Lauyan yaci gaba 




Inda suka gama a ka shiga da Farida da aka riga a ka mata allurar Anastasia a gabansu domin su tabbatar da za'ayi aikin da suka biya ayi musu 




Inda ya canzata zuwa kayan asibitin Dr ya bashi reza ya yanka hannunsa ya rika zubawa Farida jinin a jikinta domin su malam sa'ad su yadda an zubda Cikin 



Kuka mimi ta saki sosai tana riqe irjinta wani irin tausayinta ne ya qara cika mata zuciya tana danasani



Lauyan yaci gaba inda daga nan Dr ya sanar musu ya gama zubda mata Cikin suka masa godiya ya ce ga kuma shaidar komai Cikin video ya miqawa alkali 




Kowa jikinsa ya mutu da tausayin Hayat inda Baba da Taimur da General Safwan tsanarsa ta qaru musu 




Lauyan yaci gaba daga nan Malam Sa'ad da General Sa'id suka yi alkawarin ha'da Farida Aure da Taimur bayan Taimur yayiwa malam Sa'ad alkawarin ganin bayan Hayat 




Inda Taimur 'dan General Sa'id cousin ga Hayat ya fara bibiyar rayuwar hayat



Da farko ya fara zuba masa guba a wani cafe da suka je da matarsa saidai Allah ya nufa baisha ba domin ya sani shima a  nasa ma'aikatan na bashi labarin komai kuma kullum duniya suke bashi report ko baya Nigeria kuwa 




Da haka itama Binta mahaifiyar Safwan ta kai shi gidan boka inda tace tanaso a kashe masa al'aurarsa da ya ke saduwa da matarsa har yana mata ciki



Gumi goggo binta ta fara




Su goggo su ka doka salati suna kallonta



Yaci gaba shima wannan ga shaida cikin vedeo na maganarta da bokan 




Inda shima Taimur ganin wancan shirin nasa ya lalace ya koma wata inda ya shirya da wasu escortes na gidan gomnatin sojoji ta Jihar Calabar inda baisan duk mutane 'daya bane da wanda sukewa Hayat aiki 



.wani irin iska Taimur ya fitar idanunsa sunyi ja 




Lauyan yaci gaba a nan ne ya shirya sakawa Hayat bom inda ya sayi mota sak wacce hayat ya sayawa matarsa ya tura a 'dauko Hayat bayan da yasan arfe nawa Hayat 'din zai sauka 



Inda Hayat da escortes  'din da Taimur ke tsamamanin shi su ke yiwa aiki baisan Hayat su keyiwa ba suka kawo masa wani mutum wanda a ka yanke masa hukuncin kisa sabida fya'de da yayiwa jaririya har ya bata qanjamau saura kwanaki a rataye shi 




Don haka escorts 'din suka ce shi ya dace yayi aikin suka bashi inda ya sanya kaya tsaf wanda Hayat ya saka ya shiga motar wacce mai tukinta yana hango mutumin ya fita a durkushe ta 'dayan kofar ya rufo 

Mutumin ya shiga bom ya tashi 




Wani irin hawaye Mimi keyi tana kallon baba da taimur  da Safwan da goggo 




Lauyan yaci gaba mai girma mai shari'a binta kuma dalilai da dama wanda wasunsu ma basu shafi Hayat ba farida suka shafa yasa ta tsani Hayat daga ciki zan lissafo wasu yanzu da kuma shaida a hoto da video 



Juyawa duk a kayi a na kallonta inda yayyunta ke mata kallon qasqanci da Allah wadai 





Yawu goggo binta ta ha'diya tana gumi..

💖AQIDARMU💖







PART2




No comments