Breaking News

AQIDARMU Book 2 Page 15

 🅿️1️⃣5️⃣








Hawaye ta saki kafin ta furta *HAYAT MUTHALLIB* ajiyar zuciya Lauyan yayi yace yaranki nawa.?




ta furta (7)




Yace shin zaki iya bani 'dan tarihin rayuwar aurenki da mijinki.?




Shiru tayi kafin ta 'dago da nuna alamar bata fahimci tanbayar ba 




Hakan ya fahimta ya furta inaso ki bawa kotu 'dan tarihim mu'amalarki  da mijinki ma'ana wani irin miji ne shi ya ya ke mu'mala da ke 




Shiru kusan mintuna kafin ta 'dago su baba qaf idanunsu na kanta




 Da kyar ta fara magana 




Mutum ne mai tausayi, Imani, hakuri, juriya, sannan mai sanin hakkokin da su ka rataya a kansa 




Iska mai zafi Taimur ya furzar 




Lauyan yace shin kuna rayuwa tare ne ma'ana gida 'daya kamar ko wasu ma'aurata.? 




Girgiza kai tayi tace ah ah 





Yace amma a hakan ya kasance miji na gari a gareki.? 



Eh ta furta tana qwalla 




Ya juyo yana kallonta ya furta "shin daga aurenku zuwa yau ya ta'ba tirsasaki yin wani abu na cusgunawa ga danginki.?




Hawaye ta saki tana kallon su gaba 'daya kafin ta furta 'ah ah




Yace shin ya ta'ba hanaki mu'amalar zumunci da danginki.? 



Tace ah ah



Yace shin kin ta'ba zagi ko qasqantar da wani cikin danginki.?



Lula ta saki ka'dan tace ah ah



Shiru yayi ganin tana kuka ya juya ya kalli mutanen gurin tas kafin ya juyo kanta yayi shiru yanason qara mata wasu tanbayoyin saidai ganin halin da take ciki ya tsagaita yana jiran ta nutsu




Kusan 4mnts ta yi shiru kafin ya fara magana 




Malama Farida daga aurenku zuwa yau mijijnki ya ta'ba marinki.?




Lauyan su baba ya miqe ya furta "Objections mai girma mai shari'a wannan tanbayoyin sun shiga wani sashe da bai kamata lauyan mai qara ya shiga ba




Alqali yace "dole ta ansasu daidai su ke da abinda a ke tuhumar mijinta a kai 



Dole lauyan ya zauna yana huci yana hararar lauyan Najwa 





Lauyan ya furta "Nagode my lord" ya qara maimaitawa Mimi tanbayarsa





Girgiza  kai tayi kawai



Yace mijinki ya ta'ba tirsasaki yin wani abu dole..?




Shiru tayi yana kallonta sosai kafin ya fito mata a mutum ya furta 




mijinki ta'ba saduwar aure da ke da arfi.?




Irjinta ne ya buga ta saki hawaye tana kallon gaba 'daya kotun da suka qura mata idanu a yayinda baba ke mata alamar saqo da idanu 




Yawu ta ha'diya tana kallon baba 



Lauyan ma juyawa yayi yana kallon baba yayi murmushi ya furta 




Farida shin mijinki ya ta'ba kwanciyar aure da ke da arfi.?



Karki manta yadda mu ke zaune gurin nan haka zamu zauna ranar gobe a gaban babban alqali kuma zai hukunta duk wanda yayi qazafi a kan wani 




Mijinki daga ranar farko da ya fara saduwa da ke zuwa yau ya ta'ba yi mimi anfani da arfi wajen saduwa da ke.?



Hawaye ta fara sosai harda gumi irjinta na dukan uku2...











Kotun tayi shiru duk idanu na kanta ta saki kuka tana sunkwi da kai 




Mami ta kalli Dada tace wannan wace irin masifa ce abinda Allah ya 'boye yau gamu a kotu a na warwareshi 




Dada tace Allah ya kyawta kawai yaya ni al'amarin ya gindureni wlh 




Goggo jummai ta kalli Goggo hanne tace kiji Masifa wai har kwanciyar aure a ke magana gaban duniya ga wasu masu kayan tv can kinga sunata na'da 





Kallon General baba yayi yace "da Alana lauyan nan so ya keyi ya niqamu amma bai isaba 




General yayi ajiyar zuciya yace "babban lauya ne A Nigeria domin har waje yana fita aiki sun narka masa ku'di ne ya dannemu amma ni nasan wa zan kira anjuma bari mu fita 



Kallonta lauyan ya qara yi ya furta 





Farida daga saduwarki da mijinki ta Carlo zuwa yanzu ya ta'ba yi miki dole.?

💖AQIDARMU💖






PART2





No comments