Breaking News

AQIDARMU Book 2 Page 14

 🅿️1️⃣4️⃣






Saidai kuma ya tuna yanzu su ke da nasara in ya tuna hujjojin da lauyansa ya bada da kuma uwa uba takardun qarar da Mimi ta saka hannu da  haka ya juya koma masallaci da kwarin gwiwa







Tunda ya dawo 'dakinsa yayi shiru yana tariyo maganar Makas "yayi karatun ne kawai domin ya qara samun haske kan musulunci da AQIDOJI"




Wani irin danasani ta keji mara iyaka ashe mimi tana sane take son mijinta ta jajirce ba zata rabu da shi ba 




Kama kansa yayi yana danasanin mai yasa bai saurareta ba



Yana tunano ranar da ya mammare ta tana furta "yaya pls ka bari na maka bayani"




ya sake ajiyar zuciya yana tariyo yadda su ka yanke hukuncin maidawa Hayat 'yen uku shi da baba




Qwalla yaji da ya tuna yaran mimi bakwai amma  bata tare da ko 'daya kuma babu ko 'daya cikinsu da yasha nono yadda ya kamata 




Sosai ya ji kansa ya fara sara masa da ya tuna da shi su yanke hukuncin kaita gidan Gyaran hali na Barnawa inda yana sane da muguwar azabtawa yara da su keyi a gurin 




Wani irin danasani yaji da ya tuna shine ya tuna har kwanaki mummy tayi masa magana ta wpp ta nemi ya bata lambarsa suyi magana amma yayi blocking 'dinta 




Gashi yanzu jarabawa ta taso su gaba wannan magana tafi arfin waya dole sai gaba da gaba zaije ga baba 




Ya qara jin dana sani da ya tuna Wai har takwara Hayat ya masa cikin yaran Mimi amma bai ta'ba tunanin ko da ganin waye takwarar nasa ba




Jawo system 'dinsa yayi ya shiga internet inda ya shigar da sunan Hayat inda ya fara ganin komai game da Hayat 




Qura idanunsa yayi yana mamakin sauqin kai ma irin na Hayat 




Ya fimu arziki, ya fimu ilmi duka biyu ya fimu nasaba amma bai ta'ba kokarin nuna mana shi wani bane burinsa kawai *Mimi* 




 Kama kansa yayi yai shiru sosai ya ke danasani domin daga abubuwan da Hayat ya jure a kan son *Mimi* ya furta anya ko ni bai fini *sonta* domin ya nuna ya yadda da ita ya amince yayi komai domin kasancewa da ita 



A hankali ya furta ya Allah kamin afuwa ka sani ba da gangan bâ duk cikin rashin sani ne





Sosai suma su Safwan hankalinsu ya tashi da baba ya sanar musu an mayar da kara babban kotu da kuma gayyatarsu..





General da taimur kuwa da baba ya sanar musu murmushi su kayi General ya furta "kace sun maida inda zamu qarasa murqushe su" ai Abuja tamu ce gadara dai da tinkaho irin n'a sojoji haka General yayi suka yi sallama da baba





***************





Yau suke komawa kotun..!





Baba a su goggo da su mami dada da su Safwan su kayi sunyi motoci biyu na gidan baba da na Safwan




A yayinda General tun sunday su ka shiga abuja shi da Taimur inda ya cewa baba ma su sauka gidansa 




Su Najwa kuwa suka yanke sayan babban gida a Maitama n'a wani tsohon Ministan ku'di mijin zenat ne ya musu hanya suka saya gidan 850M inda su ka saya cikin ku'din ribar Hayat da sunansa Abu'noor yace ko babu komai Hayat  yanada bukatar gidan in ya shigo Nigeria ko kuma wataran in yaransa suka shigo Nigeria kamar yadda shima da kansa

 Ya sayi na kaduna sabida wannan dalilin 


.makeken gida ne da akayi kamar ba'asan darajar filin ba gida har gida inda ciki ba'a magana suka tare gidan a kan har a gama shari'a su koma 





Su mummy da Najwa sun shirya suma flyt zasu bi mimi ta so qin zuwa dole su ka tilastata inda asibiti ta shirya domin mummy da Najwa sun saya mata 'dinkakkun kaya sabida haka ta ke a asibitin babu ko takalmi 




Bayan ta gama shirin ta zauna kansa hawaye ta fara sosai ta 'dora kanta irjinsa tana shigar da yatsunta cikin na sa ta fara magana





Pls mine na tuba wlh bâti nadama komai kakeso shi zanyi wlh sonka zai kasheni nima in ka tafi ka barni ko kula da yaranka bazan iyaba ta saki kuka don Allah mine ka taimakeni ka dawo haka 



Su mummy da najwa suna tsaye suna kallonta 




Ta 'dago tana kallonsa kamar dai mara hankali ta shiga kiransa da tsammanin ya ansa ganin haka su mummy su ka qarasa ciki suna riqota Najwa na lallashinta ta qarasa shiryawa su wuce 





Mimi Najwa mummy suka bi flyt zuwa abuja inda su gidan mummy na gwarumfa su ka sauka 




11:00 daidai katun ya gama cika taf kowa na nan 




Mimi ganin su Goggo jummai da su mami ta koma gurinsu sunji da'din hakan da tayi sannan su mummy basu ji haushi ba kuma basu hanata ba 



Goggo hanne ce ta riqo hannunta ta ce "yaya mai jikin.? Sunkwi da kanta tayi tana qwalla tace "goggo yana yanda ya ke ta saki 'dan qaramin kuka"



Shafa bayanta goggon keyi tace ki fawwalawa Allah komai zai shige miki gaba yayi miki jagoranci ya kawo muku miki sauqin wannan jarabawa da ya ke tayi miki



'Dora kanta tayi kafa'dar goggon tana kuka sosai goggo ta lallasheta har tayi shiru su kaji zaa fara gabatar da qara





Kallonta Taimur ke yi sosai kamar ya ha'diye ta kuma kamar bai san matar wani bace  tsabar rashin tsoron Allah na yawancin sojoji domin mafiyansu sam kamar quda suke (yaki haram yaki halak)




Da ta lura da kallonta da ya keyi ta qara matsawa sosai jikin goggo tana sunkwi da kai 




Mai gabatarwa ya fara bayani inda yace Kotu na kiran (Farida Muhammad)





Wani irin harbawa irjinta yayi kafin goggo ta motsata alamar ta miqe 




Da kyar ta tashi ta nufi gurin batasan ma su Najwa ke da wannan qarar ba duk tsammaninta su baba ne 




Zama tayi a ka bata ku'ani ta shafa a ka ce ta gabatar da kanta ta kuma bada takaitaccen tarihinta 




'dan dagowa tayi taga yadda idanun kowa ke kanta musamman baba da Taimur da goggo binta da Safwan ta fara bayani




Ni sunana Farida Muhammad..



An haifeni kaduna mu uku ne gurin iyayenmu Rukayya, Salman, sai ni, Allah yayiwa Rukayya rasuwa saura ni da Salman iyayena duk sun rash nayi primary da secondary kaduna 




Alqalin yace kinada aure.? 



Irjinta ne ya buga ta 'dago tana kallon mutane duk an tsura mata idanu qwalla ma ta fara taji lauyan ya qara maimaita tanbayar 



Idanunta fal da qwalla ta furta *EH* ya kura mata idanu kafin ya sake furta 



Ya sunan mijinki.? 



Yawu ta ha'diya ta kalli su baba da duk idanunsu ke kanta ta dawo kan lauyan da shima ya kafeta da nasa yana jiran ansarta 




Wani irin bugawa irjinta ke yi ya sake maimaita ya sunan mijinki..?

💖AQIDARMU💖





PART2 


No comments