Breaking News

AQIDARMU Book 2 Page 13

 🅿️1️⃣3️⃣








Kiran sunan Allah kawai ta ke yi sabida yadda sam hawaye ma ya qafe mata a idanu 




Kallonsa ta keyi jikinta ya shaking idanunta su ka qafe suka juya zuwa wani kala tsabar tashin hankalin da take jin kanta a ciki 





Cikin wata irin jarumta da batasan tana dashi ba ta 'dagashi ta maida kansa kan fillow a hankali ta nufi toilet 'din word 'din 





Alwala tayi ta dawo ta shimfi'da dadduma ta tayar da sallah 




Mummy da najwa su ka shigo ganinta suka ja suka tsaya saidai suna kallon injunan Hayat da suka nuna 0%100 saidai wannan koren na nan alamar jininsa ne ya sauka zuciyarsa ta gaji domin in mutuwa ne koren zai 'dauke tass ya saura ja kawai 




A hankali suka juya su ka fita suma duk basu cikin hankalinsu tashin hankali yaqi karewa shekara kusan uku a ana abu 'daya 





Kallon Baba General yayi yace "amma nayi mamakin yadda yarinyarnan bata iya 'boye masifar son da takewa wannan balaraben yaron ko da yake kyawunsa da dukiyarsa da Nasabarsa ke ru'dinta amma in ba haka ba yarinya daga babban gidan malami kamar ka a ce har sai an kwashe kusan 3yrs a na abu 'daya taqi hakura da shi ko da bacin ma yaran zamani ni da irin kishin nan nawa sam bazan iya son mace kamar ta ba da nasan ta gala sadaukar da rayuwarta da zuciyarta vs wani na 



Amma shi Taimur yace haka yake sonta wai zai koyar da ita sonsa fiye ma da shi balaraben fatanmu dai alqali ya yanke hukuncin da muke tsammanin 




Baba da ya fa'da tunani sai yanzu yayi magana ya furta IA domin kamar naci amanar iyayena da kakanni ne idan har na barta rayuwa da wannan yaron shegen yaro kamar aljani ga kyaw ga naci 




Haka su kaci gaba da tattaunawa ....






Yana zaune wani kyakywan guri yayi nisa cikin tunani yaji baban na kiransa ya ansa da "Baba gani" yaje. Baban na zaune kan farar dadduma saidai baban babu walwala yace "ka zauna" 



A hankalinsu andya zauna ya tara hankalinsa kan baban nasa baban ya fara magana 




Salman shin bakasan baby mai shiryawa face Allah ba.? Shin kasan Allah ya haramtawa wani bawansa cire rai daga rabon rahamarsa.? 



Baban yaci gaba inaso ka sani Allah da kansa ya za'bawa Farida mijinta kuma ko da ni ne bana kaunarsa dole zanyi hakuri idan har Allah na sonsu tare 




Ma'aurata nawa suke zaune da mazajen da ke sa'bon Allah suke rufe sirrin sa'bon domin sunawa mazajen nasu tsammanin shirya 




Babu wanda zai fini kaunar farida bayan mahaifiyarku kuma na yadda ubangiji ne ya za'ba mata mijinta ba tare da yayi shawara da ita ba ya kamata ka yadda da qaddarar qanwarka 




A hankali cikin nitsuwa ya furta baba shi'a ya keyi fa.. baban yace ko kaine mai canza hukunci.? Ubangiji yace wani littafinsa na canzawa lokacin mutuwarsa wani daga sa'bo zuwa shiriya wani kuma daga shiriya zuwa sa'bo 




Abinda na keso da kai ka nutsu ka fuskanci qanwarka ka taimaketa tana cikin tsananin bukatarka kuma hakki ne a kanka ka taimake ta 




Ajiyar zuciya Salman yayi 




Baba yaci gaba ka kusanceta ka saurareta ka fahimceta na tabbata IA zaku samu mafitar komai a tare 




Toh yace baban yace kamin alkawarin yin haka yana kallonsa 




Shiru yayi kafin ya furta "Insha Allah baba na maka alkawari"




Baba yace Allah ya muku albarka ka gaisheta 




Za taji ya furta zai qara magana yaga baban ya 'bace 




Wani irin gumi ya keyi ya farka baccin a hargitse yana kulla bed syd lamp ya duba agogo 3:46 am gyarawa yayi ya jingina da gadon duk yayi uban gumi dukda ac da ke 'dakin 




Tariyo mafarkin ya keyi tare da tuna wani malaminsu da yace musu 




Mafiya yawan malamai sunyi ittifaqi a kan mafarkin tsakananin 2/4 daga Allah ne ko ishara ko wa'azi ko nasiha daga ubangiji 




Ajiyar zuciya yayi tabbas alama sun nuna Mimi na tsananin bukatarsa shiru yayi sam bayason hasasho wai 'dan shi'a mimi ke mutuwar so take son qare rayuwarta and da shi 



Ganin baccin bai 'daukeshi ba ya miqe zuwa masallacinsu na school domin yana (Limkwakwing ne university of technology and marketing kuala lampur ) wanda Hayat da kansa ne yayi masa komai na makarantar 



A masallacin ma ya samu wasu frnds 'dinsa 'yen Saudi da sudan dama su yawanci masallaci su ke kwana ibada 



Ganinsa yau su kayi mamaki domin shi yafi qoqari a class amma tanan ba gwani bane 



Makas da Anuwar ne bayan sun gama fajr tare da Salman su ka fito suna fira su ka nufi Cafe na school shi makas ya fara project 'dinsa inda hira ta 'balle tsakaninsu 



Anuwar ya kalli Salman yace kai kan me za kayi project.? Shiru Salman yayi kafin yace ni ban gama yanke hukunci ba 



Anuwar yace ni a kan Sallah zanyi 




Makas yace ni a kan "AQIDARMU" kallonsa duk su kayi yayi murmushi yace ko kuma ince a kan AQIDOJI




Salman da Anuwar hat suna ha'da baki wajen tanbayarsa mai yasa za kayi project a kan AQIDOJI.? 



Ajiyar audits yayi yace sabida mutane ke fuskantar qalubale a aqidoji tare da gabar da ke ci gaba da haddasuwa kullum tsakanin al'umma duk sabida sa'bani da banbancin Aqida



Yaci gaba kamar ni AQIDARMU itace *Izalatul bidi'a wa'iqamatu sunna*



saidai hakan bai hanamu mu'amala da mutanen AQIDOJI daban da AQIDARMU sa'banin wasu sun 'dauki banbancin AQIDA kamar yaqi da gaba wanda hakan yasa yau a duniya kashe2 da fya'de da sauransu su kayi yawa mutane na tsammanin 'bata gari ne kawai ke aikata hakan alhalin in zamu bincika harda rashin zaman lafiyar 'yen aqidu 




A kwanaki anyi wani babban taro a Bahrain an gayyaci manyan malamai na duniya da hazikan 'dalibai na Ummul-khura inda a kayi ta hira da su kan matsalar babancin aqida wanda daga cikin matsalar da (Isra'ila da Syria ke fuskanta kenan shakaru da dama, hakan Palestine wato band de Gaza da suka kasance sahara yanzu tsabar rashin zaman lafiya da tashin hankali tsakaninsu da Irak 




A cikin taron anyi hira da wani matashi balaraben Iran wanda tarihinsa ya matukar 'daukar hankalina 



Babansa balarabe ne sananne a Iran domin kakansa ya kasance hamshakin mai ku'di wanda ya ke baqo mai da kansa 




Sannan mamansa 'yer Nigeria ce kuma 'yer babban malamin Sunna 




A yayinda ya kasance tsakanin tanbayoyi bayan rasuwar iyayensa tun yana shekaru tara 




Yayi karatunsa Miami degree masters da PHD kan industrial chemistry yana aiki Gidan mai da gas na qasar iran inda ya shafe rayuwar quriciyarsa wajen neman sani a kan AQIDOJI domin ya bar shi'a tun yana aji biyu na secondary saidai tanbayoyi suka dameshi kan sani Menene Musulunci da AQIDOJI



A qarshe ya yanke hukuncin yin degree kan tarihin musulunci a Ummul-khura inda ya fito da F/class inda a za kuyi mamaki in nace muku yayi karatun ne kawai domin ya samu haske kan addininsa and yanzu haka har falon shuraim da Musti menk yana shiga kai tsaye tsabar girmamashi da su keyi bari ma kuga videon da su kayi kwanaki a ka gayyaceshi rabawa sababbin hazikan Ummul-khura kyawtuttuka inda shima ya 'dauki nauyin 'dalibai "dari 




Karkacewa Salman da Anwar su kayi makas ya saka video 



Cikin mugun mamaki Salman ya ke kallon video ganin Hayat 'dagowa Yayi ya kalli Makas yace ya sunansa.? 



Makas yace gashican kan kujerar gabansa baka gani.? *Hayat Muthallib Ahnan* 



Yawu Salman ya Ha'diya ya kar'bi wayar yana kallo shi ka'dai 



Murmushi anwar da makas su kayi à tsammaninsu Sha'awa taron ya bawa Salman saidai shi ya 'dimauce cike da mamaki da danasani ya ke kallon hoton tabbas *Hayat 'din mimi ne* ya furta a ransa ya 'dago yayi shiru Makas ya ansa wayarsa yana furta muma dai Allah Outaouais bamu muyiwa musulunci hidima



Amin Anwar yace Salman kam yayi nisa inda a hankali ma ya miqe yana tafiya kamar makaho su ka bishi da kallo






Sai kusan 2:45 am ta fara gyangya'di domin tana sallah ma Dr yazo duba Hayat a dole ya koma ganin ba hanya 




Tunaninsa ta keyi tana tariyo yadda komai ya fara tsakaninsu 



Runtse idanunta tayi tana jin yadda zuciyarta ke tuhumarta da rashin bashi hakkinsa yadda ya kamata da ta bishi tuntuni sun koma Iran da duk basu iso wannan matakin ba 



Kama kanta tayi tana tuna ranar da yake fa'da mata (banida wani shakiki da ya kai a yanzu a wannan duniyar) so take tayi kuka sam kukan yaki ta sake tariyo 




Wlh baby zan iya sadaukar da komai na domin mu kasance tare 



Wani irin numfashi ta ke ja a hankali ta 'daga kanta tana kallon injunansa 19%100 ta sauke ajiyar zuciya tana tunanin yadda aurensu yake tafiya tsawon shekaru uku kenan 



Saidai su ci junansu a duk inda bumatar hakan ta kamasu su gina cikin yaransu duk inda qaddarar hakan ta kasance sannan ta haifi yaran duk inda hakan ya fa'do 



Hayat yanada ku'di mara iyaka amma har yau basuda ko muhallin zama sabida a matsayinsu na ma'aurata and sabida banbancin AQIDA 



Yaransu na rabe a duniya yanzu haka sau 'daya ta ta'ba ganin *Najma da Noor* su kuwa 'yen uku babu wani sanayya suma tsakaninsu da ita 




Sai *Huda da Inthee* suma zuwa yanzu batasan kamanninsu ba banda hotonsu da vedeo da ta gani wayar Hayat 



Jiri ta fara ji sosai itama ta kama kanta tana lumshe idanunta saidai kanta kamar zai tarwatse ta fara fidda numfashi jin gudan jinin da ke mararta shima ya mur'do wani irin qara ta saki tana kwanciya kan daddumar sai yanzun taji wasu hawaye masu zafi na gangaro mata tare da tunano mata * hasken zuciyarta da bata sani ba ko zai qara taka doron kasa




Mummy ce ta shiga sabida Najwa ta koma gida sabida da sassafe zasu je abuja maganar kotun da zasu maida case 'din Hayat 



da sauri mummy ta riqota tana furta "Subhanallahi Farida"



Hawaye mimi ta matso ta furta mummy "dubamin ko yana motsi" kallonta mamy ta shiga yi cikin mamaki kafin ta furta 



Ki bari mu ji da ke tukuna shi ai muna ganin saukinsa da kanmu bari na kira Dr ya duba ki ta miqe 





*************





11:14 am office 'din lauyan a abuja us kallesu yace IA monday zamu shiga 




Alhamdullilah Abu'ahlam yace lauyan yaci gaba 




Duk documents 'din da Qanwarku ta ha'da ya bamu damar ci gaba da shari'arnan ko babu Hayat muthallib tunda kawai ita matarsa so ya zu haka shammaci yana dab da isa Kaduna da Calabar 



Murmushi Najwa tayi tace Tnx a gain barrister 




Baba na masallaci suna taron komitin masallaci a kace a na sallama da shi ya fito 



Wani matashi ne da bai fi 40yrs ba ya furta "barka da safiya baba"



Baba ya ansa "barka"




Enveloppe matashin ya miqawa baba yace daga babban kotun qasa da ke abuja 




Yawu baba ya ha'diya yana kallon mutumin 



Saidai ganin kamar bai fahimta ba mutumin ya kar'ba ya bu'de ya fara karanta masa 




Daga babban kotun qasa na abuja muna neman ka kan kallai a ranar 17/06 domin ansa kiran da kotun ke maka na kararka da *THARIQ AHNAN FAMILY* ke yi 




Zuwanka dole ne tare da mutanen da ke qasa kamar haka 




Safwan Mu'az 


Binta Haruna


Salman Muhammad 


General Sa'id hashim



Taimur Sa'id hashim 



Mun gode ..



Mutumin ta maidawa baba takardar ta tafi 




Wani irin zufa ne ya fara karyowa baba kansa ya fara sarawa idanunsa su kayi duhu tanbayoyi suka cika shi makil 



Kotun qasa gaba 'daya Innalillahi ya ke furtawa x3...

💖AQIDARMU💖





PART2


No comments