Breaking News

AQIDARMU Book 2 Page 12

 


🅿️1️⃣2️⃣








Qara riqo hannunsa tayi cikin gigita da 'dimuwa da kyar  ta iya furta *Mine* bai ko kalli inda take ba saidai wani irin bugawa da zuciyarsa tayi da arfi 



ya fara ganin duhu dama ba gama warkewa yayi ba 



Cikin tashin hankali ganin yana lumlumshe idanunsa yana layi ta qara qoqarin sake riqo hannunsa saidai wani irin kamar irjinsa yayi ya yanke jiki ya fa'di a sume 




Jakar hannun lauyan baba ce ta fa'di ya fara gumi ya juya yana kallonsu baba da ko gezau 




A gigice mummy ma ta qarasa Najwa na zaune tana shaqar abinda take shaqa 




Wani irin kuka ta keyi ta fara sambatu kamar hauka sabon kamu 




Nashiga uku don girman Allah ka tashi wlh zan fa'da yadda abinda ya faru ba yadda kaji ba" ta kalli mummy kamar mahaukaciya tana furta mummy na shiga uku wayyo Zuciyata 




Mummy hawaye ta keyi tana kallonta tama rasa wa zata taimakawa cikinsu ita da Hayat kawunansa ma tsabar tashin hankali da suke ciki ko motsi sun kasa kamar an shuka su 




'dora kanta tayi irjinsa tana kuka tana sambatu "pls mine ka tashi ka tausayamin wlh gara ni in  mutu da in zama sanadiyar mutuwarka mine ka tashi don Allah wayyo mama wayyo ya Allah ka na tuba ka sassautamin yarana babansu ya Allah ta qara sakin kuka sosai tana zama qasan 




Wani irin hawaye dada da mami da su goggo ke yi kamar yara 



a hankali mummy ta furta "Farida kiyi hakuri ai ba mutuwa yayi ba ta juya ta kalli su Abu'noor da kana ganinsu kasan sun kai qololuwar bakin ciki saidai a hakan ta musu alama da suzo su 'dauki Hayat shiru kafin Abu'Ahlam ya taso ya qaraso ya ta'ba gefen wuyan hayat ya kalli mummy



Mimi ganin yadda yayi ta qara matsawa tana furta mummy mu saka masa ruwa bazai mutu ba yamin alkawari bazai tafi ya barni ba 




Kallonta duk su keyi da mugun tausayawa a hankali shima Abu'noor ya qaraso zuwa lokacin da gorar ruwansa na sha su ka fara yayyafa masa shiru bai farfa'do ba 




Idanunta ne suka qara cikowa taf da hawaye ta anshi robar ruwan ta juye masa a fuska zuwa irji shiru ta juya tana kallon mummy 




Wani irin sababbin  hawaye ne suka shiga sulalo mata ta 'dago kansa ta kai hancinta kan nasa tana shako numfashinsa shiru ta saka hannunta zuciyarsa shiru ta furta "Ya Allah ka 'dauki raina nima tana sakin hawaye"




wani irin jijjigashi ta shiga yi ta saki kuka tana furta shikenan tawa ta qare 




Alqalin da kansa wani irin qwalla ya ji a gefen idanunsa ya ajiye biro 'dinsa ya kama kansa inda shima lauyan su baba ya zauna da'bal a kujera yayi shiru 





Su kuwa su baba suma shiru saidai su na nasara da suke ganin sun samu inda Taimur yafi kowa




Safwan ma da mamansa babu wanda yayi yunkurin zuwa lallashin mimi cikinsu 



Su goggo na son zuwa saidai ganin yadda surukanta ke gurin yasa basu qarasa ba 




A qarshe alqalin ya bada sanarwar 'daga shari'a zuwa farfa'dowar Hayat ya shige ciki jikinsa duk a mece




duk sunyi jigum suna kallon mimi da ke ta sambatu da kan Hayat a cinyarta da Kyar Abu'Ahlam ya kalli mummy yace kamar dogon suma yayi muje asibiti "bata iya magana ba Abu'Ahlam da abu'Nawwal su ka 'daukeshi suka wuce a zabura mimi ta bisu sai lokacin baba ya kira escorts da ke waje wai su riqe Mimi 



Suna fita an saka Hayat a mota suka shiga Mimi zata shiga su ka riqo ta, ta shiga fisge2 tana jefa qafafu kamar jarirai cizo yakushi inda ta gantsarawa 'dayan cizo har fatarsa da namansa su ka fita ya saketa yana qara ta fisge a hannun 'dayan ma ta kwasa da guru saidai itama garin gudun mashin ya ka'deta jini ya 'balle mata dukda bata suma ba kamar ya sani ya 'dauke ta zuwa asibitin 44 itama 




Tana kuka tana furtawa nurse wai ta barta zata fita nurse 'din tace tayi hakuri saidai fusge jikinta tayi ta miqe tana dafawa nurse 'din zata biyita ta 'dauki almakashi tace kika biyoni zan soka miki dole nurse 'din ta tsaya 




An dubashi kuma dr yace zuciyarsa ce tayi qaramin bugawa yayi dogon suma saidai stlill hakan bai kamata ba a yanzu ganin bai da'de da fitowa daga comma ba zai iya mutuwa in da qarar kwana don haka yacewa su mummy lallai a kiyaye masa tashin hankali 




da kyar take takawa jikinta duk jini ta bari a dubata a gani cikin ya fita ko yananan taqi 



.a haka take tafiya har ta hango su Abu'noor 





Kallon su baba lauyan yayi yace "Munyi nasara" saidai...




General yace saidai me.? Yayi ajiyar zuciya yace ban ta'ba aikn da zuciya ta ta karaya ba irin wannan a gaskiya ban ta'ba ganin soyayya kalan ta yaran nan ba 




Tsaki Taimur yayi yana juya fuska baba ma tsakin yayi yace ai ko jinin juna suka sha kowannensu zai amayar da na 'dan uwansa tunda dai yanzu gashi rabuwa dole ya kalli lauyan yace kenan yanzu a na dawowa alqali zai bada takardar ta ko.?



Lauyan yace eh saidai ina fata kada abubuwan da suka faru su zama wasu hujjoji da zasu tallafawa yaran wajen ya canza shawara 




Shiru baba yayi..




Alkalin Iyace amma karka damu IA zamuyu mu gama ni kaina a yau kawai shari'ar ta isheni zanyi komai domin mu gama da wuri 



Ok baba yace su ka masa godiya su kayi sallama 




Ganinta jina2 mummy da Najwa su ka taro ta itama kanta jiri ta keyi bata gani Sosai 



Su mummy su ka zaunar da ita



Najwa ta kira wata nurse tace maza zo a nan ki duba mana ita nurse 'din ta zo ta fara duba Mimi inda tace dole a mata scanning zata qi mummy ta riqeta suka tafi tare 





Hayat ya farfa'do kawunansa na kansa suka fara masa sannu saidai a take komai ya fara dawo masa 






*Ina kichen ya 'daukeni ya tafi yada ni yayi Abinda zaiyi da ni* ya saki numfashi *Yah Salman ne da goggo su ka tilastani* 



*ga takardu ta saka hannunta da kanta na bayanan yadda Hayat Muthallib ke saduwa da ita da arfi* 




su kaga yana wani irin numfashi na masu shirin mutuwa su kaga ya shiga yi suka yo kansa 




A anyi scanning cikin ikon Allah cikin na nan suka dawo mummy na lallashin Mimi a kan tayi hakuri a bata kulawar da ta kamata saidai nan suka samu sabon tashin hankali da sauri mummy ta qarasa Mimi na jan jiki da kyar har itama ta qarasa suna shiga word 'din yana tari 




Mimi turesu duk tayi jin Abu'Nawwal na cewa Abu'Ahlam Haka commander Salim yayi ranar da zai ras..



Mimi ta riqo hannunsa tana hawaye bai ma san wa ke kansa ba ya da'de yana 'boye damuwarsa yanzu abin ya taho masa gaba 'daya niyar zama ajalinsa 




Hawaye Mimi ke yi ta furta Mine ka taimakeni ka bari haka ni na yadda na kwanta amma kai ka tashi ka taimakeni Hawaye ta keyi duk muryarta ta dushe 



Zuciyarsa ke wani irin mur'dawa yana tariyo komai 



Shekara na uku kenan yana auren mimi suna rayuwa a gantale suna haibuwa a gantale daga nan zuwa can taji tarinsa ya qaru




Wani irin kuka ta saki ta kwanta jikinsa tana kiran sunansa saidai baima san mai ke faruwa ba juyawa tayi ta kellesu duk suna tsaye suna kallonsu ta fara magana 




Mummy na shiga uku yau ajalina ya sauka kimasa magana ni na yadda in mutu shi ya tashi 



Hawaye mummy keyi ita kanta yanzu ta rasa mai za tayi 




Komawa tayi qasa ta durkusa ta furta na tuba ka tashi pls wlh na tuba zanyi komai kakeso taji tarin na qaruwa 



Ta qarasa zama qasa tana kuka sosai ta rasa mai kuma zatayi ta koma kamar mara kai 



Abu'Ahlam ne yace Yasmin kira Dr ta fita jiki a mace suka shigo da dr ya qarasa ya fara duba Hayat saidai ya juyo yana kallonsu yace gaskiya da wuya ya tashi...




Mimi ta miqe tace "waye zai hanashi tashi.? Kallonta ya shiga yi kafin yace Aman jini ya keyi ma'na ya kamu da Ciwon zuciya kuma g... 



Yaga tana wani irin hawaye ta tureshi ta sake komawa kan Hayat ta 'dagoshi duk suka juya suna kallonta ta fara magana 




Mine nasan na maka laifi but pls kabani ko wani irin irin punishment banda wannan "last tym ka ce bazaka sake tafiya ka barni ba ka cika alqawari pls 




Ta saki kuka sosai duk fita su kayi suka barta 




Abu'Ahlam ya kalli 'yen uwansa yace wlh in Hayat ya mutu sai na tabbatar dukkansu sun bishi 




Hawaye mummy ta share ita sam kalamai sun qare mata a baki 




A hankali ta ke rera kukan tana riqe da kansa a cinyarta taji ya sake fara tarin ta qura masa idanu tana kallonsa tass yayi jini ya feso a fuskarta a hankali ta shafa ka'dan taga jinin yana yi yana lumshe idanu numfashinsa na qara sauka har taji shiru ta kalli Injin taga yana komawa 5%100 




Idanunta ko motsi ba suyi  kansa a yayinda irjinta ke harbawa zuciyarta ke shirin fitowa irjinta hawaye kuwa zuwa lokacin sun bushe  a idanunta




Jin 'diff ta kalli injin ta jawo numfashinta da wani irin qarfi tana furzar da wani irin Iska mai zafi yayinda ta shiga kiran duk sunan Allah da yazo bakinta...

💖AQIDARMU💖






PART2


No comments