Breaking News

AQIDARMU Book 2 Page 11

 


🅿️1️⃣1️⃣





Suna gama wayar ya kashe wayar yana sake furta Alhamdulillah  Allah...







A washe garin Lauya matarsa ta haihu operation inda hakan ya sashi jikirta shigar da documents 'din domin kai da komowa na hidimar matarsa a asibiti





Inda ko da baba ya kirashi yasan yadda baba ya matsu don haka ya cewa baba ya shigar saura a kirasu kawai baba yace madalla 





Shima Salman yau ya koma malay yaso sabida jarabawa da zasu fara ba kama hannun yaro in yaje bazai kara zuwa ba sai ya kammala karatun gaba 'daya 





**************






Yau kwanan Hayat goma sha tara a asibiti Mimi ke jinyarsa saidai su mummy suzo su tafi and saidai itama yanzu laulayi ya fara taso ta gaba su mummy sunyi2 ta rika komawa gidan mummy ko gidan Hayat tana hutawa amma taqi dole su ka kyaleta..





Inda kotu tace bata sauraron qara sai dole Hayat ya warware dukda hujjojin da lauyan baba ya bada sannan itama Najwa nata lauyan haka ya fa'da mata dole duk suka hakura suna jiran warkewarsa."







**************




Yau kwanansa arba'in da bakwai da asar Mimi kan dadduma ta idar da sallah tana karatu ta hango yatsar afarsa na motsi da hanzari ta qarasa ta na kallon idanunsa da suke motsawa zama tayi ta 'dago kansa tana kallonsa ta furta *Mine* kokari ya rika yi har ya bu'de idanunsa ta saki hawaye ta tana rungume kansa tare da furta "Alhamdulillah" taji said motsin shigowa ta juya Dr ne ta furta "ya tashi" 




Dr yayi murmushi yace eh ai mungani ta injunansa shiasa nazo nan ta tashi ta ya fara dubashi 




Kusan minutes ashirin ya kalleta yace mu gode Allah babu abinda ke damunsa yanzu sai ya samu abinci mai kyaw da kulawa yadda ya kamata




Tace Nagode Dr tana sharar qwalla yayi murmushi yace Allah ya qara masa lafiya tace amin ya fita ta koma kansa tana riqo hannunsa tayi kissing Sosai ta shigar da yatsunta cikin nasa tana kallonsa 





Yau kwanansa biyar da farfa'dowa yayi qwari sosai sabida kulawa daga Mimi mummy Najwa a yayinda fargaba ya dawowa Mimi na shara'din da su daddy zasu bata tunda yanzu ta gama jinyarsa saidai bata bari kowa ya gane fargabar ba shi kuwa Oga Hayat da yasanta kamar yunwar cikinsa tsaf ya gane tana cikin garba dukda baisan na mene ne ba ya alakanta hakan da komawa gida da zatayi bayan an sallameshi 





General da kansa ya shigo kaduna gun baba su ka tattauna a kan batun takardun da Mimi ta saka hannu General yace kaga mun gama da wannan 'bangaren saura mu jira kuma har ta haihu wannan ciki shi yafi damun Taimur 




Baba yace yayi hakuri dama in aski yazo gaban goshi yafi zafi amma na masa alkawarin tana haihuwa da sati zan 'daura musu auren tunda in yayi sakin yanzu haihuwarta shine iddarta dukda nasani ba'a saki da ciki amma wannan mayen balaraben bamuda mafita dashi inba haka ba 




General yace kama manta maganar ba'a saki da ciki shi kansa aurensa haramun ne 'dan shi'a kawai dai dole mu tabbaatrwa duniya ya saketa shiasa domin kada yazo yana binta gidan wani mijin yana 'barna tunda 'yen shi'a basu banbance halak da haram 



Baba yace wannan haka ne su duk wata halaka itace halal a gunsu shiasa 'dan shi a 'dan wuta ne 



General yace sosai kuwa su ai wutar ma sai an anbata ba Allah dai ya tsaremu da ko gaisuwa da su bare alakar ha'da zuri'a inba basin qaddara ba 




Baba yace amin su kaci gaba da tattaunawa abinsu.





Jama'a wannan babban kuskure ne kawai ka yankewa mutum rabonta da rahamar Allah komai sa'bon da ya keyi indai yana raye haramun ne wlh Allah ya ganar da mu.





da yamma ne a na gobe za'a sallameshi tana ba shi coffee yana sha su kaji an shigo gaba 'daya su ka juya inda take ta saki kofin hannunta shima kallon escorts 'din ya keyi su ka furta "yau contract 'din da kuka yi da Baba ya cika kina sane ko"?  Hawaye ta saki ta juya tana kallonsa shima ita ya ke kallo cikin rashin fahimta 




Munafukin escort 'din ya kalli Hayat yace "da kanta ta amince da contract tsakaninta da Iyayenta and kuma yau zata fara cikawa ta kuma sani sarai muna zuwa 'daukarta "



Yawu Hayat ya ha'diya yana kallonta ya furta "baby wani contract ne kika yi da su"? 



Batasan mai zata ce ba domin itama har yanzu batasan shara'dinsu ba ta 'dago tana kallonsa da niyar magana escort 'din yace mu bamuda lokacin da zata maka bayanin so ka bari jibi ku ha'du a kotu kaji Hawaye ta keyi sosai ya 'dago fuskarta yana furta "baby ke na ke sauraro contract 'din mai kika yi da su"? 





Kuka ta saki sosai domin itama yanzu ta fara danasanin amincewa kafin taji yanzu batasan menene shara'din ba ta 'dago tana kallonsa tana kuka escorts suka matsa suka furta mu je tun kafin muyi abinda za'azo ayi dana sani gashi guri na marasa lafiya 




A hankali ta miqe tana kallonsa tana kuka shima dai kallonta yayi ya cire kansa yanason tashi saidai sosai kansa a kwai jiri yana kallo suka tasa ta gaba su ka wuce a waje su mummy su ka ha'du da su saidai basu ce ba suka wuto 




Kallonsa mummy tayi ta furta my boy ya jikin.?




Kallonta yayi cikin rashin walwala ya furta mummy Contract 'din me Tayi da iyayen ta.? 




Yawu mummy ta Ha'diya ta kalleshi tace son wlh ban sani ba amma tabbas kam tayi akwai yarjejeniya tsakaninsu kan jinyarka da za tayi wanda a gabanmu ni da Maman kauthar  yayanta ya na'da yarjejeniyar saidai munada 'dan nisa da su bamuji mai suke cewa ba shiru yayi ya sunkwi da kansa qasa





*************





Kwanansa biyu da komawa gida gurin mummy ya ke tare da kauthar sabida school 'dinsu 'daya da su twins




Yau za'a koma kotu inda lauyan Najwa shima gobe babban kotu zata kirashi su koma can da qarar saidai su sunason shammatar su baba ne 




Sanye yake da shadda gezna lyt brown daidai jikinsa yayi wani irin fitinannen kyaw yasa baqin cover shoe sai silver watch 'dinsa kai Hayat arshe ne a kyaw da ha'duwa don ma shi ba mutum bane mai zuzuta kansa he is very simple dukda tarin dukiya da Allah ya masa rungumar yaransa yayi 'daya bayan 'daya domin gun mummy su ke tunda Hayat ya dawo yau ne bayan kotu zasu koma gun Najwa 





Kotun ya cika iya cika ta 'bangaren Hayat kawunansa a safiyar suka sauka kaduna suma ta 'bangaren mimi babu and wanda babu sai matasa da ke skull 






Baba General Taimur duk a na cike da annashuwa..!




Mai gabatar da qarar saidaiya fara bayani ya gama lauyoyi su ka gabatar da kansu inda a yanzu lauyoyin baba uku da wanda General ya qara masa babban lauya ne a Nigeria 




Lauyan baba ya fara bayani ..



Kallonta ya keyi tana kusa da mami tayi kyaw dukda ramar da tayi tana sanye da atamfa sky blue goduwar riga da hijabi saidai tayi kyaw fuskarta babu komi fayau 



A hankali itama ta 'dago idanunsa su ka nurse cikin na ta saidai tsabar fargabar da take ciki ta sunkwi da kanta shi kuwa yana ci gaba da kallonta har yaji lauyan baba na bayani




Mai girma mai shari'a mai qara na neman kotu tayi masa adalci da shi da marainiyar 'yer qaninsa uwa 'daya uba 'daya da kacokam rayuwarta ubanta ya bashi amana yaci gaba




Hayat Muthallib 'dan Hamshakin mai ku'din nan ne na iran jikan shahararren mai gidan man da gaz na *Thariq Oil and Gaz Industrials* wanda shararsu dayawa an sansu a africa musamman yadda su ke da dillalai masu shigowa africa suna 'dibar musu yaran talakawa suna kai musu suna musu bauta suna yaudarsu da ku'di suna biya musu karatu a arshe su nutsar da su cikin aqidarsu ta shi'a dayawan yara yaran Nigeria sunacan yanzu haka suna aiki kamfanoni *THARIQ AHNAN* wanda ba wani bane CEO na wannan kamfanoni face Hayat Muthallib duk kuwa da shi baya aiki da ko 'daya daga cikin wannan kamfanonin 



Mai girma mai shari'a ta wannan hanyar ne Hayat da qanwar mahaifiyarsa suka ha'da baki wajen yaudarar marayun yaran qannin Mai qara inda shi yayanta suka turashi Iran bayan yaga ne ya gudo ita kuma qanwarsa su ka ha'data auren mutu'a da Hayat jikan Thariq Ahnan wato Ceo na kamfanoninsu wani irin numfashi Hayat yaja yana qoqarin miqewa mummy da Najwa su ka riqeshi lauyan yaci gaba 



Inda Hayat ya shiga saduwa da Yarinyar yana mata ciki tana haihuwa suzo shi da danginsa kwace yaran su tafi da su domin dama manufar yin auren kenan su samu qarin zuri'a bayan shi Hayat  a kan  daga ta gama basu adadin yaran da su ke bukata sai ya sake ta inda...



Hayat ya fusge hannunsa ya miqe Abu'Ahlam da Abu'noor su ka riqeshi tamau ya tsaya 



Lauyan yaci gaba Inda Hayat ganin yarinyar ta bijire masa taki yadda yaci gaba da zina da ita



hawaye ne Hayat ya saki mai 'dumi kawunansa na kallonsa lauyan yaci gaba 




Ganin ta bijire masa ta gudo ya biyota Nigeria har gidan ubanta yana zuwa saduwa da ita ya inda yanzu haka wani cikin gareta nasa 



Hawaye su goggo kansu su keyi jin irin qaryar da lauyan ke shiryawa kuma a gaban baba 



Mimi kuwa kuka ta sunkuya cinyar dada ta nayi dada kanta hawaye take tana mamakin tsaurin ra'ayi irin na mijinta 




Lauyan yaci gaba mai girma mai shari'a yanzu ina 'dauke da hujjoji da kuma saka hannnun Ita kanta yarinyar na tabbatacin bayanan da na gabatar wa kotu na abinda Hayat ya aikata a kanta 




Sannan ga hira da a ka fara yi da ita bayan ta dawo ya kunna voice 




Wani irin hawaye mimi keyi na maganar da suka yi ne ita da dada à word 'din mama ranar da mama ta rasu 



Kallon dada mimi ta shiga yi tana hawaye dada ta shiga girgiza kai alamar sam ba ita kuwata bada voice 'din ba a hankali ya juya yana kallon mimi itama girgiza masa kai take yi tana hawaye har voice ya qare 



Lauyan ya sake  saka voice 'din Mimi .ca Salman da goggo inda mimi ke maganar sakin kuma mimi bata furta sun sake saduwa a ranar da Hayat ba 



Lauyan yaci gaba sannan mai girma mai shari'a a qarshe zan gabatar da shaidar takardun bayan da Mimi tayi mu ka shigar da qara da saka hannunta da komai ya sunkuya yana 'dauko jakarsa 



Kallonta Hayat ya keyi yadda bayan tashi da hankalinta yayi har tsigar jikinta na tashi ta na hawaye tana girgiza kai ya cire hannunsa daga kawunansa yana takawa har gabanta duk kallo ya koma kansu 



Cikin idanunta ya ke kallo ya furta "Wasa dama kike yi da ni"? 




Ta saki kuka tana girgiza kai ya 'dago fuskarta yana shigar da idanunsa cikin na ta idanunsa har da qwalla ya furta "kun shirya komai tun farko"? 



Kuka ta qara saki sosai ta riqo hannunsa ya qwace yana matsawa qara binsa tayi sam ta kasa furta ko kalma 




Duk kotun hatta da lauyan baban shima kallonsu kowa ke yi hawaye ya fara yana furta 



*why Ni*? durqusawa tayi tana kuka ta riqe kafafunsa duk yadda ta so tayi magana ta kasa kama kansa yayi yana tatiyo voice *ya kamani yayi abinda zaiyi da ni* 



A hankali ya furta *gara na fuskanci ko wani irin qasqanci a rayuwa a kan  in Zalinceki gara na hakur*....


cikin firgici har jikinta na rawa ta taso tana riqo hannunsa kada ya qarasa kalmar ya fisge hannunsa ..

💖AQIDARMU💖






PART2 


No comments