Breaking News

AQIDARMU Book 2 Page 10

 


🅿️1️⃣0️⃣









A hankali ta miqi jikinta har yana rawa ta shige word 'din ba tare da sanin ma su mummy na gurin ba hakan yasa suma suka koma zuwa wani farfajiyar 'yen jinya masu raino na nesa da su da yara a yayinda Najwa ta kalli mummy ta fara magana





Yasmin 18yrs kenan da gaba 'dayanmu mu ka gane Hayat ya bar AQIDARMU saidai mu ka 'dauka quriciya ce shiasa sannan mu kace zamu saka idanu a kanki mu gano ko kinada hannu a ciki saidai ga mamakinmu kema baki san ya bar AQIDARMU ba kuma baki kula da sam baya yadda yin magana sallah et gabanki sai in ta qure shi ya sai yayi tamu a gabanki in kika tafi ya sake tasa 




A shekaru 7 in baki manta ba Hayat yace zaije wani course à Miami à gidanki na can baki ta'ba bincikawa ba domin kuwa hutu de ya ke zuwa yi a Miami amma ainihi yana makka ne yana karatu a *UMMUL-KHURAH* inda manyan malaman sunna musamman na ku nanan Nigeria su kayi karatu kamar su *Sheikh Mahmud Abubakar Gumi* da sauransu  ban gama mamaki ba sai da na shiga makka da kaina nayi bincike na gano Hayat yayi Degree a kan tarihin musulinci mummy ta 'dago tana kallon Najwa murmushi tayi ta ta bu'de wayarta ta shiga ta kunnawa mummy videon graduation 'din hayat inda ya fito da F/class Najwa taci gaba 





Wlh duk zuri'armu ta *Thariq Ahnan* babu wanda mai kishin zumunci kamar hayat hatta da yaran da na haifa cikina mummy ta share qwalla najwa taci gaba




Bayan na gama duk bincikena na gano Hayat baya ya gane gaskiya ya kuma fi kowa sanin ba hanyar daidai mu ke tu ba saidai ya jadaddawa kansa mu ahalinsa ne mu dolensa ne don haka ba gudunmu zaiyi ba taimaka mana zaiyi mu dawo kan hanya a shekaru uku da suka wuce muka nemeshi a kan hakkinsa da kakansa ya jaddada mana cewa da zarar yayi 30yrs mu maida masa amma Hayat yace mana idan mu da muke danginsa bamu anfani dukiyarsa muna juyawa ba waya da zai anfa a lokacin ne ya mayar da komai na wannan shiya asusun Family inda yace har jikoki sai da dukiyarsa ta gadon babansa da mamansa na kamfani da kuma gadon da babanmu et ya raba musu su duka dayaranmu wadda Zainab ta bamu wasiyya ni da ke cewa kada mu bashi har sai in yanada iyali wanda da nayi bincike na gano kin ha'da aurensa ne da Farida domin ya ansa na Zainab ya bar Iran a tsammanin ki in yabar zai bar AQIDARMU ke bakima san yariga ya bari yana ba 





Najwa ta kalli mummy ta ce Hayat dukkanmu muna kaunarsa ne sabida daga shi har babansa sun kasance masu kaunar zumunci basu ha'damu da kowa hakan yasa babu wani 'dayanmu ko yaranmu da ke bakin ciki ko hassadar 'daukakar da Hayat ke samu à kullum cikin rayuwarsa yana aiki da gomnati babu irin 'daukaka da baya samu yanzu haka gomnatin na shirin bashi mukamin (Ministan mai n'a qasa dukda wasu sunso qin haka a majalisa sakamakon alaqanta hakan da su kayi da qaracin shekarunsa amma ni da 'yen uwana mu ka tabbatar basu yi nasara domin a yanzu haka bacin Hayat na kwance gurin nan da yanzu yana kan sabon mukaminsa ne na "minista of oil and gaz na Iran" Yasmin wlh tunda na ke ban ta'ba ganin ko da makamanciyar soyayyar Hayat da farida ba 




A farko da kika kawo ta nafi kowa tsanarta domin girman kanta da rashin son kala mutane ko ranar da naje mata da fayel na mata bayanin et tanada 5%100 cikin kamfanoninmu wannan kyawta ne da tun kafin Hayat mahaifinmu ya rasu ya tsara yinsa a duk sadda a kayi wata suruka mace a auri'armu amma Farida sa'banin dukkan surukanmu bata nuna kwa'dayi da zalama ba hakan ya fara sani tunani a kanta



Yasmin Farida ce ta fara sani yiwa kaina wasu tanbayoyi "shin a farko batasan AQIDARMU ba ta  auri Hayat amma ko da ta iso tasan AQIDARMU bai ta hanata ci gaba da kaunarsa tare da son kasancewa tare da shi ya ba qaramar yarinya amma ta nuna komai yana hannun Allah domin a bawai a lokacin ma AQIDARMU baya damunta  tafi kowa damuwa saidai son da takewa Hayat ta bari ya rinjayeta hakan yasa ta kalli yuwuwar ta sanjashi zuwa hanya madaidaiciya




Na tabbata idan da dayawa suka ga waninsu dangi ko masoyi ko miji cikin AQIDARMU da farko zasu mayar da hankali ne wajen jawo hankalinsa da yi a masa nasiha da addu'a bawai kyama da kyara ba da wuya a wannan zamanin a samu mace mai soyayya domin Allah kamar Mimi hakan yasa har danginta na shiga bincike a kansu




Kallonta mummy tayi ta girgizata kai kwarai kuma na gano dayawan abubuwa daga kan shi babanta et har Wasu daga 'yen uwanta saidai yanzu muci abinci et ni yunwa na keji zan qarasa baki labari dalla2 zuwa gobe de IA 



Ajiyar zuciya mummy tayi tace shikenan..





Tana shiga word 'din gadon ta nufa ta 'dora kanta irjinsa tana hawaye kafin ta 'dago tana tana kallonsa ta furta *pls mine kamin haka sau dayawa pls last tym kai kamin promis bazaka sake tafiya ka barni ba ka taimakamn ka tashi haka don Allah ta saki kuka tana mayar da kanta irjinsa 




Kallon Mama Safwan yayi yace bana fahimtar kamar yaya Shi sojan zata aura? Ajiyar zuciya mama tayi ta kalleshi tace sabida shine mafitarmu a kwana biyun nan ni da siyama mun gano wani sirri wanda Mayar da aurenka da Mimi zai iya fallasawa dole mu hakura sabida ko babu komai burina shine kada dai ta koma gurin wannan hamshakin balaraben 




Idanunsa ne su kayi ja kamar zaiyi kuka yana kallonta ta kunna wayarta  ta saka ta video ta tura qofar masa ya ansa yana kallo cike da mamaki ya 'dagota yana kallonta ta furta yanzu and kaga dalili don haka kabarta ka bi ta layla da ke sonka tuntuni karka manta kafi kowa tsoron fitar sirrin nan kuma nan ka kwana kana ciwo tunda kaji yadda balaraben nan ke saduwa da Mimi haka kake so kaje ka maidata kana tariyo yadda yake saduwa da ita ka bar shi da wancan soja dama gindinsu 'daya da balaraben su qarata nidai burina kada ta koma hannun balaraben shiru yayi yana ci gaba gaba da kallon videon





Su mummy daga can su ka wuce gida abinsu sanin Mimi nanan..




Bayan tayi ishaa ta gama zata cire hijabi wata nurse ta shigo ta miqa mata basket da qaramin akwati tace wai inji mummy "tnx" ta furta nurse ta wuce ita kuma ta zauna a hankali ta bu'de basket 'din domin sai yau taji tanajin yunwa sosai aikuwa farfesun kaza ne da dafaffen arish da plantain dafaffe da soyayyen kwai sai ketchup da tea flacks tea sai anshi and yake da ta bu'de ta tsiyaya ta zuba abinci sosai taci gaba bawai don da'dinsa ba sai domin yau ne ta samu nutsuwa ta gama ta shiga tayi brush ta fito ta bu'de akwatin ta fidda doguwar rigar bacci tasa ta saka hula a hankali ta koma kansa ta zauna gefensa ta bu'de qur'ani qarami da ta gani gefensa ta tabbata na mummy ne ta fara masa karatu har ta fara gyangya'di kafin ta kwanta irjinsa na mintuna ta masa addu'a sosai ta koma kujera ta kwanta saidai ma sam ba baccin ta kaji ba 






Kallonsa baba yayi bayan ya gama sauraron record 'din da yayi na maganar Mimi baba yace shikenan ka Adana gobe alqalin zaije mu ma yaji mai a ke ciki domin and yamin alqawarin biya mana bukatarmu bare yanzu da mu ka samu hanyar kamata ita kanta gobe zaije itama har asibitin ya kai mata takardar tasa hannu 




Salman yace baba Allah ya kawo mana arshen wanna masifa ni and nan da 4dys ya kamata na koma school 



Baba yace kada ka damu gobe tana saka hannu a takardar wahalarmu and ta qare..




*************






Tun 3:am ta tashi ta fara nafilfili har asuba tayi fajr tayi karatu ta miqe taje tayi kissing 'dinsa Sosai ta tsotsi bakinsa har tana shafa fuskarsa kamar ba wanda ke comma ba kafin a hankali ta juya ta shiga ta sake yin wanka ta shirya cikin jar abaya ta bu'de sauran kayan abincinta taci ta sha tea zata zauna nurse ta shigo still da basket hannunta ta miqa mata tayi godiya ko bu'dewa bata yi ba ta ajiye kawai ta zauna sabida ta rigada ta qoshi 





11:22 tana kishingi'de tana gyangya'di a ka shigo ta bu'de idanunta a hankali ganin mutum da shigar suite ta gyara jikinta ta jawo hijabi ta saka ya furta "sorry madam an bani izni sai kawai na shigo" ok tace kawai a hankali yace za kiyi signing ne kawai ok tace ba tare da ta tanbaya daga ina ba sabida haka kawai taji bai kwanta mata ba tanaso yayi maza ya fita ta ya zauna gefenta ya fara bu'de takardu yana 'dora hannunsa sama ya nuna mata daidai inda za tayi signing tayi har ta gama duka ya furta "yanzu" ya fito 





A cikin motarsa a harabar asibitin ya jefa kiran baba ya 'daga ya furta alhamdulillah 




Baba yace kenan yanzu ko ya farka ko kada ya farka tunda tayi signing duka kotu a zata bada sauran sakinta ko.?




Lauyan yayi murmushi yace ai tunda ga signing 'dinta ko wani irin lauya zai 'dauka dole kotu zata bata saki 




Alhamdulillah shima baba ya furta yana murmushi....

💖AQIDARMU💖







PART2





No comments