Breaking News

AQIDARMU Book 1 Page 45-46

 🅿️45/46







Najwa tace inama da a karon farko Hayat zai yadda mu da kanmu mu gabatar a shi ga dangin Zainab dukda na tabbata duk sun sanshi sabida bana manta lokacin rasuwar ta dayawansu sunzo gun Yasmin amma Hayat ya qi yadda ya gansu saidai wata qanwar zainab (Zulai) da ta biyo Hayat yana gidana ranar, sabida a lokacin bana mantawa har Yasmin dayawansu sun daina alaqar komai da ita ganin yadda Yasmin ta yaudaresu tana goyon bayan (Zainab da Mutha) kuma mun ta'ba ha'duwa California da ita Zulai a lokacin Hayat da Yasmin suna Germany hutu ita Zulai tana auren wani Babban soja ne wanda har ya ta'ba riqe muqamin "chief of Army" a yanzu yayi ritaya 



Kallonta Abu'Nawwal yayi yace gaba 'daya zuri'arnan su suka fara kafa tarihin qiyayya a zuciyar Hayat shiasa tun farkon wayaonsa shima ya ginu a kan qiyayyar  dukda Yasmin ce ta raineshi, ajiyar zuciya Abu'Noor yayi yace gaskiya ne shiasa na ke ragawa Yasmin sosai sabida ta kaunaci Mutha wanda ta sadaukar da rayuwarta da ta aurenta da yaranta wajen cika alkawarin yayarta na rainon Hayat dukda itama mijinta 'dan aqidar *IZALA* ne amma bai duba banbancin aqida ba ya barta tana zumunci da 'yer uwarta.. haka su ka ci gaba da tattaunawa a qarshe su ka yanke hukuncin zasu je taron domin taro ne da kowa zai iya zuwa ba lallai 'yen aqidar *IZALA* ba so hakan yasa zasu je taron na karrama surikin Mutha wato *Sheikh Abdullah mainasara* ....





Kallon Mama Taimur yayi yace pls mama kada ki damu zanje "Uncle habib yayi abinda zaiyi Fikhra ce bazan aura ba bcs ni ba yaro ba ne da zasu tasani gaba in auri wace banaso, ajiyar zuciya mama tayi tace naji to amma pls in a ka ha'du kabi kowa a rabu lafiya banason qananun magana kaga dayawa rabona da su tun lokacin bikin Siyam inaji ina gani banje bikin Faisal ba sabida maganar ka Fikhra pls ka kiyaye muje lafiya mu dawo lafiya "ok" yace yana tashi ya bar gidan ta bishi da kallo..




A babban office 'din Ministan ku'di wato "Habib Abdullah mainasara" cike su ke shida wani ya kalli Mininstan yace Yaya da wuya Yasmin tazo ko da waye zai mata magana kana sane itama kamar batason alaqar da mu tun bayan rasuwar Zainab da mijinta Yasmin ko bubukuwan yaran mu bata zuwa kuma ta sani, ajiyar zuciya wani yayi yace wannan wani kundu ne na *Baba* gomnati ke son karramawa ku saka idanu ina tabbatar muku za tazo domin karku manta bata ta'ba yadda baba yayi fushi .ca ita har ya rasu.. toh suka ce suka ci gaba da hirarrakinsu..




Yana Office ne su ke waya da mummy tana masa sannu da zuwa ta furta my boy ka daure kazo mu je tare a karon farko inason na gabatar da kai ga dangi wlh zuwa yanzu su kansu kowa na son ganinka da saninka



"Ajiyar zuciya yayi yace pls mummy 4get dem babu inda zan dawo sai ranar da nayiwa matata alqawarin dawowa sabida a wannan karon ni zan riqa kaita ko wani appointment 'dinta na awon ciki.. salati mummy ta saka ta furta "Hayat wai Farida ke da ciki again"? 'yer dariya yayi ya furta baba mummy meye na ihu haka.? Tayi ajiyar zuciya tace pls kabar yarinyar nan ta huta haka.. dariya yayi ka'dan kafin yace zata huta bayan ta gama gina mana zuri'a ni da ita sabida muma mu kafa namu dangin ta haifi kamar gom.. mummy ta saki salati tace yimin shiru wannan ai mugunta ce yarinya a ce duk shekara tana kan nakuda haba Hayat.. sosai ma yayi dariya yanzu yace my lovely mum karki damu zata huta nan da 3yrs IA but 4now duk shekara zata haihu haka suka ci gaba da firarsu mummy tayi2 amma yace bazaije taron ba kuma a ranar taron shima zai shiga Nigeria Mimi..!




A gajiye ta dawo lecture ta daure ta qarasa salon 'din cikin Barack 'din ta wanke kai tayi kitso sabida yanason kitso a kayi mata lalle yayi kyaw da dilka tayi gyaran jiki sosai domin 25k ta biya just na gyaran jikin sai daf magrib ta qaraso gida gobe ba zata shiga school ba sabida shigowar safe zaiyi tayi gyaran gida komai tayi turaren wuta ta gama duk ta gaji ta zauna ta 'dan kunna kallo saidai hankalinta na kan tariyo maganar sa da yayi a na gobe zai koma *zan warware miki wasu sirruka da suka da'de ina ajiye su no mummy bata san su* ajiyar zuciya tayi tana lumshe idanunta so ta ke ya samu dukkan nisha'di in ya iso dukda yadda ya ke nuna damuwar qanqantar gurin nasu miqewa tayi ta shiga alwala jin an kira magrib ta yi sallah tanada sauran miyar kuka a fridge ta yi tuwo ta 'dumama miyar ta zauna taci sosai ta sha ruwan tafasashen 'bawon abarba a school taji yana wanke dattin mara da sauqaqa nakuda hakan yasa ta mayar da hankali wajen sha sai kusan 9:45 bayan ta 'danyi karatu kafin ta hau gado tunaninsa ya shigo mata ta lumshe idanunta tana furta *I love u so much Mine*  ta kan furta haka ita ka'dai a duk sadda tunaninsa ya fa'do mata ta qara lumshe idanunta wato tana jin tana sonsa daidai da kowani bugun numfashinta da haka har bacci yayi gaba da ita..





**************








Tun asuba da ta tashi sallah ta ke jin irjinta na 'dan bugawa saidai tana basarwa jin cikin dare ma cikinta na ta motsi har wajejen asuba tukuna cikin ya daina motsi tazo kitchen tana gyarawa ta fito da kazar da zata masa anfani da shi ta ajiye zata shiga kasuwa ta 'dan yi cefanen wasu abubuwa da take buqata na girkinsa juyowa tayi zata fito ta 'dauki plate ta saka bread da zata ci da jam ta 'dora cup 'din tv gefe zeta fito taji irjinta ya buga gaba 'daya plate 'din ta saki tana sakin qaqqarfan ajiyar zuciya sakamakon motsin da cikinta yayi da arfi bushewa tayi a gurin tana qoqarin saita numfashinta...




Kallonsu Najwa tayi tace shima gobe zai shiga Nigeria amma fa atubur yaqi bazaije taron ba so shiasa kada kowa ya qara masa maganar in munje bayan taron sai muje in kaiku ramin da suke rayuwa a 'boye shi da matarsa, ajiyar zuciya Mustapha yayi yace "mummy rami kuma"? Tsaki tayi tace kwarai rami domin ko "Dakin (Baqil) yafi gurin girma nesa ba kusa ba" duk kallonta su kayi da mamaki jin tace 'dakin baqil yafi na Su hayat da Mimi girma ta girgiza kai alamar eh haka ne tace kuma zamuje ku gani" sosai ransu ya qara 'baci da baba ace dakin baqil yafi inda hayat ke rayuwa da matarsa (Baqil karen gidansu ne wato thariq Ahnan Mention" da haka suka fice domin a jet 'dinsu zasu je taron...





Yana zaune yana tunani saidai sam baya gajiya da jin zaiyi komai domin ta kasance matarsa ba nan duniya kawai ba yana fata har lahira ta kasance matarsa mafificiya yanajin yana sonta fiye da komai da ya ke dashi kai fiye ma da yaran da ta haifamasa domin yanajin soyayyar tace ya ke sanmusu lumshe idanunsa yayi ya furta *u r d first n last love in my life*  Insha Allah ya qarasa yana miqewa ya bar office 'din zuwa gidansu domin har lokacin yana "Thariq Annan mention" kuma shi ka'dai sai 'yen aiki da securities domin dama babu kowa sai in abu ya faru zuri'ar ke taruwa gidab komawarsa gidan duk kawunansa suka ji da'di sunata qoqarin kada ya canza ra'ayi ya bar gidan ganin ya warke saidai ganin bai bari ba hakan na musu da'di.."




**************





A babban hotel 'din na (International Tourists Hotel da ke Maitama su ka sauka mazan suka kama babban suites mai 'dakuna biyar sai matan Najwa, Ammi'Noor, Ammi'Nawwal, Ammi'Ahlam sai matar Noor, Lubaiyya..  domin Najwa tace sunyi yawa bazasu sauka gun Zenat ba.





Mama, Taimur, Sameerah, Sumayya, Najim duk tuni sun bi jirgi suna abuja suma can gidansu na abuja domin za'a fara taron ne daga abuja zuwa kaduna 






*BIG DAY* 




Cike maqil gurin taron cikar har baki bai iya furtawa 



Zuri'ar *Sheikh Abdullah mainasara" kaf suna gurin 'ya'ya da jikoki banda mutum 'daya cikin jikokinsa inda a kayi musu wani Babban gurin mai kwalliya na alfarma da qawatarwa duk suna gurin yaransa (Habib Abdullah mainasara, Kamalu Abdullah mainasara, Ahmad Abdullah mainasara, Umar Abdullah mainasara, Shuaib Abdullah mainasara, Usman Abdullah mainasara, Sai mata Zulaiha Abdullah mainasara, Bilkisu Abdullah mainasara, Yasmin Abdullah mainasara Rabi'atu Abdullah mainasara.. dukkansu da iyalansu mazan da matan saidai mummy tunda ta zauna gurin bata yiwa ko 'daya daga cikin 'yen uwanta magana ba inda Ma'aruf ya riqo hannunta yana cewa mummy pls ki roqi Ya Hayat ya zo mana ajiyar zuciya tayi tace nayi duk abinda zan iya yaqi zuwa ya kake so nayi..




Minista Habib ya kalli 'dan uwansa Kamal yace gaskiya wannan yaron na Zainab ya gaji kakanninsa kasan 'dan shi'a da baqin rai a ce. Bai sammu ba amma bai ta'ba nema ya sammu ba bayan naji labarin Yasmin tayi masa aure a qasarnan ai ko menene yazo ya ganmu mu ganshi mu san juna kafin kowa ya kama gabansa, ajiyar zuciya Kamal yayi yace kasan irin arzikin da kakansa yake da shi sannan babansa shi yafi kowa arziki cikin yaran kakansa sabida yayi aiki da WOM ta duniya to dole shi bayan jininsu na shi'a Akwai jin izza da isa da takama yanaganin bamuda abinda zai nema gurin mu ajiyar zuciya Habib yayi  yace wannan duk da hannun Yasmin domin duniya ance baya ketare maganarta inda ta nuna masa darajarmu da komai lalacewarmu da sa'banin da muka samu da uwarsa da 'yer uwarmu ce zai neme mu domin babu ruwansa da abinda ya ha'da mu da uwarsa mu kawunansa ne kamar yadda yake bawa 'yen uwan ubansa hakkinsu dole ne muma ya bamu domin na ka ko kafiri ne Allah yace kayi zumunci da shi,, tsura masa idanu Alhaji kamal yayi sai kuma ya ha'diye maganar sa su kayi shiru kowanne da abinda ya ke saqawa zuciyarsa inda Habib ke saqa danasanin gaba da 'yer uwarsa har ta rasu ga 'dan ta ya girma basu sanshi ba, inda shima kamal danasanin ce fal cikinsa na meyasa basu kar'bi qaddara ba suka yanke dukkan alaqa da ,yer uwarsu har ta rasu ko gawarta basu gani ba ajiyar zuciya yayi ya kalli Minista Habib yace bayan angama taron nan zamu bi Yasmin gida gaba 'dayanmu a yau mu tilastata kaimu gurin Yaron (Zainab) murmushi Habib yayi yace wannan shawara mai kyaw ce domin muna gidan ta kiransa kawai za tayi yabi jirgi yazo ko in yanaso mu mubi jirgin  mu je..




Ya fito gidan Sanye da shirt hash da bakin dogon wando da bakin takalmi sai silver wacth 'Dinsa yayi kyaw har fa'da ma 'bata baki yana gyara amwatinsa kiranta ya shigo ya kalla yayi murmushi ya tsinke ya jefa mata video call 



Wani irin numfashi ta sauke ganinsa ta lumshe idanunta ta ma kasa magana ya masifar tafiya da imaninta kamar bata riga ta mallakeshi ba ganin ta qi magana ya furta "My queen" har tsigar jikinta sai da ta tashi ganayin da ya kirata kallonta ya shiga yi ganin daga ita sai 'yer tawul za ta shiga wanka ajiyar zuciya ya sauke ya cikin mufyarsa da ta gama nutsewa ya furta "Baby za ki 'batamin wanka in ina kallonki haka" numfashi itama ta sauke tana kallonsa ta furta *Mine I love u* lumshe Idanunsa yayi yana kallonta kusan 1mnts kafin ya kai hannunsa bakinta yana shafawa kamar tana gabansa ya furta *love more baby* suka saki ajiyar zuciya tare agogonsa ya kalla ya juya yana shigar da idanunsa cikin na ta kamar tana gabansa ya  furta baby let me come to u at d ryt tym  bcs *I really miss u*  ajiyar zuciya tayi kafin ta furta *miss u too* yayi 'dan murmushi ya shafa fuskarta ya qara furta *I love u* itama ta qara furta  * me too* suna kallon juna kusan 4mnts ba magana kafin ya kai hannunsa ya kashe wayar yana ajiyar zuciya kusan 5mnts ya qara a zaune kafin ya miqe ya fito zuwa airport 





Sosai gurin taron ya ke ta qara cika anata gabatar da manyan baqi wanda yawanci qusoshin gomnatine da attajirai da sauransu sai commeetee kala2 na masallatai musamman na 'yen aqidar sunna daga ciki kuwa har da 'yen commetteen masallacin su Baba da ya taho shima da iyalansa su goggo da su mami duka kuma shi commeeteen masallacinsa suka saka ya jagoranci qungiyarsu and a taron inda hakan kamar wani buri ne da baba ke dashi na son shahara a kan Aqidarsa ta *SUNNA" wato *IZALA*  



Taimur na gurin saidai gaba 'daya imaninsa na kan tunaninta da begenta har yana jin yadda zuciyarsa ke ansa masa sonta da kaunarta ..




Tsaf ta gama shirinta wata shegiyar rigar less ja ta saka ta masifar matseta haka ta saya a jiya a Borno fashion Calabar 'yer hula ce ta yadin satin a ke ha'dawa da rigar ta jefa dogon hijabj ta fito ta tayar da mota ta nufi airport saidai haka kawai taji irjinta na 'dan harbawa da sauri kuma tun asuba ta ke ta jin haka saidai ta danganta hakan da rashin isashen bacci kuma Dr na cewa mace mai ciki in bata samun hutu irjinta kan yawan bugawa da arfi 




Sai yanzu a ka fara taron inda a ka fara gabatar da sunayen iyalan marigayin cikin tsananin mamaki su mami suka kalli juna bayan jin an kira *Yasmin Abdullah mainasara* mummy ta fito shi kansa baba mutuwar zaune yayi cike da mamaki har gumi ya fara 




Yana fitowa jirgin ya hango motar ya nufi bu'dewa kawai yayi ya shiga 




Wani irin harbawa irjinta ke yi tana driving saura ka'dan ma tayi accident ta tsaya ta kama irjinta tana ta kiran sunan Allah kusan 10mnts kafin ta tayar da motar tana shiga airport 'din ta faka motar ta fito kamar a na wadda tasha giya ta fara layi kanta ke wani irin sarawa daf da gurin motar ta kama da wuta alamar bom *BOMM* tsayuwa tayi kamar zautacciya mutane duk suka bushe a na kallon motar a hankali ba tare da sanin mai ya ke faruwa ba ta fara taku cikin mugun firgici in ka ganta zaka 'dauka kisa tayi a ka kamata idanunta sun fito har gurin da motar ke ci da wuta mutane na shaqe a gurin sunata maganganu itama tsayuwa ta yi sam taji ta manta abinda tazo yi a airport 'din




Motar police ce ta iso da ta 'yen kwana2 take suka fara kashe wutar saidai ina is late haka wani yace zo is gani sun gama qonewa inda suka matsa gurin su ka fara dube2 



Mimi da jin haka itama ta 'dan matsa jikinta na rawa ta fara kiran layinsa na Nigeria off ta qara jefawa 


can nesa sosai wani police ya hango wallet ya bu'de ya gani ya juyo yana qarasowa 



Kamar cikin mafarki taji yana cewa daga cikin mamatan akwai *HAHAT MUTHALLIB AHNAN* wani irin zamewa wayarta yayi daga hannunta ta juyo a gigice ta qarasa ta fisge Wallet 'din hannunsa tana kallo su kaga ta zame ta fa'di da sauri suka qarasa suna ta'bata sam babu numfashi jikinta suka fara kallon juna da tanbayoyi inda a ka 'dauketa zuwa asibiti kafin a ka cigaba da duba wallet 'din suka ka ga wani qaramin kati da sunan Yasmin Abdullah mainasara da information na komai na butik 'dinta da layukan wayarta nan suka shiga kira





Duk sunaq cike gaban manbarin inda zasu fara gabatar da tarihin mahaifinsu jama' a duk sun tara hankali kansu cikin mutanen kuwa har da *THARIQ AHNAN FAMILY*  wayar mummy ta fara ringing ta basar ta miqa ba tare da ta kalli wayar ba ashe yayanta minista ta miqawa ya kalli wayar ganin number police ce ta qasa sannan reshen Calabar ya kalleta kafin ya ,daga wayar, 



Sannu sir munason magana da hajiya Yasmin, ok yace lafiya,? Da ke police ne babu sirri nan suka masa bayanin abinda ke faruwa cikin mugun tashin hankali shima ya saki wayar yana kallon mummy har ta kalleshi itama ganin yanayinsa ta yi shiru daga bayanin da take ta qura masa idanu hannunsa hakan ya jawo hankalin jama'a a ka fara tanbayar abinda ke faruwa inda Habib ya aro jarumta ta namiji ya miqe ya ansa lasipika ya fara magana daga danginsu har jama'ar gurin duk su ka tara hankali kansa domin da alama muhimmin abu zai sanar




Numfashi ya sauke mai nauyi ya fara furta *innalillahi wa'inna ilayhi raji'un x3 kafin ya furta* 



Jama'a a gafarcemu nan zamu tsayar da wannan taro sakamakon babban rashi da ya tunkari zuri'army a yanzu wato jikan mahaifinmu wato *HAYAT MUTHALLIB* wani wawan zabura mummy tayi ta isa gabansa ya kalleta kafin yaci gaba "Ya samu hatsari ne yanzu da shigowarsa Nigeria inda motarsa ta qone qurmus"



Zuuuuu mummy tayi sukaga ta fa'di su kayi kanta mutane kuma a ka shiga salati, inda *Ahnan Family* kuma suka bushe kamar an shuka su kafin cikin mugun gigicewa Abu'Noor ya furta (Wlh tallahi ba zamu yadda ba) duk sai yanzu suka dawo hankalinsu wani mugun hawaye ne Najwa ta fara mara tsayuwa ta furta "shi ya kasheshi"  Abu'Ahlam kuwa ya yanke jiki shima ya fa'di duk su kayi kansa 




Salati goggo Jummai ke yi tana kallon dada tace kamar sunan mijin mimi kenan ko.? Hawaye Dada ta saki idanunta na kan baba ta qura masa ido tabbas aurenta da shi ya qare a yau, a yayinda mami ma tana hawaye ta furta sai da suka ga bayansa.. tabbas *BINTA DA SAFWAN* abin zargi ne 




Najim ne ya kalli mama yace mama wa ye shi mai rasuwan.? Cikin hawaye ta furta baku sanshi ba yaron yayata Zainab da kuke gani a hotunana na quriciya wacce na ke baku labarin munfi shakuwa sabida tsakaninmu babu nisa kuma bayan rasuwar innarsu baba ya dawo da ita gun innata shiasa mu ka tashi kamar tagwaye  " Sameera tace to mama mai yasa bamu sanshi ba hasali ma bamu ta'ba ganinsa ba? Ajiyar zuciya tayi ta kallesu duka Taimur da shima sosai alamomi suka nuna ya shiga tashin hankali ta furta ku bari bayan angama makominsa mun koma gida zan baku labarin komai 




Tsayuwa Mudassir yaron baba da ke karatu Sudan yayi ya dafa baba ya furta baba mu je an watse cikin mugun gigicewa baba ya 'dago yana kallonsa ya furta mudassir ya sunan yaron da a kace ya rasun.? Mudassir yace wai jikan sheikh.? Baba ya girgiza kai kamar qadangare mudassir yace (HAYAT) kama kai baba yayi ya shiga kiran sunan Allah..









Nan na kawo arshen *AQIDARMU* kashi na 'daya..!






Ga mai son karanta *AQIDARMU* kashi na biyu ya tuntu'bi wannan no 09067895777 




Godiya sosai mai tarin yawa ga fans 'din *AQIDARMU* qwarin gwiwarsu ce ta bani dama ci gaba Allah ya saka da alkairi 💖AQIDARMU💖 



Salaam.  




Ina masu bin littafin *AQIDARMU*  part1 ga mai bukatan *AQIDARMU* part2 ya tuntubemu ta wannan no 'din 




08141545851 

09067895777



Kati ne za ki/ka turo na #200 Mtn ko airtel a na iya turowa domin mallakar *AQIDARMU* ga masu yin VTU zasu turo S/short na shaidar sun tura katin.!



 sannan pls a kiyaye amana kowa ya saya da kansa maimakon sharing hakan ya sa'bawa amana da hakkin 'dan adam wannan littafi hakkin marubuciya ne don haka a kiyaye pls ina godiya mai tarin yawa mara iyaka a gare ku tare da neman afuwar duk wanda kalamaina su ka 'bata masa. 




Marifanta A.D Nagode




Sannan dubun godiya ga *@FATIMATOU* a kan dubun qoqarinta a kan wannan littafi na *AQIDARMU* Allah ya saka ya bar zumunci Allah ya biya miki bukagunki na alkairi duniya da lahira Nagode 



Marubuciya Marifanta A.D Nagode!

Created by itz B.M.B

DUNIYAR MARUBUTA ADMI NUM 07046396992

An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya


Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,


Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490


A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, 


Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu


Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC 


Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku

No comments