Breaking News

AQIDARMU Book 1 Page 43-44

 🅿️43/44







A can 'din ma zaune ya kwana zuciyarsa na tafasa.. 





A babban hall 'din makaratar ta Gwagwalada Dr Mas'ud ya kalli 'daliban wanda ke shirin graduation nan da sati biyu masu zuwa ya fara magana...




Da farko muna muku fatan alkairi da nasara da cigaba na wannan kammala karatun na ku sai na biyu kamar yadda kuka kasance 'daliban da su kayi karatu a kan ilmin musulunci wato *Islamic studies* muna muku fatan anfani da abinda kuka karanta kamar yadda 'daukacinku suka samu maki mai kyaw su keson koyi da manyan magabatanmu na musulunci daga farko har zuwa yanzu sannan a qasarmu su ke son koyi da manyan malaman mu fittatu kamar su (Sheikh Sufyan Ali, sheikh Ahlan Sammani, sheikh Thaiban Manaf, a qarshe sai shahararren malaminmu na babbar AQIDARMU da ya shahara a wannan gari da ta mu ta Kaduna da ma Nigeria baki 'daya *Sheikh Abdullah Mainasara* nan 'dalibai suka shiga tafi suna Allah ya masa rahama kusan 10mnts suna hayaniya kafin ya dakatar da su yace *Sheikh Abdullah mainasara* mutum ne wanda ya bar tarihi na har abada qasarnan ma yayi aiki tukuru wajen kafa wannan qasa ta hanhar musulinci gidajen jaridu dayawa sun saka tarihinsa a kan shafinsu na manyan magabata kamar yadda 'daukacinku ke rubuta project a kan tarihinsa






Ya kasance mutum haziki  jarumi a kan komai musamman a kan maqiya *AQIDARMU* jibi ne gomanatin tarayya ta shirya taron (launches book) 'dinsa a bababn gidan tarihin abuja inda za'a shigar da tarihinsa a kundun gidan tarihi na (Arewa House) da ke nan kaduna hakan yasa mu ma mu ka nemi alfarmar a bamu katin gayyata domin zuwa taron wannan babban jarumi kuma haziki na *AQIDARMU* Allah ya masa rahama sannan mu na so zamu gabatar da wata babbar kyawta zuwa ga zuri'arsa 'ya'ya da jikoki duk 'daliban suka ansa da hakan yayi malam a fa'da mana ko meye zamu bayar " murmushi yayi yace wannan sai anjuma bayan mungama meeting na department Malama Shamsiya zata zo ta sanar muku abinda mu ka yanke da haka a kayi addu'a a ka watse..




Baba na falonsa ya shagala wajen kallon labaran da AIT ke nunawa inda suka fara gabatar da bayanin taron da za'ayi daga Abuja har kaduna na girmama marigayin malamin wato *Sheikh Abdullah mainasara* wanda sannanne ne gun kowa har gun wanda ba 'yen aqidarsa ba hakan ya sa baba shima ya 'dauki wayarsa ya jefa kira a ka 'daga ya ce committee tayi maganar zuwa taron ne.? A ka ansa eh ai dole ne dukda wai taron ma yazo da tsaro domin gomnati tace sai ta zauna da iyalan marigayin kafin ta yanke hukuncin makamar lokacin taron kasan wai gomnati na son ganin duk zuri'arsa gurin taron sabida akwai karramawar sirri da gomnatin ta ware musu dukda yawancin yaransa da jikokinsa duk masu arziki ne daga matan har mazan sannan yanada jikoki dayawa qasashen waje shiasa a ke tunanin gomnati zata 'daga taron zuwa arshen sati domin tabbatar da duk zuri'arsa sunzo taron






Ajiyar zuciya baba yayi yace haka ne Allah ya kaimu nima gobe zan shigo masallaci inji yadda tafiyar zata kasance domin banason tsallake komai na tafiyar "ok" yace Allah ya kaimu su kayi sallama baba ya fa'da tunani na yadda *Sheikh Abdullah mainasara* ya shahara kan aqidarsa shima haka ya ke burin tsayuwa kansa dukda shi gashi Mimi tanason 'bata masa tarihinsa da na aqidarsa amma bazan ta'ba bari haka ya ta kasance ba domin koyi da manyan malamai kamar wannan da basu fuskanci matsala da damuwa da iyalansu ba kamar yadda kuka ni yanzu na ke fuskanta da Mimi..





A hankali ta ke juyawa tana hamma ta ganshi zaune yana kallonta kamar cikin mafarki ta mutsutske idanunta tana kallonsa a hankali ta yaye mayafin tana saukowa qaramin gadon inci 12 ta je kan kujerar da ya ke zaune a hankali ta zame hannunsa ta zauna cinyarsa tana 'dora hannunta kan wuyansa ta na kallonsa ajiyar zuciya yayi yana sunkwi da kai ya furta "u need rest u kno ko"? 'Bata fuska tayi kafin cikin yanayin shagwa'ba tace wani rest zanyi bayan zuciyata na zaune kallonta yayi ta riqo fuskarsa tana kallonsa ta furta "ka ta'ba ganin gangar jikin da take bacci zuciyarta bata bacci.? Lumshe idanunsa yayi yana shigar da yatsunsa cikin na ta ya furta "baby soyayyarki ce ke bani qwarin gwiwar da nake rayuwa a yanzu" 'dora kanta tayi kan cikinta nasa tana lumshe idanunta ta furta "nasan damuwar ka and ko bola kakeson mu rayu I will the most happier woman in dis world bcs is u my world.. 'dagota yayi yana kallonta ba ka'dan ba yadda take nuna masa so da kulawa  ke qara mata daraja a idanunsa kulkum musamman yadda bata gajiya da bayyana masa matsayinsa a zuciyarta da rayuwarta domin ya sani yayi 'yen mata dayawa wanda bawai basu sonsa ba ah ah sosai ma suke nuna masa soyayya saidai su nasu ha'de da kwa'dayin martabar danginsa da kuma shi kansa suyi ta bibiyar 'yen uwansa hakan yasa a lokacin indai yana tare da yarinya sai yanacin gindinta inda a qarshe ya fara wulaqantata bayan ya gama saba mata da cin bura in taje gun wasu mazan kuma ya mata korar kare yace bazai auri mara kamun kai ba..itama kallon na sa take a hankali u furta "u r d best" murmushi ta masa tana miqewa da kyar jin mararta ya qulle yayi maza ya riqeta yana tanbayarta tayi murmushi ya 'dauketa ya kwantar shima ya koma ya rungumeta su ka koma baccinsu..



************





Daddy ne ya kalli mama da Taimur da Najim yace ke Zulai ya kamata ki yiwa 'yer uwarki magana ku san yadda zaku tsara taron nan ta 'bangareku mata domin zuwa yanzu ya kamata kuna manta abinda ya wuce ko sabida yara rannan Mijinta ke fa'damin ta dawo Miami jinyar bayanta yacemin tun matsalar da ta samu lokacin twins har yanzu tana fama Da bayan "shiru tunda ya fara magana ba tace komai ba har ya gama ya ce ni gobe zan shiga abujar maganar Najim so zamu tsaya gaba 'daya mu jiraki ok kawai tace suka je cin abinci bcs Summy na sama..






Da safe batada lecture yasa tasha wanka da Doguwar rigar atamfa su shima sanye da dark blue na shadda gezna daidai jikinsa 'dinkin zamani sunsha kyaw ita cikinta ya 'dan fara nunawa yanzun ka'dan ya riqo hannunta su ka fito ga mamakinta mota ce sabuwa dal (BMW 922) kallon sa tayi da alamar tanbaya ya miqa mata key ta kalli key 'din baice qala ba ya riqo hannunta har gaban motar ya kaita bayan motar tana kallon plak 'din da no ba sannan da sunansu da a ka ha'da (Fayat) wani irin hawaye ne ya zo mata ta kasa ha'diye shi tayi maza ta rungume shi a tsakar wajen shima qanqameta yayi ta fara kuka ta furta baby is too much ka bari haka pls"  'dagota yayi yana kallonta ya furta "Ni kaina I belong to u bare abinda na mallaka"  qara rungume shi tayi dama ta koyi tuqi a Iran a school don haka ya shiga gefen ta ta shiga ta tayar sam rayuwarsu su keyi ba shakkar kowa saidai shi Hayat kamar da gayya ya ke a lot tinks a yanzu..






Ajiyar zuciya yayi ya kashe wayarsa yana huci kafin ya ci gaba da ayyunkansa na office..!





Dare su ka dawo gida sunsha yawo ko da su ka dawo wanka kawai su kayi ya ha'da musu coffee su kasha tasha drugs 'dinta su ka kwanta saidai shi cikin dare ya farka yanata ayyuka a nasa system ganin ta fara motsi yayi maza ya kulle ya koma ya rungumota ta saki ajiyar zuciya tana qara shiga jikinsa..!





Har airport ta kaishi a karon farko sannan ya riqo hannunta suna kallon juna ya furta "take care of yana shafa mararta lumshe idanunta tayi ta qara kallonsa suka runguma sun da'de kafin ya mata peck a goshi ya wuce bai juyo ba tanata hawaye har ya 'bace kan ta juya ta fita airport 'din tana tuqi tana hawaye har ta kai Barack tana parking shima Taimur yana parking a hankali ta fito ta qarasa ta gaisheshi duk ta 'dan hargitse ya ganta da mota maj zai fa'dawa iyayensa dukda Hayat yace mata kada ta damu ba ma zasu ta'ba tanbayar ta ba murmushi yayi ganin gane halin da take ciki ya furta gobe ance kunada test ko.? Eh tace ya ce after test 'din "mari zata rakaki ki 'danyi wani practice a labour room 'dinsu ok tace tnx yayi murmushi ya wuce itama ta shiga nata gurin cike da tanbayoyi na yadda Taimur ke yi sam baka gane ina ya dosa ta basar taci gaba da ayyukanta na gida...




AIT ta sanar da ,daga taron zuwa sabon sati mai kamawa domin tanaso gaba 'daya zuri'ar Sheikh Abdullah mainasara suzo don haka a gari ma an fara sayarda pass na shiga taron mutane na ta rububin saya musamman 'dalibai daga dukkan 'bangare na Nigeria har ma da wasu qasashen qetare kamar kamaru, Niger, Ghana, baba ma ya saya pass har ya sayawa su goggo da dada da mami duk zasu je..





kallon Abu'Noor Najwa tayi tace ni fa inason zuwa taron ko don na ga wa'dan nan yayyun Zainab da suka riqa cin mutuncin Mutha.. ajiyar zuciya abu'Ahlam yayi yace ni kaina inason zuwa domin ganin iya inda suka tsaya da qiyayyarsu zuwa yanzu ga dai Hayat ya girma dukda basu ta'ba neman ganinsa ba kai mugaye ne mutanen nan sun iya nuna qiyayya irin wacce suka nunawa mutha ne Hayat ke gani daga wasu yanzu Noor ne da Amal da Mustapha yaron Najma suka shigo Mustapha yace muma gaskiya muna son zuwa Abu'noor yace duk ku shirya a jet 'dinmu za muje IA

💖AQIDARMU💖


          Na 



Boyayyiyar marubuciya


No comments