Breaking News

AQIDARMU Book 1 Page 37-38

 37/38






Cikin firgici Alqalin yayi kansa ya 'dauki ruwa ya yayyafa masa  ya saki qaqqarfan ajiyar zuciya yana bu'de idanunsa har ya gama bu'desu alqalin ya furta "Sannu alhaji ajiyar zuciya ya qara saki ya miqe alqalin ya taimaka masa inda ya da'de kafin alqalin ya furta "babu yadda za muyi sai mu jira ta haifi cik.. Baba ya furta "ta gama haihuwa da wannan 'dan shi'an kallonsa alqalin yayi yace to ya za'ayi da cikin.? Baba ya furzar da iska mai zafi ya furta zai fita dole zaro idanu alqalin yayi yace nasan abin kwai tashin hankali amma alhaji karmu bari muyi abinda musulunci zai tuhume mu baba ya miqe ya kalleshi ya furta ba wata uku bane cikin.? Kallonsa alqalin yayi baba yaci gaba zan 'dauki matakin arshe a kan wannan 'dan mummunar aqidar domin bazan ta'ba bari ya 'bata suna da darajar AQIDARMU da kowa ke girmamawa ba ya fita ko da ya fito su goggo su kaga yanayinsa wani iri babu wanda ya tanbayeshi mai ya faru ya wuce su ka bi bayansa...





Murmushi yayi ya furta mummy I so much miss u ta saki dariya tace bayan yanzu bakada damuwa da ya wuce (Farida) duk soyayyar ka ka tara kanta dariyar ya qara saki yana qara jawo system 'dinsa kamar yana gabanta ya furta mummy u kno ba haka bane is just I love her yadda har kaina na kan manta in tunata dariya ta yi sosai tace (Hayat Allah ya shirye ka) dariya yayi ya furta amin my lovely mum ta kalleshi ta furta now tell me mai kuke ciki.? Shiru yayi yanayinsa ya canza ya furta mummy bazan iya cewa komai ba ki bari kan ki dawo zan shigo Miami kiji komai "Ok" yace ki gaida Ma'aruf ok tace ta furta pls my boy ka riqa kula da kanka kaji.? Lumshe idanu yayi yace IA mummy su kayi sallama ya kashe video call 'din ya fa'da tunani





Yau kwana goda sha shida baba ya gama yanke hukuncin fidda cikin mimi ganin saura kwanaki cikin ya cika wata hu'du gara yayi maza a cire ba tare da kowa ma ya sani ba tunda cikin bai kai ya bayyana kansa ba kuma cire wannan cikin baba ya  jaddadawa kansa cewa jihadi ne domin kashe 'yen AQIDAR iyayen cikin jihadi ne da wannan shawarar da zuciyarsa ta bashi ya qara samun arfin gwiwa inda ya yanke hukuncin shiga Calabar gurin wani abokinsa bayarabe kiran alqalin yayi ya masa bayani shima alqalin yayi na'am inda yace gaskiya ne wataqil ma iyayensa ne suka shirya ya tasa 'yerka gaba domin 'batawa AQIDARMU suna a idanun duniya ya fake da aurenta ya ke ta yaudararta baba yayi ajiyar zuciya yace gobe zamu wuce Calabar 'din tare can zan barta domin shi tsohon soja ne general kuma gidansa kwai tsaro sosai ga camera ko ta ina sannan tun yana aiki ya shiga AQIDARMU ok alqalin yace hakan yayi sosai kada suma mata su kawo mana wata matsalar idan suka san halin da a ke ciki haka dai suka ta tattaunawa kan batun arshe su kayi sallama baba ya saka a kayi musu bucking na flyt shi da mimi zuwa calabar ko da su dada su ka tanbayeshi ce musu yayi a kan maganar qoqolwarta ne a ka bashi labarin wani likitan qoqolwa duk su kace Allah ya bada sa'a goggo na goge da Muthallib da ke ta rigima Salman kuma na hannun mami tana bashi madara sai muhammad yana bacci falon dada 




7:22 am Su goggo su ka raka mimi da baba airport tun cikin motar mimi ta kwararawa mami amai sosai harda kore2 a jiki sakamakon warin petur duk su ka tsura mata idanu a qarshe dai haka a kayi parking hanya ta goggo hanne ta wanke mata jiki ta fito mata da wata riga suka shiga wani gida ta canza kayanta zuwa riga bubu na material a ka fiddo mata cikin akwatinta goggo jummai da goggo hanne sai yanzu suka qare mata kallo cikin fargaba goggo hanne ta kalli goggo jummai tace yarinyarnan anya ba ciki ne da ita ba.? Goggo jummai tace ni tun sati uku da suka wuce na fara zargin haka zasu qara magana dada ta shigo tace ku fito malam yanata fa'da suka fito jiki duk a sanyaye suna qara qarewa mimi kallo




Suna shiga driver ya tayar su kam su goggo duk bakinsu ya gama mutuwa har mimi da baba su ka wuce basu qara magana ba ko a mota har su ka iso gida suka shiga 'dakinsu goggo jummai ta kalli hanne goggo hanne tace wlh ciki ne sabida ko shekaran jiya da a ke suyar kifi guduwa tayi can 'dakin dada har yamma bata fito ba sannan ina lura bataci abincin ba ajiyar zuciya goggo hanne tayi tace in yaya ya gano Allah ka'dai yasan mai zai faru a wannan karon domin ina kula da shi ya gama kaiwa bango kan lamarin, shiru goggo jummai tayi kafin ta furta "to ma tayaya suke ha'duwa suna saduwa.? Da duk irin tsaron da yaya ya saka mata, tsaki goggo hanne tayi tace karki manta mai ku'dine babu abinda zai gagareshi sannan yaya wlh yanzu laifin yaya ne tayaya duk kunyar mimi karki manta ranar da Safwan ya santa budurwa mu kaje jinyarta 'boyewa tayi 'daki ta kulle kanta amma yau an wayi gari ta kasa 'boye masifar so da jarabar balaraben nan da takeyi nan ko cikin bacci saduwa su keyi don Allah duk wannan bai isa yaya ya hakura ya kyalesu ba.?  Ajiyar zuciya goggo jummai tayi tace bayan ma wannan ki duba irin girman rabon da ke tsakaninsu wata goma sha 'daya tayi hannun Safwan bata ta'ba ko 'batan wata ba amma gashi nan da ta haihu da ya maida, shiru duk su kayi a qarshe su ka furta Allah ya kawo arshen wannan al'amari ya tabbatar da abinda yafi alkairi ga su yaran da mu baki 'daya...




Babban gida ne na duniya palace an narka dukiya iya dukiya a securities ko ina motoci sun kai ashirin a gidan a wani Babban flat a cikin gidan a ka sauke baba inda Mimi ke can cikin Babban gidan 'bangaren matar gidan wani irin ha'da'dden gidane na duniya mai gidan bayarabe ne inda matar gidan bafulata ce yaransu hu'du maza biyu mata biyu mazan duk suma sojojin ne babban sunansa Taimur sai mai binsa Najim duk suna gari inda tunda Taimur ya kalli mimi ya gigice kuma bai 'boyewa kowa hakan ba daga iyayensa inda babansa ya masa bayanin matsalar da mimi ke ciki da dalilin ma zuwansu inda Taimur yace zaiyi magana da baba babansa yace ok taimur ya je ya nunawa baba buqatar sa a kan mimi shiru baban yayi saidai a take yaji zuciyarsa ta amince da buqatar Taimur don ko babu komai sunada arziki da mukami da 'daurin gindi a qasar so kuma a yadda ya fahimta wanda zai auri mimi ya kamata ya samu wannan qualities domin yaqi da Hayat sai yanzu ya gano lallai ma idanunsa sun rufe ne ya kasa gane sam Safwan bazai iya yaqi da Hayat ba 'dan murmushin manya baba yayi kafin ya kalli Taimur ya furta "zaka iya Fa'da da mijinta kaga shi ba 'dan AQIDARMU ba ne sannan nayi2 ya rabu da ita yaqi murmushi Taimur yayi yace "Baba in har za ka bani ita ina tabbatar maka sai ya rabu da ita.. ajiyar zuciya baba yayi yace "zan baka" murmushi Taimur yayi yace Nagode nan ya fara tanbayar baba a kan Hayat baba na masa bayani kusan 2h suna tattaunawa kafin Taimur ya wuce baba cike da nisha,di yana godewa Allah da ya kawo masa mafita cikin sauqi yanzu zai koma ya kwanta hankali kwance Taimur zai kawo masa arshen Hayat...




Dare sosai 1:24am tana bacci makeken gadon da a ka sauke ta yau a saidai ba bacci ta keyi ba tunanin yanayin baba a yau bayan sun dawo asibiti sai sannu ya keyi mata yana kallonta yana furta komai ya wuce IA ajiyar zuciya ta qara yi tana tuna yadda taga jini jini jikinta alhalin ita ba period ta keyi ba sannan har tura hannunta tayi cikin gindinta babu alamar jini a hankali ta miqe ta jawo jakar magungunan da mai aikin gidan ta rako ta dashi 'dakinta ta fara dubawa vitamines ne da su magungunan hutu da bacci ta hango paper cikin Ledar maganin ta fito da shi ta fara karantawa 



Ki adana drugs 'dinki da kyaw nesa da idanun mutane sannan ki mayar da hankali wajen sha...



Ajiyar zuciya tayi ta fara fito da su duk tasha dama taci abinci ai kuwa take ta fara jin bacci ta mayar da drugs 'din cikin akwatinta ta  kwanta 



Da safe ma sai kusan 9 ta tashi da kyar jin ana qoqonsa qofar ta ansa a ka bu'de a ka shigo wata budurwa da wata kyakykyawar mata fara suka qaraso inda take suna mata murmushi budurwar ta furta "barka da tashi ya jiki? Mimi tayi murmushi ta ansa da sauqi ta kalli matar ta gaisheta cikin sakin fuska matar tace kin tashi lafiya ya jikin.? Sunkwi da kai tayi tace da sauqi sai ga mai aikin gidan ta shigo da tray cike ta ajiye gaban mimi, mimi ta kalli tray 'din Farfesun kan saniya da dankalin turawa ciki da su vegetables sai 'dayan bull kunun tsamiya sai 'dan qaramin plate da bread sai wani cup da ruwan tea yanata anshi ajiyar zuciya tayi matar tace maza kici sabida jikinki na buqatar abinci kar kirika wasa da abinci kinji.? Girgiza kai tayi ta furta "zanyi wanka... matar ta doka salati tace hala enjection 'din bai sake ki da wuri ba maza je ta miqe suma su ka miqe suka fita a bathroom tana wanka tunaninsa ya fa'do mata ta fara shafa jigidarta wani masifar yunwarsa take ji kwanan nan a hankali ta furta "I so much missing u my hrt beat" ta qarasa wanka da sauri ta fito tayi sallah sosai kuwa ta kejin yunwa ta shiga cin abinci kamar hauka har ta shaye farfesun tas ta jawo drugs 'dinta ta sha nan danan ta fara jin bacci ta daure miqewa ta saka hijabinta zata je gayar da baba 



Sosai baba ya saki inda ya kalleta ya furta ya jiki ta sunkuyar da kai ya fara magana "Akwai karatun da zakiyi na hudimar haihuwa kamar yadda kika fara a baya to abokina ya nema miki nanan cikin barikinsu  nasan zaki so domin ba yaran kowa ke samun irin wannan damar ba don haka na masa godiya wata uku ne kawai za kiyi ki gama kuma can zaki zauna 'bangaren 'dalibai sosai Mimi taji da'di domin ta gaji da zaman haka ta 'dago da 'dan murmushi ta furta baba nagode Allah ya qara girma amin yace Allah ya miki albarka ta ansa da amin yace nan zuwa jibi litinin zaki fara inajin lahadi ne zasu kaiki can sabida ki gama shirya gurin zamanki to tace ya ce ni anjuma zan koma ya qara mata nasiha ko da wasa bai furta wata kalma da ta shafi Hayat ba har ya wuce ta koma sama 'dakinta can budurwar 'dazun tazo ta ce ni sunana Sumayya nice autar gidan nan yayata Sameera tana Malaysia can take karatu za kuyi made ke da ita murmushi mimi tayi haka sumayya tayi ta janta da hira har mimi ta fara sakewa da ita sai daf zuhur Sumayya ta sauka mimi ta shiga tayi alwala ta fara sallah






Bayan ta idar ne ta qara kwanciya sai kusan 3:29 ta farka ta shiga tayi wanka ta sanja zuwa abaya ja ta mata masifar kyaw ta zauna ta fara karanta wani English novel da ta gani 'dakin sai ga sumayya tazo tace Mimi muje ki rakani zan siyo cosmetics Mimi zata qi Summy ta fara roqarta a dole ta miqe suka fito wai summy ce za tayi driving saidai suna fitowa taimur ma yana parking 'din motarsa ya kira summy yana tanbayarta inda zasu ta fa'da masa ya ce suzo shi ya kaisu koda summy ta kira Mimi taqi da kyar Mimi ta hakura a dole ta shiga inda ya bu'de mata gaba summy na baya sai yayi tuqi ka'dan ya saci kallonta har suka iso wani Babban mall na borno fashion summy ta za'bi duk abinda ya kawo ta a yayinda Taimur ya shiga za'bawa Mimi kaya itama gowns da shoes da su parfumes sosai ya mata siyayya suka fito yace su qarasa baya wajen ice cream a dole su ka zauna a ka kawo musu Mimi ta kasa ko qwaqwaran motsi a yayinda Taimur duk hankalinsa na kanta yana 'dan janta da hira a dole ta 'dan sha ganin har magrib ta kusa ya ce su wuce gida ko a hanya kanta na qasa har suka iso gida ko kafin ya qaraso ya bu'de mata har ta bu'de summy ta saki dariya tace kai Mimi yaya kike gudu ko.? Sunkwi da kai Mimi tayi shima ya tsura mata idanu a hankali ta kalli summy ta wuce cikin gidan suna tana shiga mama kamar yadda taji yaran na kiranta tana shirin haurawa sama itama Mimi ta gaisheta tace ya jiki.? Mimi tace da sauqi ta haura mama ta bita da kallon tana ayyana yanayin kunyar yarinyar na burgeta tana shiga ta shiga bathroom ta 'dauro alwala tazo tayi sallah ta bu'de qur'ani tana karatu summy ta shigo ledoji ta zauna kan wata 1sita da ke 'dakin har Mimi ta dasa aya taso tayi karatu mai tsawo sabida ta da'de batayi ba amma a dole tasa aya tana kallon summy nan summy tace mata kayanki ne yaya ya saya miki ajiyar zuciya Mimi tayi tace ah ah ki Maida masa summy ta mata hararar wasa tace naqi nan zan barshi ta miqe har ta kai bakin qofa tace ki fito kuma zamu ci abinci inji mama tana gama fa'da ta wuce Mimi ta da'de kafin ta miqe jiki ba kwari ta sakko su hu'du ne mama taimur sai Najim da summy a hankali Mimi ta qarasa ganin yadda Taimur ya tsareta da idanu har ta qarasa ta zauna




Bayan sun gama cin abincin an da'de ana fira dukda Mimi ko qala ganin 10:37 ta musu sallama ta haura ta rufe qofar tana kama irjinta tare da wasu hawaye masu 'dumi da suka zo mata sosai ta kejin tana kewarsa tanason ganinsa wani gobarar sonsa ne taji ya kama mata zuciya ta zauna qasan tiles bayanta na jikin qofar ta saki kuka sosai ta keyi taji anshin a hankali ta 'dago kanta idanunta su ka shige cikin nasa lumshe idanunta tayi ta qara bu'dewa da tsammanin mafarki ta keyi saidai shi 'din ne rungumarsa tayi tana kissing wuyansa tana kara kuka sosai ta qanqanmeshi shima haka tanata kuka tana furta "I love u" ya saki ajiyar zuciya ya na qara manneta jikinsa..

💖AQIDARMU💖



       Na 



Boyayyiyar marubuciya

No comments