Breaking News

AQIDARMU Book 1 Page 31-32

 🅿️31/32






A gigice duk su kayi kanta baba kam wucewarsa yayi ya koma falonsa mami ta ta'ba irjin mimi saidai shiru babu alamar numfShi doguwar riga dada ta jawo ta jefa mata goggo ta kalli Dada tace maza je taso salisu ya fiddo mota mu je asibiti Dada taje ta kira salisu a guje su ka nufi hospital 44 a ka anshi Mimi a kayi emergency da ita 




Kusan 5:22am Dr yazo ya kalli su Dada yace an tsaida jinin sannan alhamdl cikin nanan saidai yanzu ba mai ganinta har sai ta farfa'do ajiyar zuciya su kayi babu wanda ya qara magana dr ya wuce su kaje su ka fara alwala 





Yana zaune yayi shiru ya 'dauki wayarsa yayi mata msg ta duba ta masa reply cikin wani irin yanayi ya sake mata reply shiru tayi kafin ta miqe ta shirya cikin Jan less ta fito duk yara na school da kanta ta ke driving yara driver yaje cefane tunani ta keyi har ta iso asibitin a daidai lokacin da wata black range rover itama tayi parking can nesa 



Mummy ta fito ta nufi cikin asibitin saidai ta jefa kira a ka 'daga ta furta ka sameni bayan lab "ok" yace ta tsinke call 'din 



Koda ya zo bayani ya mata cike da tausayawa ta ke kallonsa ta furta pls Dr ku mayar da hankali sosai a kanta she's very important 4us ajiyar zuciya yayi yace IA hajiya ta masa sallama ta wuce 





****************





Yau cikin Mimi wata bakwai da kwanaki sha 'daya tunda a ka sallamota ta qara dawowa haukan tuburan a kan ganta tana kuka tana nuni da hannunta ko taita furta "Babyna" duk an dawo an duqufa yi mata addu'a saidai baba ko gezau anyi lallashi an yi roqo anyi magiya yana kan bakansa mimi bazata ta'ba komawa zuri'ar da bata 'yen "AQIDARMU" mu ba wannan kalma ta dawo tana fusata kowa harta da qanninsa da a baya su ke goya masa baya 




Tana zaune babban falon gidan su kuma 'yen gidan suna falon baba yana musu karatu domin yanzu 'dalibansa sun ragu sosai sun dena zuwa taji anshinsa a hankali ta 'dago tana kallonsa har idanunta sun kawo qwalla ta fara ja da baya yana matsawa tana ja da baya har ta kai arshen kujerar zata fa'di ya tsaya yana kallonta tanata ruwan hawaye ta furta " pls live me alone" ya bu'de baki zaiyi magana ta saka hannunta ta kulle kunnenta ta furta "i hate u" ya riqota yana shigar da idanunsa cikin nata ta fara kuka tana furta " baka sona baka tausayina i dont want see u a gain live me alone ta saki kuka ya fara kokarin nutsar da ita ta fusge hannunta saura ka'dan ta fa'di ya tareta ta qara sakin kuka tana live me alone  ta saki kuka da arfi tana zama qasa idanunta a rufe hannuwanta a kunnenta tana kuka da arfi da gudu duk suka shigo falon ganinta ta tanata ihu suka qarasa mami ta riqota ta fisge tana matsawa inda can bayanta babu komai ko kafin goggo hanne ta tarota tuni ta zame ta fa'di suka saki qara duk falon nan take ta suma kuwa jini ya 'balle mata mai masifar yawa cikin gigicewa Goggo jummai ta saki kuka tana furta shikenan ta mutu






Mami tace dada riqeta mu je nan suka fito da Mimi rai hannun Allah ko ta kan baba basu qara bi ba suka kira salisu ya tayar da mota sai 44 




Cikin mugun tashin hankali ya kiran layinta yana furta "Mummy kizo yanzu pls" kallon wayar tayi tayi shiru kafin ta nufi    ,dan marina road U/rimi tana shiga makeken gidan yana tsaye yana kallon qofa ta ko qarasowa ba tayi ba ya furta "Mummy she hate me sabida ni yanzu take cikin halin mutuwa" ajiyar zuciya mummy tayi tana qarasawa ta riqo hannunsa su ka zauna ta kalleshi tana furta "my boy ka kwantar da hankalinka zata warke ta yafe maka idan tasan duk abinda kake yi domin ita ka keyi" kallonta yayi ya furta "Mummy u kno i love her fiye da rayuwata, ajiyar zuciya tayi tana ta furta i kno and Insha Allah ba zaka rasa ta ba Allah yana kallon duk kokarin da kake yi domin ta shiru yayi yana kwantar da kansa cinyarta tana shafa kansa 




A 44 likitoci su kace Opération za'a yiwa mimi sosai hankalin su goggo ya tashi inda Dada ta kalli mami tace yaya ki saka hannu sabida bamu da mafita, mami ta kalli takardar tayi shiru tana tunanin yadda zata qare da baba in ta sakarci hannun tafi kowa  



Jin shiru dr ya ce hajiya babu lokaci sosai dada tace pls mami kece babba ki saka mami tace ke ce fa kike kawo ta awo ke ya kamata ki saka su goggo su ka shiga bala'i wai shi yayan mala'ikan mutuwa ne da kukejin tsoronsa haka bari za kuyi yarinyar marainiya ta mutu sabida tsoron mijinku a hankali suka ji wani lafiyayyen anshi da ya hargitsa gaba 'daya gurin su ka juya duk baki bu'de suna kallon wani kyakykyawa matashin balarabe dogo ne da 'dan mur'da'den jiki ba dayawa ba yanada lumsassun idanuwa marasa girma sai shanyewa idanun ga dogon siririn hancinsa har baka sai bakinsa mai 'dan tudu ka'dan dark pink kamar ya shafa jan baki gashinsa a kwance a tsintsiyar hannunsa yana sanye da shirt fara sky bleu mai aramin hannu da baqin wando da bakin cover shoe babu safa sai silver watch na Kamfanin Alberto Vagga wani italian company ne da ba kowa ne ya sansu ba ko sayan kayansu tsabar tsadar kayansu duk sun shagala kallonsa ganin ya miqa hannu ya anshi fayel 'din mimi har lokacin suma su goggo idanunsu na kansa suka ji dr ya furta "wanene kai"? ya juya yana kallon yadda duk suka tsura masa idanu ya kalli dr "Yace Mijinta"..!  Yawu su mami suka ha'diya suna kallonsa...

💖AQIDARMU💖



           Na


Boyayyiyar marubuciya


No comments