Breaking News

AQIDARMU Book 1 Page 25-26

 🅿️25/26






Sam batama jin mai suke fa'da sabida wani jiri da take ji yaya Fatima yafinyar goggo jummai ce ta matsa cikin tausayawa ta ruqo mimi tana miqar da ita inda a she gaba 'daya mimi a jiqe take jagab bayan baqar abayar da ke jikinta da ruwan da ta fiddashi tun cikin baccin Salati su goggo suka saka suna kallon junansu goggo hanne tace wannan wace irin jaraba ce da tsakar rana haka. Hawaye mimi ta fara Yaya Fatima ta raka ta har toilet ta barta cikin tausayawa  ta fito runtse Idanunta tayi tana sakin zazzafa hawaye tare da kai hannunta qasan pant 'dinta taji shi jiqe har ruwan na fito wani irin qaramin kuka ta saki tana kama gaban kanta 



fatima ta kalli su goggo tace haba goggo ya kamata muna tausayawa mimi da wanne za taji suka daka mata tsawa kimana shiru, goggo jummai tace kiduba yadda mimi duk ta haukace a ce bar cikin Bacci da tsakar rana mafarkinsa take yana saduwa da ita don tsabar jaraba duk ta jiqe jiqewar da ko a zahiri a namiji ya kusance ka ai baka jiqe haka ba bare cikin mafarki inba jarabar da ya koya mata ba shiasa duk ta fitsare bata damu duk duniya susan tana sonsa ba dukda muguwar Aqidarshi da ba kaunar "AQIDARMU" su ke yi ba Fatima ta sake bu'de baki za tayi magana duk suka mata caaa a dole tayi shiru ta kyalesu arshe ma ta musu sallama ta wuce gidanta ta barsu da kumfar baki



Tana wankan tana kuka ganin rin abinda ya fita cikinta harda kauri2 superm ta gama tana shafa jigidarta tana hawaye har ta gama ta fito duk suka bita da harara...





Yana zaune babban falonsu shi da Banat inda Banat ke bashi labarin kuriciyarsu yana lumshe idanu Banat 'din ma haka sun da'de kafin banat ya wuce inda yayiwa wata made 'dinsu alama tazo ta jashi ta kaishi 'dakinsa ta fito a hankali ta barshi ta rufo masa 'dakin ta wuce qarasawa yayi ya jawo wata drower ya fidda wata qaramar akwati ya 'dauki waya ya fara rubuta text ya gama ya tura 



Mummy na Office msg 'din ya shigo ta karanta tayi murmushi ta masa reply shima murnushin yayi ya qara mata msg yaji pic ya shigo a hankali ya bu'de wayar yana kallo ya saki wani kyakykyawan ajiyar zuciya yana shafa pic 'din ya kai bakinsa yayi kissing ya qara shafawa kafin ya kashe wayar ya Maida cikin akwatin ya rufe ya mayar inda take ya kira matsa wani abu wani qararrarawa take a ka mayar da camerar gidan a ka kunna ya lumshe idanunsa ya miqe a gadon yana lumshe idanunsa....




Sosai su Najwa hankalinsu ya kwanta sunyi nasara kan Mummy sannan kullum suna kan sawa noor yana yiwa Hayat injection na mantuwa 



Haka mimi ke fuskantar cusgabawa da izaya a gun su goggo Salman ba ya zuwa ko hutu yana matuqar son of bawa mimi waya amma shima dole ya hakura sabida bayason taje tana alaqa da Hayat dukda ance Hayat 'din ma ya samu ta'bin hankali so zai bari sai ta haihu in zata tare gun Safwan sai ya bata dukda mugun tausayinta da yake ji babu yadda zaiyi ya barta ta rayu da 'dan shi'a..




*************




Kwanaki sun shu'de abubuwa sun faru dayawa wasu na ban mamaki da al'ajabi...




Yau cikin mimi wata tara har da kwana biyar goggo na kaita awo amma na ganin dama sai dr ya basu appointment amma goggo taqi kaita in ya bada drugs a saya ko mummy ta tanbayeta sai tace ta yar da takardar haka mummy ke kyaleta gudun kada ' dan damar da ta bata ya gushe wani abin mamaki ma sai goggo ta yiwa mummy qaryar EDD 'din mimi sabida dama babu takarda ko 'daya mummy duk bata damu ba itadai fatanta mimi ta haihu lafiya sannan sau biyu a na yiwa mimi scanning amma goggo tace kar a basu results basuso 




2:45am ne ya zaro akwatinsa ya fidda wayar ya fara msg 'din ya da'de yana rubutu kafin ya gama ya tura 



Mummy na kan dadduma ta gani ta masa reply ya lumshe idanunsa kafin ya sake mata ta qara masa reply ya karanta yayi shiru yana kallon msg 'din bai iya bata ansa ba ya kashe wayar ya maida ma'ajiyarta ya yi shiru zuciyarsa na harbawa da sauri2 ya runtse idanunsa 



Itama mummy shiru tayi sosai kafin ta miqe taci gaba da nafilfili har a ka kira asuba...




Cikin Bacci ta saqi wani qara sakamakon wani irin irin turzajjen riqewa da bayanta yayi ta qara yunqurawa da nufin tashi ganin an fara kiran asuba saidai abu yaci tura ta saki kuka sosai tana komawa kwancen goggo ta farka tana furta lafiya tayi kanta cikin gigita ta furta "wayyo goggo bayana" goggon tace ciwo abin ne yazo nan tazo ta riqota ta 'gyarata ta fita ta kirawo mai napep na kusa da gidansu ta riqe mimi tana cewa yaran su mufida da safina ku kula da gida suka ce to 




Tun a napep wani azababben ciwon mara ga cikin da wani irin mugun tsawo da girma goggo tace ki daure mu isa kinga wannan qadaddararren ciki naki da shegen tsawon tsiya Allah dai ya kawo mana arshensa yau kuka ta ke har suka isa take a kayi 'dakin labour da ita goggo ta kira goggo hanne da su fatima su firdausi da bilki da safara 'u haka suka cika asibitin 




5:22pm mimi shiru nakuda take duk tagama jigata tayi kuka har hawayen ya bushe tayi addu'a har addu'oin bakinta sun qare ta dawo yanzu sai idanu suma su goggo har sun dawo suna tausaya mata tare da Allah wadai goggo jummai tace ba dole ta wahala ba jinin shi'a ai taurin kan tsiya garesu a kace tun farkonsu surutai marasa anfani da har yaranta haushin maganganunta su keyi 




Tun safiyar ranar kawunansa suna zagayeshi dashi sakamakon yau ce ranar haihuwarsa sun masa cakes kusan kala goma ga ciye2 kala2 kallonsu duk ya keyi yana murmushi baby wanda babu cikin danginsa na "Thariq Ahnan" har matan cousins 'dinsa da mazajen cousins 'dinsa mata haka su ke ta yi masa waqa cike da nisha'di abu'noor yazo ya shafa kansa kansa ya furta happy birthday my son murmushi yayi 

Fusataccen Ciwon mara ya tayar da ita daga 'dan qara ta saki ta furta  "ya Allah" goggo ta farka cikin hanzari a ke an dawo da Mimi word su ka'dai sabida prior hospital ne kuka ta keyi tana riqe hannun goggo sosai goggo ta tausaya mata wannan nataccen naquda nan goggo ta fita ta kira Dr yazo a ka qara maidata 'dakin Labour sai nishi ta keyi tana hawaye 



Sunata shagalinsu a na ta ciye2  yayinda shi ya tsinci zuciyarsa cikin wani irin yanayi ga irjinsa sai harbawa ya keyi...


11:23pm wani faya ta fashe inda azaba ya qaru mata ga muryarta ta dashe haka hawaye sai nishi 11:39 ta haifi kyakyawar babynta bayan fitowar macen da 3mnts ta sake haihuwar santalelen yaronta namiji wanda kamar an tsaga kara da Hayat tana haihuwarsa ne numfashinta ya tafi inda cikin mugun tashin hankali drs su ka fara qoqarin taimaka mata 




Su goggo na waje a ka sanar da su ta haihu suka yi hamdala 




A hankali ya saki ajiyar zuciya yana kallon danginsa da ke ta harkokinsu ya Banat ya qaraso yana bashi wani samosa a baki murmushi yayi ya ansa ya kalli Banat yace ya raka shi 'daki ok Banat yace ya raka shi ya kullo masa 




Wayar ya fitar yayi msg mummy cikin bacci ta ji shigowar msg 'din ta duba shiru tayi tana tunani kafin tayi reply ya duba ya qara mata reply ta kalla itama shirun ta qara yi kafin ta masa reply yayi ajiyar zuciya ya kashe wayar ya maidata ma'ajiyarta ha danna 'yer qararrawar ya ja kekensa ya sakko qasa still sunata shagalinsu 




7:23 am Mummy ta sauka domin tun kafin asuba su ka fito gida da driver




Mimi na ta bacci goggo na sallah sauran sun koma gida yiwa mimi girki a hankali ta fara bu'de idanunta har ta bu'de goggo ta miqe tana mata sannu lumshe idanunta tayi goggo za tayi magana nurses suka shigo su ka kalli goggo su kace "a kawo yaran za'a musu allura goggo ta kallesu da mamaki tace ai mu a gadon da aka ajiyesu a nan mu ka barsu cikin ki'dima nurses su ka kalli goggo itama kallon nasu take tace "kuna nufin yaran sun 'bata ne ko me? Wani irin zaburowa Mimi tayi daga gado zama ta fa'di ta kalli goggo har idanunta sun ciko muryarta da "kyar ta furta goggo wasu yaran"? Yawu goggo ta ha'diya a karon farko tunda masifun suka fara taji tausayin Mimi ya kamata ta kasa magana 'dayan nurses tace "yaranki"... Idanu Mimi ta qurawa nurse 'din irjinta na harbawa a na hangowa kamar zai fito waje



Mummy na parking qofar su goggo su Fatima na isowa suma suka gaisa tace goggo fa suka bata labari ai jiki na rawa tace musu su shiga mota suje asibitin suka shiga suna kwatantawa driver har suka isa inda suna tsayuwa motar police ma na tsayuwa cike da .mamaki suka qarasa suna tanbayar mai ya faru a ka basu labari mummy cikin masifar tashin hankali tace garin yaya.?  Suka qarasa shiga asibitin inda nan ma hankalinsu ya qara tashin sakamakon suman da mimi tayi ga jini ya tsinke mata wai zuciyarta ce ta buga da a ka tabbatar da an sace yaran ta goggo na ta kuka itama hankali a tashe tace fatima ta kirawo mata baba inda shima hankalinsa ya tashi yace su Dada nanan zuwa saidai yana kashe wayar maganar sa da su Abu'noor ta fa'do masa inda bai ko 'bata Monaco grand ba ya jefa layin abu'noor  bugu 'daya kuwa abu'noor ya matsa daga cikin mutane ya ,daga wayar sanin dama yana jiran wannan kiran tun watanni takwas sallama kawai baba yayi ya furta "kun turo an 'dauke su"? Abu'noor yace su wa"?  Baba ya tsinke kiran yayi shiru yana ayyana mummy ce 



Abu'noor yayi ta kiran baba 'baba yaqi 'dagawa ya juya zai shiga yaga Najwa bayansa kallonta yake da mamakin yaushe ta qaraso yaji ta furta "Ko waye ya sacesu wlh ni zan kar'bosu da hannuna kallonta yayi da mamaki nan ta Shiga bashi labarin haihuwar mimi inda tace wani ya shammacemu daga mu har Yasmin amma zan hanka'doshi nasa wasa ne shiru abu'noor yayi ya kalleta yace Hayat zai iya warkewa anytym kuma kin sani so kiyi kokari bamuda isasashen lokaci murmushi tayi ta ce muje..



Hawaye mummy ke yi sosai tana ayyana a yau zata bar Nigeria a wannan karon ko me zai faru ta shirya facing 'din "Thariq Ahnan Family" Dr ya zo cikin tashin hankali ya kallesu yace ta farka saidai a yanzu ba mu ya kamata mu kula da ita ba " goggo tace kamar yaya likita bayan kaine ke kula da ita tunda tazo garin nan mummy kam ta kasa magana Dr ya kalli goggo yace "sabida a yanzu matsalar qoqolwa gareta ba ta cikin haibuwa ba" zabura mummy tayi tace Dr wat.? Yace wlh yanzu ma 'allurar bacci mu ka qara tana sabida tana farfa'dowa ta fara muga kanta a bango har har ta fara yiwa kanta rauni so yanzu asibitin mahaukata ya kamata kawai ku kaita salati goggo ta saka tana zama qasa mummy ma haka....

💖AQIDARMU💖


           Na



Boyayyiyar marubuciya

No comments