Breaking News

AQIDARMU Book 1 Page 21-22

 21/22





Durqusawa mummy tayi ta fara roqar security 'din wai ya kira Abu'ahalm za tayi masa magana saidai kamar baya gurin inda a qarshe ya ce mata in bata bar gurin ba zai saka yaransa su wulaqantata cikin tashin hankali da kuka ta tashi tana tafiya ta kuka tana juyawa har ta Fito taxi ta 'dauka direct "medical institute  Iran" tana shiga direct office 'din Banat ta wuce yana ciki ta shiga tana sakin kuka tare da furta (banat ka taimakeni hayat 'dana ne yaya ta bani shi tun tanada rai" banat ya taso daga kujerarsa yana riqeta ya furta mummy pls ki zauna ya zaunar da ita ya 'diba mata ruwa da kansa ya bata ka'dan ta sha ta ture tana kallonsa ta fara magana " Banat kana sane tun kuna yara iyayen Hayat na raye amma gurina yafi zama girgiza kai banat yayi za taci gaba da magana ta sauke ajiyar zuciya tayi shiru tana hawaye sakamakon tunawa da tayi kwai kyakykyawar zumunci tsakanin zuri'arsu Banat da ta su Hayat wanda hakan yasa 'yen gidansu Banat biyu na auren cousins 'din Hayat yayinda maman Ahlam itama goggo ce a gurin Banat duk kuma duk AQIDARSU 'daya tun kakanni don shiasa duk amincin Hayat da Banat bata ta'ba bari Banat ya gane tana son Hayat ya bar Iran ba domin tasan hatsarin yin hakan jin tayi shiru shima ya sauya maganarsa zuwa cewa "mummy ciwo da sauqi duk yana gurin Allah Hayat zai iya warkewa a kowani lokaci pls ki kwantar da hankalinki , ajiyar zuciya tace bari naje gida na huta zan bi jirgin safe gobe ta miqe tana share hawayenta ta kalli Banat da shima ita ya ke kallo ta fara magana cikin yanayin da dole mutum yaji sai ya tausaya mata tace 'Pls Banat inaso domin Allah da amincin da ke tsakaninka da Hayat kayimin alfarmar turamin video 'din situation 'dinsa a kullum da safe da kuma yammA zan iya amincewa da kai.? Cikin mugun tausayawa yace Mummy IA na miki alkawari (Tnx) tace tana share hawaye ta fita ta hau taxi ta nufi gida zuciyarta kamar zata fito sabida damuwa tana shiga falon ta fara tariyo ranar da ta kawo mimi Hayat ya qura mata idanu har sai da ta dungure masa kai yayi dariya yana ra'da mata (Mummy a ina kika samo wannan cute babyn.)? Kallon mimi tayi ta kalleshi tace (ba ruwanka da ita tana ja masa kunne yace to mummy yayi dariya yana kwantar da kansa kafa'darta zama tayi kujerar tana hawaye sosai tabbas burinta na shekara da shekaru ya rushe burinta mafi tsada da daraja cikin duka burukanta na duniya ya rushe garin yaya.? Sosai mummy ke hawaye tare da qara jadaddawa kanta bazata karaya ba zata koma Nigeria ta qara tunani da neman mafita sannan dole na ta rigasu kar'be abinda duk mimi ta haifa ko mai ze faru bazata bari su kwace jaririn ko jaririyar ba da haka taje tayi wanka ta mayar da sallolinta ta 'dan nemi abinci taci ta Sara shirya kayanta..



Babu irin roqon da Mami ba tayiwa baba ba ya bu'de mimi yaqi tace ko don abinda ke cikinta wanda bashida laifin komai baba yace wannan ma shine babbar matsakarta a yanzu zata haifi jinin shi'a.. goggo hanne ta ansa ai kuwa wlh yaya gara ma shegen cikin ya fita ko zamu tsira da mutuncinmu wannan jagwalgwalo yayi yawa in maganar nan ta fita waje mai zamu cewa duniya ana kallonmu a matsayin babban gida wanda a ke koyi da tarbjyar yaranmu yau a ce 'yermu ta auri 'dan shi'a har tana suma sabida jarabar sonsa wlh in mimi zata mutu bazamu barta ta koma hannun  'yen wannan aqidar ba baba kam tashi ma yayi ya tafi abinsa 'bangarensa har lokacin yabajin kamar yaje ya shaqe mimi ta mutu su huta 



Dab asuba ne zazza'bi mai masifar qarfi ya dirar mata tun tana kukan 'dauki har hawayenta ya qafe hakoranta duk sun cije kanta na wani irin sarawa ta idanunta suka fara haurawa sama numfashinta yayi qasa har shiru... 



Dada dai bacci rabi da rabi tayi duk hankalinta na kan mimi...



5:23am jirginsu Salman ya sauka abuja bai ko 'bata lokaci ba ya 'dauki shatar mota har kinkinau



Yana sauka qofar gidan baba na shiga baba bai ganshi ba ya tsaya yana sallamar mai mota baba kuma dab zai shiga gida Fauza ta tsuguna gabansa tana kuka ta furta don Allah baba ka taimaka ka fito da Mimi ko wanka tayi yayi kamar zai wuce ta sake furta baba ko zaka qara maidata don Allah ka bari ta fito tayi ko da wanka ajiyar zuciya yayi ya furta minti goma ta gama komai ta dawo fauza tace eh baba ya fara bu'de qofar ya bu'de suka yana tsaye ta shiga saidai yaji ta saki mugun qara da duk gidan a ka fito shima baba ya 'dan razana da yanayin da tayi qarar a daidai lokacin Salman ya shigo shima ganin iyayensu na rububin shiga falon baba kuma ga baba a tsaye sai shima ya kutsa kai,,, numfashinsa ne shima ya tsaya ganin mimi a sandare babu alamar rai a tare da ita kuka fauza ke yi Sosai tana jijjigata tana furta mimi ki tashi don Allah... a hankali cikin mugun tashin hankali har jikinsa na rawa Salman ya qarasa yana sunkuyawa gaban kanta ya 'dora hannunsa irjin ta yaji tsit ya saki zafafan hawaye yana sunkuyar da kansa goggo jummai cikin rawar murya tace wai mai kuke jira ku 'dagata muje asibiti mana dada ta kalleta tace bana tunanin hakan na da anfani a yanzu.. goggon cikin gigicewa tace kamar yaya...? Fauza ta qara sakin kuka tace goggo mimi ta mut.. maman Safwan ta fara salati tana furta wai wannan wace irin jarabawa ce baba ma dai a yanzu hankalinsa ya tashi duk yana jinsu ya kira salihu driver yace kace Binta da Hanne su 'dauko mimi muje asibiti salihu ya shiga saidai bash yi musu ba suka cicci'beta suka fito har mota suka shiga Salman na baya da su goggo domin tsabar gigicewa babu wanda ma ya tuna ai da Salman bayanan dada da fauza a gaba suka nufi asibitin 44 inda à kayi emergency da mimi su kuwa duk su kayi tagumi suna qara neman agajin ubangiji a kan abubuwan da ke ta faruwa a just 'yen kwanaki 




Drs sunyi nasarar shawo kan mimi dukda har lokacin babu alamar farfa'dowa sabida dogon suma ne tayi don ma anyi sa'a ciki daram haka dr yayiwa su dada bayani hankalin kowa ya kwanta dukda su goggo su fatansu ma bai wuce cikin ya fita ba goggo hanne ta kalli jummai tace wannan shegen ciki da alama sai mun masa taron dangi kan ya rabu da ita goggo jummai tace ai kuwa IA bana barin gidan yaya sai mun tabbatar da fitarsa ko ta wani hali dada na jiyosu ta yi tsaki tana mamakin son kai irin nasu sudai kansu yarinya na can tana fama da rayuwarta su sunanan et suna fatan cikar burinsu Allah ya kyawta ta furta ta miqe tacewa fauza bari naga dr nazo ta wuce Sai yanzu ma su goggon suka hango Salman su ka cika da mamaki goggo jummai ta kirashi ya qaraso ya gaishesu suna tanbayrsa ina ya shiga duk abubuwa suka faru baizo ba bai iya basu ansa ba sanin halinsu nan suka shiga bashi labarin komai harda qari da kuma labarin zuwan najwa



Sosai Salman ya girgiza da labarin tare da qudurce daga nan gidan mummy zashi ta yaudareshi taci amanarsa tabbas shi kansa in da tun farko yasan Hayat 'dan shi'a ne da ko duniya mummy za ta bashi bazai yadda da buqatar ba inda tabbas tanan kam yana bayan baba ko mimi zata mutu don son hayat zai gayawa baba baya suyi komai don tabbatar da sun rabata da Hayat da komai  da ya shafeshi ko ciki kuwa harda qadaddararren cikinsa da ke jikinta...

💖AQIDARMU💖


         Na 



Boyayyiyar marubuciya


No comments