Breaking News

AQIDARMU Book 1 Page 19-20

 19/20






'Dago mimi Najwa tayi da kyaw tana kallonta mimi ma jin masifaffen anshin da ya ke tayar mata da zuciya ta fara qoqarin miqewa tayi nisa da anshin bu'de idanunta tayi a hankali suka kuwa fa'da kan Najwa da itama na ta ke kan mimi cikin rashin walwala 



Irjin mimi ne ya buga taji take jirin ya tafi ta zabura tana qoqarin tashi cikin mugun tashin hankali har ta fara ruwan hawaye.. Zenat duk itama ta gigice tanason gane mai ke faruwa ta kalli Najwa tace "kin san ta ne" Najwa ta kalli mimi da gaba 'daya Hankalinta ya gama tashi sai ruwan hawaye ta keyi tace "Matar Hayat ce" zaro idanu Zenat tayi ta kalli Mimi sannan ta juya tana kallon baba da ke qarasowa inda suke ta furta "NAJWA ko dai mai kama da ita ne"? Najwa da idanunta ke kan mimi da ta fara ja da baya cikin mugun tashin hankali tana girgiza kai tana hawaye ba qaqqautawa na sabon tashin hankalin da ya tunkarota baba ya tsaya gurin yana kallon su ya furta me ke faruwa.? Zenat tayi shiru tana kallon Najwa yayinda Najwa ta miqe ta juya tana kallon baba ta furta "Hayat bazai qara cigaba da auren 'yerka ba domin kuwa yanzu da na gano manufarku ku da Yasmin wlh za muyi komai ni da 'yen uwana domin raba auren "Farida da Hayat" irjin baba ne ya buga nan ya juya yana kallon yadda mimi ke ta girgiza kai kamar nahaukaciya kafin ya dawo da kallonsa kan Najwa ya furta "Ban fahimci mai kike nufi ba.?  Cikin tsagwaren tsana da qasqanci Najwa ta 'dan qara matsawa gaban baba ta furta "ina magana ne shirin da kukeyi kai da Yasmin domin raba mu da yaron mu har ka bashi 'yerka ba tare da neman danginsa vae wanda kowa yasan dangin uba ke aurar da 'da mace ko namiji amma  indai dangin na raye amma sabida sharrin da muguwar manufar da kuke da shi a kan "AQIDARMU" yasa kuka yi auren (Farida da Hayat) baku sanar da mu ba yawu baba ya ha'diya na baqin ciki ya kalli Zenat da itace ya sani ya furta "Zenatu wannan wacece"? Zenat tace baba qawata ce 'yer Iran ce nan ta bashi labarin dangin Zenat da alaqarta da Hayat wani irin jiri baba yaji yana fusgarsa ya kalli mimi da tazama qaramar mahakaciya can nesa da su domin har lokacin girgiza kanta kawai take tana hawaye baba ya fara takawa zuwa inda take tana qara ja da baya har ta kai bango kallonta baba keyi yana wani irin hucin baqin ciki ya keyi yasa hannunsa ya shaqo mimi ya shar'ba mata lafiyayyen mari da numfashinta ya 'dauke ya qara shar'ba mata na biyu numfashinta ya tsaya na second ya wullata qasa ta saki qarar da wasu cikin gidan su kaji mummy ma fitowarta kenan da gudu ita da dada suka nufi falon baba da suka jiyo daga nan qarar ke fitowa irjin mummy ne ya buga ganin Najwa taja ta tsaya itama  taji kanta ya wani irin sarawa tana tanbayar kanta "tayaya"? Baba ya juya dada za tayi magana ya dakatar da ita yana kallon mummy cikin mugun 'bacin rai ya furta "'danki 'dan wace AQIDA  ne"? Jikin mummy ya fara  ya fara ka'duwa baba ya daka mata data irin tsawa ta saki hawaye bakinta na rawa tanason yin magana ta kasa sai rawar tashin hankali jikinta ke yi Najwa ta kalli baba cikin gadara tace "mu 'yen asalin Iran ne iyayanemu da kakanni kuma (AQIDARMU) tun iyaye da kakkani har gobe shine (SHI'A) kasan kanada matsala da 'yen "AQIDARMU" ta yaya ka aurawa 'danmu 'yer ka"? Baba da Dada suka ha'diyi yawun bakin ciki taci gaba au ko kuma dama kwa'dayin tarin dukiyar da mahaifinsa ya bar masa ne bayan wanda kakkaninsa suka bar masa kasan ku 'yen sunna kwaiku da shegen kwa'day..... Baba ya tsinketa da lafiyayyen mari da sai da walkiya ya fito sannan ya kalli Zenat cikin mugun 'bacin rai yace maza ku fitarmin a gida Zenat za tayi magana ya daka mata tsawa itama jikinta na rawa ta jawo hannun Najwa zasu fita Najwa ta fusge ta tsaya ta kalli inda Mimi ke kusan sume ta kalli baba ta kalli Yasmin ta furta "za muyi komai domin ganin bayan wanda duk ya nemi shiga sabgarmu musamman ta zuri'armu har kuma ya nemi cire wani daga cikin Iyalanmu daga "AQIDARMU" tana ganache fa'd'i ta fisge hannunta cikin na Zenat ta fita gidan har da qafa ma take tafiya sai da Zenat ta bita a mota tukuna ta shiga suka bar kinkinau 



Dada mummy baba duk suna tsaye tun bayan fitar su Najwa baba ya kalli Mummy ya furta "na baki 30mnts ki barmin gidana sannan kisani ko 'danki ya saki mimi ko bai saketa ba indai ni ne uban mimi a yanzu a wannan duniyar to babu ita babu 'danki har abad... Bai qarasa ba suka ga mimi riqe da qafarsa ta rungume tana kuka duk fuskarta a kumbure kallonta duk suke baba yana motsa qafarsa tana qara rungumewa tana kuma "tausayinta ne ya cika mummy da Dada ta furta "baba don girman Allah kayi hakuri kayimin komai amma karka rabani da shi wlh shine rayuwata" qoqari baba ya qarayi ya janye qafarsa ta ringume gam tana kuka mummy da Dada ma kukan su keyi a hankali ta fara magana "baba nasan nayi laifi nabi tsarin Ya Salman da goggo ba tare da izninku ba kai da Mama, amma don girman Allah baba inason hayat bazan iya rayuwa da kowani namiji ba sai sh... Wani wawan fincika baba tayi mata ya jefa ta gefe ya kalleta yace wlh Farida wannan jika kuma 'dan AQIDAR shi'a ko shine qarshen namiji a zan gwammace na ki mutu babu aure da ki....su kaga ta salale a gurin da sauri zasu qarasa ya daka musu tsawa yace su fita Dada za tayi magana ya furta wlh 'kina furta ko wace irin mamma ce a bakin aurenki.. juyawa tayi ta fita mummy ma za tayi magana "ya furta nace na baki 30mnts ki barmin gidana in ba haka ba hukuma ce zata fitar da ke daga gidan nan" jimm tayi cikin tashin hankali ta fita falon yana inda yake Karin shima fitowar yayi ya kulle qofar falon da key duk 'yen uwansa qanninsa na qofar falon sunji duk abinda ya faru goggo can nesa da su sai hawaye ta keyi ya kalleta yace "anjuma ka'dan kiyi shiri ki bar gidan nan kada na qara ganinki" ya wuce abinsa zauren waje inda duk a ka juya a na kallon goggo asma wasu na jifanta da mugayen alkaba'I wai ta zama annoba a danginsu kanta na qasa tanata hawaye



Mummy ma tayi kuka har ta gaji kafin ta fara tattara kayanta ta gama tas ta fito ta shiga gun dada ta mata godiya sannan ta bata wata recorded tace ta bawa mimi hawaye dada keyi mummy ta fito duk a nata binta da kallo har ta bar gidan napep ta 'dauka zuwa airport zata koma Iran dukda wani masifaffen tsoro da ya shigeta a kan batasan suma yaya zata qare da su ba acan domin zuwa najwa Nigeria na nufin sun fara zarginta sunan Allah ta fara kira a kan ya kawo mata 'dauki har ta iso airport ta bi jirgin abuja a can abuja ma cikin sa'a ta samu flyt 'din Tehran ta shiga zuciyarta cike da saqe2 



Salman yayi shiru mai ke faruwa tun jiya da ya sayi sim yanata neman layin mama off na goggo off ga mimi ba waya tunani yayi baiso a san yayi nisa ba sai ya 'dan kwana biyu but yanason sanin halin da gida ke ciki musamman in ya tuna halin da ya bar mimi no ba Safwan ya fara kira saidai wayar na ta ringing Safwan na Office ganin no waje yayi tsammanin ko wani daga cikin abokansa ne ya 'daga Salman yayi sallama safwan ya ansa ya 'dago wayar yana kallon no wannan no na (Malaysia) ne cike da mamaki da tsana da 'bacin rai Saddam ya furta 'dole ka bar qasar tunda burinka ya cika bu qatarka ta biya ka yiwa qanwarka auren samun ku'di to albishirinka mugun kwa'dayinka kai da goggonka yayi ajalin mamanka' irjin Salman ne ya buga yace Safwan maganar me kake yi ne.? Tsaki Safwan yayi ya tsinke call 'din yana hucin baqin ciki labarin da Layla ta bashi 'dazu wai mimi na ta ihu tana roqar baba ya barta ta koma gun mijinta tana mutuwar sonsa , jifa Safwan yayi da wayarsa qirar Samsung s8 ta tarwatse yana fidda huci mai zafi yana tuna tunda ya ke neman mimi har ya aureta har suka rabu ko (kana burgeni bata ta'ba furta masa ba bare ina sonka wai yau baban da kowa ke shakkarsa mimi take roko tana kukan ya barta da wani sabida tsabar son da take masa; huci ya furzar mai zafi tabbas zasu saka qafar wando shi da Mimi domin kuwa bazai ta'ba bari ta ku'buce masa ba 



Cikin tashin hankali Salman ke nanata abinda Safwan ya fa'da masa da sauri ya lalubi wayar Dada sanin tafi kowa Sanyin hankali cikin iyaye mata na danginsu tana 'daki zaune har lokacin tausayin mimi ya hanata sake fitowa waje taji wayarta na ringing ta 'daga ko kallon no batayi ba Salman ya mata sallama ta ansa a qagauce kamar dama tana jiran kiran nasa hakan da ya fahimta ne yasa jikinsa ya qara sanyi ya furta "Dada mai ke faruwa"? cikin jimami ta fara bashi labarin komai har izuwa abinda ya faru yau kuka ya keyi tabbas shima yayi danasanin wannan badakala da ya kawo sakamako mara kyaw lallashinsa ta fara yace dada zanyi bucking yau IA zuwa taso hanashi sabida gudun wani sabon tashin hankalin da baba saidai ta tuna mahaifiyarsa ce ta rasu dole ko mai zai faru ya zo sannan ko ba komai qanwarsa zata 'danji sanyi in ta ganshi ganin har goggonta baba ya kora ga danginsu yanzu kowa ya fara tsanarta jin tana Hayat ta ke so ba Safwan ba saidai dada bata fa'dawa Salman wannan 'bangaren ba ganin hankalinsa ya gama tashi da rashin mahaifiyarsa ko bayan sun gama waya da dada sosai yayi kuka ya bu'de system 'dinsa yayi bucking ya shirya kaya ka'dan just 9dys zasu lecture kuma baima gama sauran hidimominsa ba amma yace mama tafi komai domin dama sabida ita na keson yin komai 



Koda suka isa U/rimi Najwa taqi magana da Zenat saida Zenat tayi ta lallashi kafin tace 'kenan kinyimin qarya kuma 'yen Aqidar Izala ne.? Zenat tace wlh qawata AQIDARMU 'daya kawai a akwai abinda mu ke son ganowa ne a AQIDARSU kasancewarsa babban malamin AQIDAR anan kaduna shiasa mu ka yanke hukuncin yin binciken gurinsa domin dayawa basusan mu 'yen shi'a bane muna 'boyewa sabida yadda a ke tsanarmu sa  AQIDARMU, na tabbata shima surukarku inda yasan ainihin AQIDARMU wlh ko karen gidanmu bazai kula ba, tsaki Najwa tayi tace zancen banza talaka ma kawai AQIDARMU ai itace Aqida kuma ko Hayat zai mutu da son 'yer sa wlh zamu rabasu domin babu wanda zai kawo mana arshen AQIDARMU a zuciyar wani daga cikin iyalanmu domin kuwa in bamu raba Hayat da Farida ba to tabbas ita zata rabamu da shi sabida tunda ya aureta ma ya zama sakarai nan komai ya saki na family ya dena zuwa gurinmu ko yaushe yana gida in ba aiki sannan tana juyashi son ranta ko gaban 'yen uwansa in sunje gidansu sannan kinsan a tsarin danginmu indai 'da namiji ya auro mace a na bawa matar 5%100 daga kason kamfani dayawan yaran matan  da ke auren yaranmu ko sabida wannan kwa'dayin suna mana biyayya amma mu kayi mamakin ita Farida tunda a ka aurota ko kamfanin bata ta'ba saka qafarta sannan in contract yazo sauran surukanmu duk da kansu suke zuwa har kamfanin suyi signing amma ita ko mun tura mata documents gida tayi signing sai ta qi ashe tabbas ba shi ya kawo ta ba aiki ne tazo yiwa Yasmin na su raba mu da Hayat ko kuma cikin firgici fa kalli Zenat da tunda Najwa ta fara magana bata ce qala ba cikin mugun tashin hankali da 'bacin rai Najwa ta kalli Zenat tana girgiza kai ta furta na yanzu ma na gano ainihin manufar Yasmin na aurawa Hayat Farida kallonta Zenat keyi domin sarai tasan halin Najwa 'yer bala'i ce " ta furta manufar auren itace cire Hayat daga AQIDARMU ta iyaye da kakanni a zabure ta shiga  'dakin da a ka sauketa ta fito da lapton 'dinta ta shiga video call da 'yen uwanta cikin sa'a duk suna tare dama su haka suke indai ba waninsu bane yayj tafiya zuwa wata qasar to a Iran ko da yaushe suna tare dare kawai ke rabasu kowa ya tafi gun iyalansa nan najwa ta basu labarin komai da ya faru da kuma abinda take zargi a kan mummy inda suka shirya yadda zasu fara 'daukan mataki a kanta 



Wani wawan kullewa taji mararta tayi wanda ba komai bane illa yunwa domin bata tuna yaushe ne rabonta da abinci hakan ya sanyata farfa'dowa daga dogon suman da tayi ta fara qoqarin bu'de idanunta da kamar an 'dora mata gum samansu haka taji da kyar ta riqa qoqarin bu'dewa har Allah ya bata nasarar bu'dewa saidai mararta ya riqe kamar wani gingimemen dutse a ka ajiye mata a mararta jan 'duwawu take kamar gurguwa har ta kai main falon baba hango kula da su drinks tayi taci gaba da jan jiki har gurin sam batajin cin komai don haka ko kallon kular ba tayi ba ta jawo gorar ruwa ta fara sha saida ta shanye tas ta ajiye gorar tana mayar da numfashi a kamar irjinta zai 'balle 



Salman na jirgi ya nufo Nigeria saidaj duk duniya ta gama fita a ransa yanata tunano iyayensa yau su duka na rasa su ya furta yana sharar qwalla



Mummy ta sauka Tehran direct "Thariq Ahnan memorial Hospital" ta nufa saidai ga mamakinta tun daga Bakin gate securities ne maqil irin kuma securities 'din nan na manyan sojoji da manyan attajirai da manyan 'yen securities 'din sunkai 'dari suka tare ta za tayi magana suka nuna mata jikin bangon shiga main hospital 'din inda ta fara karantawa kamar haka "Daga yanzu babu mai shiga an tsayar da 'daukan marasa lafiya har sai bayan babban jikan na "Thariq Ahann" ya farfa'do kuma babu mai shiga sai yaran Thariq Ahnan guda biyar " yawu mummy ta ha'diya har ta fara hawaye tab 'din wani security ya fara ringing ya 'daga video call 'din ya fara magana kafin ya juyawa Mummy wayar tana kallo gaba 'dayansu kawunan Hayat ne Abu'Ahlam ya kalleta yace Yasmin damar ki ta kasancewa cikin rayuwar Hayat ta qare mun baki dama dayawa kika ha'incemu don haka zuwa yanzu mun yanke duk wata alaqa tsakaninki da Hayat kuma in maganar matarsa ne mun raba auren shima kuma zamuje mu ga babanta munji tanada ciki kuma lingo kowa sanin yadda mu ke kaunarmu jininmu a duk inda Allah ya qaddari fitowarsa kuma wlh kika je kuka fitar da cikin domin gudun kada ya tashi cikin  cikin AQIDARMU da itace gadonsa wlh tallahi daga ke har uban nata sai mun tabbatar kunyi dana sanin zuwanku duniya mummy ta ha'diyi yawu call 'din ya tsinke tana sakin hawaye cikin mugun tashin hankali.....

💖AQIDARMU💖


          Na


Boyayyiyar marubuciya



No comments