Breaking News

AQIDARMU Book 1 Page 17-18

 🅿️17/18






Tunda ta fita baba yayi shiru wanj irin baqin ciki ya ke ciki mara iyaka mai kenan ya faru ya 'daura aure kan aure.? Ba ma haka ba Salman da goggo sun wulakantashi sunci zarafinsa shin ma yanzu wane mataki zai 'dauka to ma waye wanda suka aurawa mimie 'dagowa yayi cikin yanayin rashin walwala ya kalli Hajiya ya fara magana " yanzu idan irin abinda ya faru da mimie ya faru da da 'diyarki ya zakiji.? Ta yaya zaki yanke hukunci irin haka ba tare da tunani ba a matsayinki na musulma.? 





Hawaye ta saki tace nasan nayi kuskure Ta fara basu labarin "Hayat"  maraya ne wanda dukiyarsa ke hannun danginsa kuma shi ka,dai yayanta ta bari banason rasashi yanada burin aiki qarqashin kansa Hakan kuma bazai yuwu masa ba sai yanada aure a tsarin danginsa hakan yasa na shirya yi masa aure domin cika masa burinsa na kar'bar gadonsa ta dai fa'da musu yadda ta fa'dawa su goggo da Salman domin ta tabbata yadda mimie ke son Hayat ba zata ta'ba furta musu asalin Hayat da "AQIDARSA" ba baba yayi shiru sam ya rasa Madigan on domin kuwa abinda ya sani tabbas shine ba'a aure kan aure wannan al'amari ya zama babba domin dole sai an yawaita bincike dalla2 domin yanke hukunci na musulunci da haka ya kalli Dada yace kuje ki bata masauki kafin asma'u ta dawo toh Dada tace suka miqe saidai ya qara kiran Dada yace ki tabbatar basu ha'du da mimie ba har asma'u ta dawo "toh" tace suka wuce mummy na ayyana komenene za tayi a wannan karon sai ta maidawa Hayat farin cikin sa 



Goggo ta duba 'dakin Salman tass babu 'daddaya tayi da 'dakin saidai babu ta zauna tayi jigum ga zazza' bi itama tanaji sosai a haka ta miqe zata koma kinkinau jin jikinta ya qara 'dan rikice mata ta bu'de 'dakin mama ta shiga ta kwanta saidai baccin ya gagara tanata tariyo rayuwarsu da mama tun suna yara da kuma inta zo suna 'dakin nan ta fara gyara 'dakin can saman Shoglass 'din Mimi da ke 'dakin goggo ta ga takarda ta 'dauka ta fara kokarin bu'dewa tana bu'dewa kuwa ta ga ni cikin hanzari ta mayar da hijabinta ta kullo gidan ta nufi kinkinau 



Mummy tayi sallah a ka kawo mata abinci bata ma ci ba bataso kowa yasan tana kaduna sabida da sun gama zasu koma da mimi 



Sai bayan Ishaa wajajen 9:pm y'en gaisuwa sun tsagaita baba ya tarasu kaf a falonsa harda mimi kanta na qasa domin bata magana ko ta second da kowa baba ya gabatar musu da mummy inda duk abin kowa ke ganinsa kamar almara inda baba yace inaso duk mu kwantar da hankalin mu zamu bi yadda ya kamata in ta kama har gaban alqali zamu je domin a warware komai cikin adalci da tsarin musulunci yanzu muna jiran asm.... Goggo tayi sallama duk suka bita da kallo ta qarasa ta rusuna gaban baba ta miqa masa takardar ya kar'ba ya miqawa Dada yace ta karanta da arfi kowa ya ji ta fara...



Salaam..  9:34 am 23/05 


Ni Hayat Muthallib Ahnan na saki matata Farida Muhammad saki 'daya.



Baba ya kalli mummy yace kinji , mummy tace wlh ya mayar da ita a ranar a tanbayeta... Duk juyawa su kayi suna kallon mimi da kanta har lokacin ke qasa tanata hawaye a kayi a kayi tayi magana ta qi a qarshe ma kuka ta saki sosai baba yace Dada ki riqeta kuje Dada ta riqeta bayan fitsrsu baba ya kalli mummy yace hajiya kiyi hakuri wannan maganar mu barta nan to ma shi 'dan naki yazo da kansa ayi komai da shi domin wannan al'amarin ba qarami bane yanzu dole sai mun kaishi ma ga manyan malamai su tayamu dubawa domin sannan dole sai 'danki na gurin shi yasan abinda ya faru yazo ya warware mana komai" kuka mummy ta saki ta fara roqon baba tana fa'da masa halin rayuwa da mutuwar da hayat ke ciki baba yayi shiru sai ga Dada da ta shigo ta da'de tsaye mummy na kuka tana wa baba magiya ta qarasa tace malam mimi jikinta ya qara zafi ko na maidata asibiti "yace ki bari zan kirawo likita kije ki zauna da ita kuma kada kibari kowa ya shiga inda take "to tace ta koma duk al'amarin ya fara yi musu yawa daga wannan sai wancan 



A haka mummy ta koma masaukinta cike da ru'dani da neman mafita har dare ta kasa bacci sai tunani 



Wajajen 1:45 na dare ne Dada najin motsin kukan mimi abin ya mata yawa ga rashin mama ga na yah Salman ga nata matsala kuka ta keyi a hankali mai ban tausayi Dada ta tashi tazo har gefenta ta 'dagota ta zauna ta fara magana "mimi wai bakisan qaddara bane.? Wanne daga cikin qaddararki ke damunki? Mahaifiyarki da wanda ya fiki sonta ya ansa.? Girgiza kai tayi mimi tayi, dada ta kalleta tace mimi inaso ki fa'damin komai a kan abinda matarnan da goggo ke musu à kai kingà mahaifiyarsa tace yayi hatsari yana can rai a hannun Allah 'dagowa mimi tayi tana kallon dada cikin tashin hankalii dada tace wai a ranar da kuka taso yayi hatsarin kuka mimi ta saki tana kama kanta dada ta 'dan qura mata idanu kafin taci gaba kinga babu yadda zamu ganshi bare a ji nasa 'bangaren zahiri à gabanki na karanta takardar sakinki safiyar talata shin da gaske ne kunyi kwanciyar aure a ranar talata da daddare? Sosai mimi ke kuka dada ta riqeta tana kallonta tace mimi ki rage kukan nan kada ciwo ya shige ki" kunyi saduwar aure a ranar da daddare"? Cikin kuka mimi ta girgiza kai shiru dadan tayi tana nazarinta kafin ta 'dago fuskarta tana kallon idanunta furta "Mimi kina sonsa ko"? Kuka ta qara sosai dada tayi Shiru duk jikinta ya mutu tabbas kwai ru'dani sosai cikin lamarin a hankali jawo mimi jikinta tana shafa bayan ta saidai itama yanzu sai taji mimin na bata tausayi domin kuwa tasan baba bazai ta'ba barinta da wani ba bayan Safwan musamman yadda auren na ta da  Hayat ya kasance..




Sosai ta ke kuka tanajin yadda take matuqar buqatarsa daidai wannan yanayi da komai ya rikice mata ta dawo bata da kowa mama ta tafi yah Salman ya tafi ta saki wani kuka mai ban tausayi tana qara kwantar da kanta jikin dada shafa bayanta dada ke yi sosai tana rarrashinta har ta 'dan tsagaita da kukan kafin dada ta 'dagota tana kallonta ta furta "amma inaso na tanbaye ki wani abu guda 'daya don Allah mimi ki fa'damin gaskiya kinji.? Girgiza kai mimi tayi dada tace "à wane lokaci kika gane cewa kina son sa.? Shiru mimi tayi dada tace zan taimaka miki ne in kika fa'damin komai.. cikin sarqaqiyar murya tace tun ranar da na fara ganinsa naji zuciyata ta buga .. dada tace to ya mu'amalarku ta fara.? Shiru tayi kafin ta fara magana



A duk lokacin da zaiyi baqi in suka zo ya kance na zauna ne kusa da shi kamar dai da gaske muna rayuwa tare sa'in a gabansu ma har ya kan riqe hannuna ko janyoni jikinsa da dai sauransu... Dada tayi ajiyar zuciya tace to in yanayin hakan ke ya kike ji.? Tayi shiru kafin tace abinda na kanji ne yasa yawanci in yayi baqin na ke tafiya na barsu.... Dada tace ki fa'damin gaskiya da gaske ne da arfi ya fara anfani da ke.? Shiru tayi kafin tace bawai don bana so bane a lokacin sai kawai don ina kiyayewa kaina soyayyarsa da naji ta fara nisa a zuciyata a lokacin.. Dada ta qura mata idanu tace kenan bai tun farkon saduwarku baiyi miki dole ba.? Girgiza kai tayi..! Kallon qofa dada tayi tace mimi yanzu in nace ki za'ba tsakaninsa da Safwan fa.? Shiru tayi dada ma tayi shirun tana kallonta jin shirun yayi yawa dada tace ina sauraronki.. ita mimi tana tunanin ranar da zasu gane waye "Hayat" da kuma asalinsa ranar ne tashin hankali zai faru ta tabbata saidai "ina sonshi fiye da kaina" tana lumshe idanu da hawaye bata sani ba a fili ta furta kalmar "Inajin sonsa fiye da kaina" dada ta ta kashe recorda 'dinta ta dafa mimi tana qara lallashinta ta ce ta kwanta Dada tayi shiru tana ayyana yadda baba ke da taurin kai " tabbas babu wani auren Safwan ko gaban wa zaaje mimi matar "Hayat" ce wannan record 'din kawai ya isa alkali ya bar mimi da mijinta wanda ta ke so da haka itama ta fara bacci 




A babban office 'din kamfaninsu Najwa da Abu'noor da Abu'Nahal sai Abu'Ahlam..



Najwa ta kalli yayyunta ta aje qaton laptop 'dinta na Apple a tsakaninsu ta kunna musu video suna kallo... Hayat ya kalli Mutumin yace Mummy tace kaima 'dan Nigeria ne.? Eh mutumin yace yaci gaba sannan shekarata 29 a Ireland kamar yadda ta fa'da maka kuma kamfanin dama ni da abokina ne 'dan Spain ne to babansa ya rasu ya koma qasarsu so kuma as'idar ko yazama na saidawa 'dan qasa ko gomnati ta saya shine mummynka tace zaku saya amma sai kagama shawara ko.? Ajiyar zuciya Hayat yayi yace eh zanyi tunani sosai dukda komai ta yanke ina kai nima dis is abt in dawo nan da rayuwata gaba 'daya so dole na qara tunani kit video ya tsaya .. Abu'noor ya saki huci mai zafi yace tabbas Yasmin rabamu ta ke son yi à fakaice da Hayat sannan shi kansa bata barshi ya gane ba, Abu'ahlam yace sosai kuwa ace duk kamfanoninmu a qasar nan har Hayat ne zaije qasar wasu sayan kamfani sannan ya koma can da zama shiru su kayi suka ji najma ta furta abinda baku sani ba Yasmin ta sayi gida a Ireland 'din duk suka tsurawa Najwa Idanu tace Lima de har yau bata ta'ba zuwa vidange de ba sannan da sunan Hayat ta sayi gidan zaro idanu su kayi duka najwa taci gaba so nagama duk bincike na shiri ta keyi na rabamu da Hayat ta cireshi daga qasarnan wanda kuma hakan na nufin dole mu Tadjikistan de mu fara yaqarta et muma ajiyar zuciya su kayi duk abu Abu'ahlam yace ta yaya.? Tayi ajiyar zuciya su tace inada qawata 'yer Nigeria zan shiga Nigeria yau zan binciko wacece Hayat ke aure kuma 'yer uban waye domin wannan shine ta inda zamu fara yaqi da ita idan har 'yer qananan mutane ce to tabbas Yasmin ta auro masa ita ne domin su ha'da kai su yaqe mu kaga mu sai mu fara yaqar su duk 'yen uwan su kayi na'am da maganar najwa inda tace ita zata bi jirgin dare domin qawarta 'abuja take mummy kuma yasmin kuma a kaduna take na kwashe duk informations 'dinta a Facebook so qawata zata taimakamin da haka su kayi sallama suka watse 




Haka mimi ke bacci tsakanin mafarkin Mama da mafarkin hasken ruhinta "Hayat" kewarsa da kaunarsa da tausayin sa ta ke ji mara iyaka a hankali ta miqe taje tayi alwala sam batajin da'din jikinta ga yunwa ta fara jero nafilfili har a ka tada sauna tayiwa iyayenta addu'a sosai sannan tayi wa "Hayat" tana kuka da yi masa fatan warkewa da kuma shiriya ya bar "AQIDARSU" ta gado ya gane gaskiya "sujadda tayi tana kuka tana gayawa Allah ya tausaya mata ya kuma tausayawa abunda ke cikinta ya shirya mata "mijinta" ya dawo "AQIDAR" gaskiya a yanzu batada babban damuwa irin "AQIDAR" sa wannan wani sirri ne da zata yi komai domin ta tabbatar babu wani da ya sani cikin danginta hatta goggo da Yah Salman  Dada ta tashi ganin mimi kan dadduma ta wuce itama toilet 



Najwa ta sauka Abuja ta kira qawarta Zinat matar wani tsohon ambassador ne Zinat tace zan driver zaizo ya 'dauko ki nima ina kaduna gun naje ta'aziya so zaikai ki airport ki biyo jinrgin kaduna zansa a zo a 'dauke ki ok Najwa tace 



Tsohon Ambassador Musharraf 'dalibi ne ga baba tabs kar'ban darasi duk sati sau biyu domin gidansa na Gobarau road U/rimi  kaduna su ke wk end da iyalansa hakan yasa su  ke zumunci 



Koda a driver na kaduna ya 'dauko Najwa a airport ya  wuce da ita hajiya zenat ta gama shirin zuwa ta'aziya sosai su ka rungume juna Najwa tayi wanka ta ci abinci ta kintsa ta suka qara duba adress 'din mumny Zenat tace ai ba nisa daga gun ta'ziyar zamu wuce can yaso acan zan samu ko maqota mu kwashi informations 'din da muke buqata a kan surukar tata da haka Suka miqe suka fita Zenat ke driving har kinminau 


Mimi na folon Baba da Dada sabida jikinta nan yafi shiru sannan sabida yanzu dayawa na jifanta da mugayen kamai da habaici a wai tayi auren sirri sabida kwa'dayi ko da safe da ta gaida su goggo hanne da jummai banza suka mata haka layla duk dada na kula agissant ta kaita falon baba ganin cikin gidan a cike ya ke 



Mummy ma bata fito ba tukuna sabida dare ta kwana sallah sai asuba ta kwanta gajiya ganin batama da wayar kiran Banat taji jikin hayat amma yau komai dare zata bar gidan nan da mimi haka ta ke ta saqawa har ta koma baccin







**************



Koda su Zenat su ka iso


Direct su ka isa cikin gidan sun gaisa da kowa Zenat tayi ta'ziya inda Najwa ta tanbayi Zenat wannan gidan 'yen wace AQIDA ne.? Zenat tace "IZALA" Babban malamin sunna ne tsaki Najwa tayi har mutanen da ke gurin su ka kalleta tace shiasa naga ne da sauri da gida kika barni da zuwa wannan gidan "sosai a ke kallonta à falon taci gaba ke kinsan sarai ko gaisuwa ba nayi da wanda ba 'dan "AQIDARMU" ba rage murya Zenat tayi tace yi hakuri ai yanzu zamu tafi shi malamin zanwa gaisuwa mu wuce.. Zenat ta qara tsaki goggo hanne sai hararta ta keyi inda Dada ta shigo suka gaisa da Zenat tace yace kuje falo yana zuwa toh tace suka  miqe 



Mimi na falon tana kwance can nesa suka shigo suka zauna cikin bacci taji wani irin anshi da ya fara yamutsa mata hanji taji amai na taso mata 'dan 'dagowa tayi ta hango baqine don haka ta fara qoqarin miqewa ta bar falon kafin tayj amai gaban baqi tana miqewa baba na shigowa Zenat na juyowa Najwa fuska ba annuri ganin na'din kan baba na 'yen sunna tabbas wannan maqiyan "AQIDARMU" ne baba ya hango mimi da jiri ke shirin yar da ita ya furta subhallahi Hajiya yarinyata zata fa'di ku tare ta da ke sun fishi 'dan kusa da mimi Zenat tayi maza ta qarasa tana tare mimi inda ta cesse Najwa tazo su kai mimi cikin gidan a dole Najwa ta qarasa ta tayata saidai irjinta ne ya harba idanunta suka fito ganin mimi ta kalli Zenat ta qara kallon mimi...

💖AQIDARMU💖


           Na 



Boyayyiyar marubuciya


No comments