Breaking News

AQIDARMU Book 1 Page 13-14

 🅿️13/14




Sai kusan 11 dr yazo ya kira Salman yace suje office ya bishi bayan sun wuce goggo tace yaya ana sallamarmu daga nan zamu wuce kinkinau ni da Mimie yau ce ranar da Baba ya bamu ni kaina banason ku qara samun matsala da shi yaso sun qarasa jinyarta a can, ajiyar zuciya mama tayi tace to asma nan suka ci gaba da yin shiru sunyi tagumi suna jiran fitowar Salman daga gun Dr



A office dr yacewa Salman ya zauna ya zauna ya kuwa zauna dr ya fara masa bayani daga binciken da mu kayi na qirji da qanwarka ke fama da shi ba komai bane illa damuwa da ke shirin Haddasa mata ciwon zuciya so zamu fara kula da Ita IA indai ta kwantar da hankalinta kuma a na kiyaye sanyata cikin damuwa to zata warware IA sai zafin jikinta shima da yayi yawa bamu bata magani ba sai bayan mun yi mata gwaje2 to yau kuma ana hutun aiki da gobe 'yen lab basu zo ba so dole sai zuwa monday zaku dawo da Ita IA zamu  'diba jininta a yi mata gwaje2, ajiyar zuciya Salman yayi yace yanzu babu damuwa kenan zamu iya tafiya da ita.? Eh Dr yace yana 'dan rubutu ya gama ya bawa Salman yace ka saya mata wa'dan nan magungunan hutu ne b4 monday IA sai musan sauran magungunan da suka kamata ansa Salman yayi yayi godiya ya fito nan ya sanarwa su Mama yace suje su riqo mimie goggo har jikinta na rawa suka qarasa word 'din da mama suka cicci'bo mimie suka fito har mota inda goggo tace mu sauke yaya hanya ta qarasa a napep mu mu wuce kinkinau gudun matsala da babanku Salman yaso gardama ya tuna gaskiya ne kada ma suje su fara zargin wani abu don haka ya kawo mama har kusa da gida suka sauketa suka wuce kinkinau 



A kinkinau gidan na cike manya da yara har an fara hidimar 'daurin auren mimie da Safwan motar ta shigo gidan Salman baiyi mamaki ba sanin duk danginsu dama babu wanda baya son auren Mimie da Safwan gyarawa yayi yai parking ya fito goggo ta riqo mimie suka nufin cikin gidan nan cousins 'dinsu mata sa'o'in mimie suka fito suna tanbayar lafiya goggo tace zazza'bi ke damunta tun kan mu dawo sai kuma da muka iso ya ha'du da gajiya haka duk a ka 'dunguma zuwa cikin gidan iyayensu mata duk suna gidan nan a ka miqe a nata oyoyo a ka shiga babban falon gidan Fauza da Layla da Hajara duk sune suka tashi tare da mimie suna ABU su nan a ka kwantar da mimie kan kujerar falon a ka fara gaisawa da Goggo da a ka kawo mata ruwa da drinks inda ta fa'da musu daga asibiti suke tun jiya da suka shigo a ka kwantar da mimie jajantawa suke maman Safwan duk suna gun inda Fauza da layla tuni taje ta sanarwa baba isowar su mimie da kuma halin da mimie ke ciki ya 'danyi jimami kafin yace ina goggon na ta.? Fauza tace tana ciki yace kuje ku kiramin ita suka miqe suka fita suka fa'dawa goggo koda ta isa falonsa suka gaisa yake tanbayarta ta fa'da masa yadda ta fa'dawa iyalansa yayi shiru kafin yace tunda haka likitan yace to babu damuwa yaso lokacin ma sai mijinta ya kaita kallonsa tayi ya gane me take nufi wato a hakan za'ayi auren gobe.?  Murmushi yayi yace asma'u baki girma to zazza'bi zai hana ibadar Allah ko gidan mijinta take za tayi ciwo to mai zai hana a yi don kawai tana ciwo abu 'daya zanyi zata zauna nan zuwa kwanaki in tayi warware da kyaw sai ku kintsata ku kaita gidanta sabida ma naji 'yen uwanta matan wai sun shirya masu walima Allah ya bata lafiya ya basu zaman lafiya "amin tace murya a raunane" tana mamakin taurin kai irin na mutumin ta rasa shin 'yen sunna ne gaba 'daya haka ko dai dama shi haka halinsa yake tun fil azal da haka ta masa sallama ta fito ta koma mimie har tasha drugs tana bacci don haka ta yi wa mutanen sallama ta wuce gida a kan sai ta shigo da safe kafin 'daurin auren suka ce to ta wuce zuciyarta fal tunani inda ta yanke hukunci zuwa ganin mummy kafin ta wuce t/wada saidai Salman yace yace mata mummy ta wuce abuja shiru tayi ko shi ta kada gaya masa dalilin da yasa ta keson zuwa gun mummy haka suka wuce gida kowannensu zuciyarsa cike da tunani har suka iso 



Hayat bai Farfa'do ba har lokacin inda hankalin danginsa ke matuqar tashe musamman ganin wai matarsa bata tare da shi a irin wannan mawuyacin yana yi ko babanta ne ya rasu ya kamata a yau ta bar gun makokin ta zo kusa da mijinta duk suka qara quluwa da mummy suna jira ta iso ayita a qare inji abu'Noor 



Safwan kamar zai tashi sama don farin ciki saidai abokansa na danneshi a kan kada ya nemi mimie har sai gobe da yamma bayan ta zama mallakinsa ganin sun da'de basu tare ko wpp ya mata bata ansawa tun bayan rabuwarsu haka ma mamansa ta fa'da masa sabida tace 



Dare wajajen 3:am ne mimie ta farka wata goggonta goggo hanne ta riqeta zata rakata toilet yanayin mugun zafin jikin mimie ya bata tsoro saidai ta kalleta tace muje ki 'dan kwara ruwan sanyi zaki ji sauqin jikinki har toilet goggo hanne ta Raka ta tayi wanka inda ta kullo mata ta zauna kawai Shiru masifar jiri take ji har lokacin funds tana samun bacci ga mararta da ke damunta da qullewa sosai hannunta ta kai a hankali tana shafa sarqarta bata fatan ta ta'ba cirewa sai ranar da zata shiga kabarinta to amma yaya zatayi da Safwan ranar da tsautsayi yasa ya gani runtse idanunta tayi tana furta bazata ta'ba barin wani namiji ko waye ya qara ta'bata ba har abada saidai in ta zauna babu aure domin kuwa ita yanzu haka ma take so indai ba "HAYAT" bane to ta yafe kowa ta saki hawaye mai 'dumi tana qara shafa sarqar a mararta ta da'de kafin da kyar ta yi wanka ta fito sanye da kayanta da ta shiga da su ta koma goggon ta bata tea da kyar ta sha kafin ta sha naganinta ta koma ta kwanta dukta ita ba baccin ta keji ba 



11:am agogon Tehran mummy ta sauka Tehran direct Asibitin ta wuce inda ta samu masu aikin babban gidan kakansu Hayat ne sunata 'yen aikace aikace word 'dinsa dukda tulin nurse 'din da ke Asibitin tanbaya tayi a ka kaita word 'din Hayat inda yake kwance kamar gawa da hawaye ta qarasa shiga tana isa gaban gadon kuka ta daki sosai shikenan abinda yayarta ta bari ya Allah ka tayani ruqonsa ta furta tana qara sakin kuka taji motsi a hankali ta juya wata qanwar baban hayat ce itace autarsu sunanta "Najwa" da ke auren ministan lafiya ta shiga itama sun da'de kafin suka fito a tare Najwa ta kalli Mummy tace Yasmin domin zasuyi sa'o'i da mummy tace Yasmin gaskiya kina shiga mana hanci dayawa kallonta mummy keyi da mamaki dukda tasan duk dangin najin haushinta suna ganin tanason qwace Hayat ne daga garesu suna kyaleta ne domin baban Hayat yasha fa'da musu itace ka'dai mai kaunarsa duk cikin danginsu mummy 'din " Najma taci gaba Yasmin Kinje kin aurowa Hayat qaramar yarinya wacce kowa ya gane ita kanta bata gama sanin ciwon kanta ba bare ta iya kulawa da mijinta, report 'din Hayat na hannun noor tsabar damuwa ce ta sanya masa gushewar hankali har yayi accident wato bama ta kula da halin da mijinta ke ciki bare ta taimaka masa ko zai riqa samun nutsuwa tunda ya aurota tazo qasarna babu wani Family event 'dinmu da ta ta'ba zuwa kinfi kowa ssnin komai namu tare da yaranmu da surukanmu maza da matansu mu keyi amma yarinyat nan bata ta'ba zuwa ba sannan kullum a kai mata documents tayi signing  bata yi haka za'a dawo mana da shi a je gidan ta bar mutane ta tafi wlh ko babanta ne ya mutu ki tabbatar gobe ta dawo quasarnan jinyar mijinta in ba haka ba zamu bashi wata matar kinsan dai gidanmu cike yake da Cv 'din mata tunda dama mune bakiso muyi masa auren kika yi sauri kika auro masa ta ku ... Tunda Najma ta fara magana mummy ba tace qala ba bar ta idda tana gamawa kuma ta juya ta bar mummy gurin mugun tashi hankalin mummy yayi abinda ta guda na shirin faruwa hawaye ta fara taji wayarta na ringing domin tun taxi ta maida sim 'dinta na IRAN kallon wayar tayi Banat ne ta 'daga nan ya fara tanabyarta Hayat ta bashi labari da cewa itama yanzu ta dawo Tehran 'din cikin tashin hankali yace mummy bari nazo to tace ta tsinke call 'din 



Har asuba mimie bata farka ba inda goggo hanne tace ba'a tashin mara lafiya suka kullo mata qofar suka fita anata sha'ani mutane duk sun fara cika gidan maqota da 'yen unguwa 



Salman na 'dakinsa ya bu'de envelope 'dinsu na gun mummy yaga passeport da komai sai takardun banki da check na 5M inda ya saki murnushi zai kai mama hajj sannan ya bata jari mimie ya bu'de mata camis a hankali kuma ya zaro takardar sakin mimie ya bu'de ya fara karantawa 



Ni Hayat Muthallib Thariq na saki matata Farid.... Goggo ta fara qwalo masa kira Salman ka fito kada muyi rana ajiye takardar yayi ya fito ya jawo qofar kawai suka wuce mama na ce masa a haka zaka ko wanka ba kayi ba.? Yace mama nayi da asuba ai to tace ya wuce har yau motar aikinsa na hannunsa koda ya kira baban twins yace zai dawo da motar yace masa Salmanu ka bar ta gunka kuci gaba da hidimar asibitin qanwarka goggo ta shiga ya tayar suka bar gidan 



Banat bayan ya fito ya kalli Mummy yana bata labarin yadda su kayi da Hayat ranar faruwan hatsarin shiru tayi banat ya kalleta yace mummy nayi mamaki abinda ya damu hayat har yayi hatsarin bcs ranar da anaérobie gobe zaku tafi ke da matarsa inajin sun kwana cikin nisha'di shi da ita kuma a yadda nazo na dubata ya bata wahala sosai domin ko motsi sosai ba tayi har ina tsokanarsa irjin mummy ne ya buga tace ban gane ba.? Kana nufin banda ranar da kazo da yamma muna tare da shi a daren suka kwana cikin nisha'din.? 'Dan murnushi banat yayi da ke kamar turawa suke basu 'boyewa juna komai yace eh mummy Hayat baya ragawa yafinyar wlh ko qarewa drip 'dinta baiyi ba ya kwana ranar yana murzata bayan fajr ne ma na fito nazo dubata duk tayi lashi ko yatsanta bata iya 'dagawa har saida na bata kulawa innalillahi mummy ke tayi a zuciyarta wannan yana nufin "Hayat ya mayar da aurensa da Farida"  indai ya sadu da ita bayan sakin da ya bata jiri ne mummy ta fara ji ta yi tagaaa zata fa'di Banat ya taro ta tanata kiran sunan Allah a ranta wannan wane irin tashin hankaline yau za'a 'daura auren Farida hawaye ta fara ta shiga lalubar wayarta banat yace mummy lafiya.? Tace pls ka samomin panadol in sha yace ok ya fita ta zauna da kyaw ta shiga neman wayan Salman 




Gidan maqil ga 'daliban baba da ke zuwa karatu alhamis da juma'a suna cike suma daga sun gama za'a wuce masallaci wayar Salman kuwa 'dakinsa ya bari garin sauri inda mummy ke ta kira babu ansa gani tayi yanzu 10:35am ne a Nigeria tayi yafi 10mclls ba ansa ta ajiye wayar tayi tagumi ta rasa ta ina zata fara matsaloli sun tunkaro ta hawaye ta keyi sosai har banat yazo tace ya rakata gun shakatawar Asibitin tana buqatar nutsuwa yace ok suka wuce 



Sosai gidan ke cike har lokacin babu labarin farkawar mimie magungunan hutu ne da bacci dr ya bata sai kayi 10h kana bacci babu wanda ya zargi komai a nata sha'ani kawai



Salman ma baba duk ya tsaresu hidimar baqinsa ga cikowa 'yen uwansu da abokai a qarshe da zasu wuce mosque gidan ya qara wanka Abba wani cousin 'dinsu yaron baba ya bashi kaya yasa inda Salman ya kwashi wasu mutanen a motarsa suka wuce gun 'daurin aure 



Bayan banat ya tafi akan zai dawo anjuma mummy duk 1mnts take kiran layin Salman babu ansa itakam dole ne ko me zai faru da su yasan yadda zaiyi ya tsaida 'daurin auren har Hayat ya farka ya qara bawa mimie wani sakin domin tafi kowa sanin ba'a aure kan aure haka take kiran layin Salman shiru ta shiga kiran sunan Allah yayi mata 'dauki a kan tashin hankalin da ya tunakro ta 



1:38pm a ka 'daura auren a babban masallacin "Malam algarqawi" ke kinkinau kan sadaki 250k Sosai Safwan yayi shirin dawo da martabarsa idanun mimie domin har lefe ya sake yi mata akwati shida





A na shafa fatihar Hayat ya fara kakarin numfashi yanson farkawa nan likitoci suka taru kansa suna kokarin daidaita masa numfashintsa wata Noor mummy ta hango ta miqe da sauri ganin shima yana sauri ta ce Noor mai ke faruwa cikin mugun tashin hankali ya furta "Hayat yana tafiya bata qara tanbaya ba tabi bayansa har word 'din Hayat da ke ta numfashi da kyar kamar numfashin na shirin 'daukewa Hawaye mummy ta fara sauran drs zasu ce ta fita Noor yace musu mamansa ce


Cikin bacci taji wani muguwar fa'duwar gaba har irjinta ya riqe numfashinta yayi nauyi ta  fara nishi ta kasa bu'de idanunta sai ganinsa da takeyi cikin idanunta tana qoqarin ta'bashi yana nisa da ita kuka ta saki mai tsananin ban tausayi wanda ashe ba cikin mafarki bane wasu mutane 'yen taro da ke falo suka jiyota a ka 'dunguma 'dakin nan labari ya baza gidan goggo tayi hanzari ta shiga mimie na riqe hannun baba jummai idanunta na lumshe sai kuka take sosai ga nunfashin sai a hankali cikin tashin hankali goggo ta qarasa ta riqota ta kalli mutane tace a 'dan basu guri ta kintsata a kaisu asibiti duk suka fita goggo ta kulle qofar hankali a tashe musamman danginsu wasu kuwa tanbayoyi suka fara yiwa kansu a kan ciwon mimie



Kallonta goggo ke yi cikin tsabar tausayawa ta furta "mimie mai ya ke damunki kin sani ina babu wanda ya kaini ajiye muku sirrinku wlh ko yaran cikina bana tausaya musu kamar yadda na keyi muku "ta riqe mimie da kyaw tace "ki fa'damin abinda ke damunki ko zan iya samo miki mafita a kai "hawaye kawai ta keyi zuciyarta kamar zai fito goggo ta qara riqo hannunta tana kallonta ta sake maimaita Mimie ki fa'damin kinji.? A hankali kamar nunfashinta na son 'daukewa tace "goggo in ya mutu nima mutuwar zanyi" goggo kamar daqiqiya tace "ban gane ba.? a mainaitawa ta qara yi tana hawaye ba qaqqautawa wani na bin wani, riqota goggon tayi da kyaw tace "waye shi mimie"? Kallon goggo tayi tace "HAYAT" goggo dai bata gane ba tace waye "Hayat"? Mimie ta saki hawaye sosai tace "Mijina" irjin goggo ta ne ya buga tace "mimie hala kin samu baki cikin hankalinki sunan mijinki "Safwan" kallon goggo mimie tayi ta kasa iya qara magana goggo tace 'dazu a ka 'daura muku aure wani zazzafan hawaye ne ya fara biyo kunatunta tana kallon goggo kafin goggo taga ta sulale mata a jiki sumammiya cikin forgiving and goggo ta fara jijjigata ina shiru salati goggo ta saki a ka kuwa jiyo a kazo ana buga qofar da kyar goggo ta bu'de cikin mugun tashin hankali ta ma kasa ta'ba mimie su goggo hanne da su jummai suka riqeta har mota Salman ma da shigowarsa kenan shi ya kwashesu a ka koma asibiti hankalinsa shima a tashe gashi talata zai bar Nigeria kuma lahadi da yamma zai bar kaduna zuwa abuja ya gama sauran hidimomin tafiyar sa haka yake jan mota da arfi cikin mintuna suka iso giwa hospital





Nan a ka qara bawa mimie gado wannan karon ba ta ita ba barin asibiti har sai angama dukkan bincike haka dr yace Nan a ka yanke bilingual goggo zata zauna da ita a asibiti



A kinkinau kowa hankalinsa a tashe baba yana masallaci a na jira ya shigo a sanar da shi Safwan kuwa yafi kowa gificewa saidai iyayensa ke danneshi da haka ya kwantar da hankali mamansa tace kada ya je asibitin ya bari sai zuwa gobe da safe da kyar ya hakura yaso yaje ya ganta yayi missing komai na ta 



Sosai a kayi fama da numfashin Hayat kafin ya samu ya dawo normal normal dukda bai farfa'doba mummy kuka take sosai tana dana sanin auren shirya auren Hayat da Farida Noor ma yaji tausayin mummy dukda da suna jin haushinta shi da Iyayensu kallonta yayi ya furta mummy kiyi hakuri and addu'a zamu rika yi masa shiru tayi kawai shima ya wuce yana kiran iyayensu yana sanar da su 



A giwa ma hankalin Salman na tashe ganin wai sai Monday lab zasu dawo amma an d'ora mimie kan drip ta samu bacci goggo da Salman duk sunyi tagumi kowannensu da abinda ya ke saqawa zuciyarsa



Mama da ke aiki a tsakar gida maqota 'yen Allah ya sanya alkairi na ta shigowa yanzu ne suka ragu tana 'dan gyara gidan ta jiyo wayar Salman na ta ringing ta kasa kunne tabbas wayarsa ce ya manta gida tun safe gashi yau sai Allab qila ma sai gobe zai shigo gidan domin yace tafiyarsa ranar lahadi ce a hankali ta tura qofar da nufin ta kashe masa wayar ta shiga cikin 'dakin wayar na kan takardar sakin mimie sabida Salman ya tura sauran a envelope sunkuyawa tayi a hankali ta 'dauki wayar zata kashe kira na shigowa ta zata 'daga a tajiyo a na sallama ta fara kallon kofar fita inda kawai ta sunkuya ta ninke takardar da sauri bata kalla ba ta tafi dashi da wayar ta fito ta fara gaisawa da baqin da suka shigo Allah ya sanya alkairi 



Sai kusan 11:pm Salman ya bar giwa gida ya nufa direct duk zuciyarsa babu da'di har ya iso mama ta da'de da bacci shima 'dakinsa ya wuce baima wani dogon tunani ba ya nemi guri ya kwanta saidai ya kai 1:pm kafin yayi bacci 



A Giwa hospital goggo na ta rarities maganarta da Mimie tanason ta fahimci  wani abu ta kasa sai kalma biyu da ke dawo mata "In ya mutu nima mutuwar zanyi in" mijina" waye "Hayat" zabura goggo tayi ta Jawo wayar gefen ta jefa layin Salman na mtn a kashe ta fara duba qaramar tecno 'dinsa da ba kowa ya sanshi da layin ba cikin sa'a taji wayar na ringing Salmn da bai da'de da fara bacci ba wayar na ringing cikin magagi yaji kiran ya fara neman wayar can cikin wadrobe 'dinsa ya ganin wayar sai lokacin ma ya tuna da ba bar wayarsa itama ko kallon wayar baiyi ba ya ansa yasa kunnensa goggo tace ka tashi da kyaw muyi magana to yace yana gyara zamansa " tace ka karanta takardar sakin mimie.? Eh yace na fara na fita amma amma sakin yayi tace ko kasan sunansa.? Yace wa.? Tace shi wanda su kayi auren kudin.? Yace wlh ban sani ba nifa tun da mu ka abada na 'daura na fita zanc.. tace amma Salman ka iya sakarci ta yaya zaka 'daura auren qanwarka da kanka ka manta da sunan mij... Ya katseta na tuna goggo tace yawwa yace "Hayat" irjin goggo ya buga Salman ya qara da cewa kuma a Takarar sakin ma haka ya rubuta sunansa "Hayat" salati goggo ta fara tace  Salman yace menene goggo.? Tace Salman asirinmu zai tonu.. cikin tashin hankali yace "a sabida me asirinmu zai tonu bayan gashi har an 'daura auren mimie da Safwan"? Tace Salman ciwon son "Hayat" mimie keyi cikin rashin fahimta yace kamar ban gane ba goggo nan ta bashi labarin yadda su kayi da mimie wato rabuwarsu ce ta saka mimie cikin Wannan ciwon, ajiyar zuciya Salman yayi ya aro jarumta a matsayinsa na namiji yace "goggo to ko tana sonsa ina zata ganshi yana can yana aikinsa Hajiya tacemin yafi 20yrs a can kuma kinsan halin masu ku'dinmu basu ta'ba yadda yaransu su auri yaran talakawa kuma ma ai  magana ta qare ita matar Safwan ce yanzu haka dai yayi ta kwantarwa goggo hankali bayan shima ya 'dan shiga ru'dani inda a qarshe su kayi sallama da goggo yayi Shiru 



Itama goggo Shiru tayi ta qurawa mimie da ke bacci idanu zuciyarta fal tanbayoyi



A kinkinau ma dai hankalin mutane dangi duk ya karkata kan mimie inda a lot suke ganin dama ba'a maida auren ba har sai ta warke baba kansa ciwon mimie ya fara 'daga masa hankali inda yace a gyara mata 'dakin su Fauza ita ka'dai zata zauna nan har ta warke sosai kafin ta tare 



da safe Salman ya qi fa'dawa mama halin da mimie ke ciki baya son qara tayar mata da hankali ita tsammaninta goggo zata zauna ne gidan baba babba har a a gama da jama'a don haka ya mata sallama ya wuce asibiti a can ma goggo sama2 take ya lura ya basar domin baiso suna 'dago abinda ya wuce a gurinsa auren mimie da "Hayat ba wani abin baiwa muhimmanci bane "ikon Allah haka suka da'de da goggo suna fira zuwan Safwan ne ya sasu yin shiru har Safwan kallonta yake kamar ya ha'diye ta kasa fita ta batshi da mimie ya da'de kafin ya miqawa goggo jakar da yazo da ita sannan ya bata 10k yace in tana buqatar wani abu godiya ta masa ya miqe Salman ga bishi suka fita tare suna 'Dane tattaunawa har kowa ya shiga motarsa 



Mummy tun lokacin da Hayat jikinsa ya tashi ta bi noor a gigice a she ta yar da wayarta kuma ko ta kan wayar bata qara bi har yanzu..



Sai yanzu Salman ya kunna wayarsa da y shiga  mota inda yaga 52 mclls na Mummy mugun firgita yayi a kan mai ya faru ya shiga binta s/off ya shiga wpp rabonta tun last 4dys ya kira laraba tace masa ai Mummy tayi tafiya tun washegarin dawowarta sosai ya shiga fargaba da tulin tanbayoyi a ransa 



Lahadi da 7:am Salman yayiwa mama sallama ya wuce tanata masa fatan alkairi domin yace mata bayason danginsu susan da tafiyar sai ya isa zai kira kowa yace ya isa Mama tayi masa Madigan Sosai da ke dama tasan da tafiyar yasha ce mata kwatsam tafiyar zata tashi sabida yanata shirinsa a hankali daga gida ma asibiti ya wuce saidai cikin rashin sa'a mimie ta farka tayi sallah a ka qara maida mata drip ta komai so yayi sallama da goggo a kan sai ya isa za suyi magana domin ma nan da 4mths zaizo hutu IA nan ya mata sallama ya wuce Isa kaita ya nufa ya ajiye mota su kayi sallama da su balaraba da Tara ya wuce 'daukan train zuwa abuja




A na cike falon baba ne Dada matarsa ta biyu tace Malam gobe mu ma bayan yara sun wuce boko za'a saukemu asibiti gaba 'daya sai mu duba jikin mimie tunda suka kwanta goggo hanne ce kawai ta Samuel zuwa sai su Fauza, ajiyar zuciya yayi yace haka ne Allah ya kaimu sai kuje har da su yapendon shanono sabida wai jibi zasu wuce 'to tace a kaci gaba da hira...



Cike suke can special sitting room da suke da shi a Asibitin mummy na can nesa da su wacce a kwana biyu kawai ta gigice duk ta fita kammaninta Abu'Noor yace "Yasmin wai har yanzu matar Hayat batada labarin halin da mijinta ke ciki.? Za tayi magana Abu"Ahlam yace Yasmin yau kwanan hayat uku a asibiti ke uwarsa har kinbar duk abinda ke gabanki kin dawo tayaya matarsa da ya kamata ace itace za tayi haka ace har yau batazo ba..? Za tayi magana still Najwa ta katseta kinga Yasmin wlh wannan yarinyar in tana juyaku ke da Hayat mu ba  zamu 'dauka ba sannan yanzu ma hukuncin da muka yanke zamu fa'da miki yadda kika kawota har gidan mijinta to kema bamuson qara ganinki Asibitin nan har sai kuna tare in kuma sun rabu ki fa'da mana sai musan abinyi da wuri sabida mu munada ayyuka dayawa a rayuwarmu dole matarsa ce ya kamata ta kasance dashi a kowani lokaci har ya warke in kuwa sun rabu mu sani domin a yadda yake a kwancen nan zamu masa aure tsaf matar kuma da gudunta zata tare asibitin nan tafara jinyarsa


Yawu mummy ta ha'diya abu Nawwal yace gaskiyar kenan yanzu ki koma abinki ko ku dawo tare yadda kika aurota ko kuma kuma ki fa'da mana ainihin halin da aurensu ke ciki sosai mummy ta fara gumi tana binsu 'daya bayan 'daya da kallo 



Tun 7:am a kazo a ka 'diba jinin Mimie da fitsari da komai inda a ka tafi gwaji mimie da farkawarta kenan bayan an gama 'diba goggo ta tilastata shan tea mai kauri wanda tun kan ta gama sha taji yadda gaba 'daya maha'dar jijiyoyin jikinta sun bata wani mummunan garga'di ji tayi komi na jikinta na yanutsewa ta runtse idanu saidai ta kasa magana ta riqe kanta idanunta a rufe su kaji shigowar gayya sosai goggo ta fara musu maraba haka duk a ka zauna a takure a ka fara Hayat da goggo da tanbayar mai jiki ko 5mnts ba suyi ba sai ga Safwan shima haka goggo tace su Fauza su sauka gefen mimie ya zauna kallonta ya ke tunda suka shigo har yanzu bata 'dago kanta ba sauran da goggo sunata fita shi SafwAn yanata kallonta inda ya juya ya kalli goggo yace Dr bai shigo ba har yanzu.? Ya shigo harma sun 'diba jininta da fitsari sunje bashi wai yanzu zasu gama sai a san abunyi a kan zazza'bin ok yace. Bari mu jirashi 




Har a abuja Salman naci gaba da neman layin mummy still off dole ya hakura saidai sam zuciyarsa ta kasa samun nutsuwa in ya tuna yawan kiran da tamasa ko da yayi aiki gidanta 5yrs bata ta'ba masa ko 5mclls ba koda yayi lattin kai yara school ko lattin 'daukosu tabbas abune mai matuqar muhimmanci zai sa tayi masa wannan kiran da haka dai ya share yaci gaba da hidimominsa domin gobe da rana zai tashi zuwa (kuala lampur



Suna zaune duk dr ya shigo ya kalli yada sunkai su 13 yace wannan in kuka da'de a nan zaku qarawa patient 'dina ciwo bayan ta na buqatar hutu sosai ajiyar zuciya Safwan yayi suka gaisa ya ce "ina yayanta"? Goggo jummai ta ce likita ai wannan yayanta ne kuma mijinta" ok yace yana murnushi ya miqawa Safwan hannu tare da furta "Congratulation" dûk suka qurawa dr ido musamman su fauza Safwan yace dr ban gane ba.? Dr yayi murmushi yana dafashi yace "matarka na da shigar ciki ..

💖AQIDARMU💖


          Na


Boyayyiyar marubuciya


No comments